JusticeForHanifa: Kisan Hanifa ya fusata ƴan Najeriya

Asalin hoton, Family
Jama'a da dama na alhini da nuna ɓacin ransu a shafukan sada zumunta bayan rahoton da aka samu na kashe Hanifa ƴar shekara biyar da haihuwa a Kano.
Batun kashe Hanifa na daga cikin manyan abubuwan da ake tattaunawa a shafin Twitter inda akasari mutane ke neman a bi mata haƙƙinta da hukunta waɗanda suke da hannu a kashe ta.
A ranar Alhamis ne rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta bayyana cewa an gano gawar Hanifa bayan sama da kwana 40.
Ana zargin malamin makarantar su Hanifa ne ya sace ta ya kashe ta sannan ya binne gawarta a cikin makarantar.
Tun a watan Disambar bara ne aka sace Hanifa a hanyarta ta dawowa daga Islamiyya.
Me jama'a ke cewa kan kashe Hanifa?
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wannan mai suna Manus a shafin Twitter yana kira da a hukunta wanda ya kashe Hanifa tare da cewa idan an jinkirta hukunci kamar an ki yin adalci ne.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Ita kuma Sodukunle Fadilat na da ra'ayin cewa aksarin malamai a wannan zamani suna koyarwa ne domin su samu kuɗi ba wai don suna sha'awar koyarwar bane. Ta ce masu irin wannan ra'ayin ne za su iya aikata komai.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Wannan kuma cewa take yi "babu inda ke da akwai tsaro, ba makaranta ba gida ba. Ba za mu iya tura ƴaƴanmu makaranta ba tare da tunanin za a sace su ba ko kuma malamai ko ɗalibai su cutar da su," in ji ta.
Ita ma ta rubuta mau'du'in #JusticeForHanifa wanda ke nufin a hukunta waɗanda suka kashe Hanifa
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Wannan mai suna Garba kuwa cewa ya yi har ta kai ga malamai sun soma sace ɗalibansu alhalin ya kamata a ce daga iyaye sai malamai. Shi ma ya buƙaci a yi wa waɗanda ke da hannu da sace Hanifa hukunci.
Waiwaye
A ranar wata Asabar 4 ga watan Disamban shekarar da ta ƙare ta 2021 ne aka sace Hanifa mai shekara biyar a unguwar Kawaji da ke birnin Kano.
Mutanen sun ɗauke Hanifa Abubakar ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma bayan sun isa wurin a cikin babur mai ƙafa uku ko kuma A daidaita-Sahu.
Iyayen Hanifa sun ce mutanen sun sace ta ne jim kaɗan bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya tare da sauran yaran maƙota.
"Babu nisa tsakanin makarantar da gidansu (Hanifa), saboda haka yaran sun saba zuwa da ƙafarsu," a cewar Suraj Zubair, kawun Hanifa.
"Wasu daga cikin yaran da suka ga lokacin da abin ya faru sun ce ɓarayin sun zo ne a A daidaita-Sahu kuma suka ce za su kai su gida.
Bayan sun kai su, sai suka ce Hanifa ta sake hawa don su ɗana ta, amma sai suka gudu da ita."