Ƴan Arewaci biyu da ke ƙalubalantar Paul Biya a zaɓen Kamaru

Asalin hoton, Getty Images/Collage
Mutum biyu ƴan arewacin jamhuriyar Kamaru ne suka shiga sahun masu fafatawa da shugaban ƙasar Paul Biya da ke neman sabon wa'adi.
Mutanen sun haɗa da ministan yawon buɗe ido na ƙasar, Bello Bouba Maigari da tsohon kakakin gwamnati, IssaTchiroma Bakary.
Bello Maigari ya amince da damar yin takara da jam'iyyarsa ta ba shi a zaɓen shugaban ƙasa na watan Oktoba domin karawa da shugaba Paul Biya wanda ya kwashe shekaru 39 a kan karaga.
Har kawo yanzu dai Paul Biya bai sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takarar ba.
Wane ne Bello Bouba Maigari?

Asalin hoton, Getty Images
Bello Bouba Maigari, mai shekaru 78 ya kasance abokin tafiyar shugaba Paul Biya a tsawon fiye da shekaru 30. Maigari ya kasance tsohon firaiminista a jamhuriyar ta Kamaru.
Yanzu haka zai yi takarar domin ƙalubalantar Paul Biya a jam'iyyar NUDP duk da cewa bai ajiye muƙaminsa na ministan harkokin yawon buɗe ido ba.
Shi ne ministan gwamnati na biyu daga arewacin ƙasar da ya bayyana aniyarsa ta takarar neman shugaban ƙasa a baya-bayan nan wani abu da ke nuna ɓaraka tsakanin shugaba Paul Biya da masu faɗa a ji a arewacin ƙasar.
Wane ne Issa Tchiroma Bakary?

Asalin hoton, Anadolu Agency via Getty Images
Issa Tchiroma Bakary - fitaccen minista kuma daɗaɗɗen abokin tafiyar shugaba Paul Biya ya bar kujerarsa ta ministan sadarwa domin ƙalubalantar tsohon ubangidan nasa a zaɓe mai zuwa.
Watanni huɗu kafin babban zaɓen jamhuriyar ta Kamaru, Tchiroma ya ce al'ummar ƙasar sun yanke ƙauna da gwamnatin Paul Biya, inda daga nan ne sai ya koma wata jam'iyyar ta masu hamayya.
"Babu yadda za a yi ƙasa ta ci gaba a ƙarshin mutum ɗaya," in ji Bakary.
Muhimmancin arewacin Kamaru

Asalin hoton, Getty Images/Collage
Arewacin Kamaru da ya ƙunshi lardunan Adamawa da Arewa da kuma Arewa Mainisa na taka muhimmiyar rawa a zaɓen jamhuriyar.
Bayanai sun nuna cewa akwai masu ƙuri'a fiye da miliyan biyu a yankin Arewacin da ke iya sauya alƙiblar zaɓe.
Aƙalla mutum miliyan takwas ne suka yi rijistar zaɓe daga cikin mutum miliyan 30 na yawan al'ummar jamhuriyar.











