Paul Biya: Shugaban ƙasar da ke ƙara kunyata masu jita-jitar mutuwarsa

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Paul Melly
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai Sharhi kan harkokin ƙasashen Afirka
- Lokacin karatu: Minti 5
Jita-jita game da lafiya da kuma halin da Shugban Kamaru Paul Biya mai shekara 91 a duniya yake ciki, sun zamo babban batun da ake magana a kai a sassan Afirka a wannan makon.
Bayan halartar taron China da Afirka a birnin Beijing a farkon watan Satumba, bai zo da mamaki ba da ba a gan shi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya ba, UNGA.
Amma kasancewar ba a ji ɗuriyarsa ba a taron makon nan na ƙasashe masu magana da harshen Faransanci a arewacin Paris, sai raɗe-raɗi ya kaure musamman a shafukan sada zumunta saboda rashin ganinsa a bainar jama'a tsawon kusan wata ɗaya.
Jakadan Kamaru a Faransa ya dage cewa Biya yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana Geneva - wurin da ya saba yada zango idan ba ya gida.
Sauran majiyoyi sun bayyana cewa ya yi haka ne saboda yana buƙatar hutu bisa kulawar likitoci bayan taruka da dama da ya yi a Yuli da Agusta.
Shi ne shugaban ƙasa a Afirka mafi tsufa kuma na biyu da ya fi daɗewa bayan Shugaba Toeodoro Obiang Nguema na Eguitorial Guinea, mai maƙwabtaka .
Waɗannan alamu ba su wadatar ba a ci gaba da yin canki-canka game da halin da Biya ke ciki a kafafen yaɗa labaran Afirka.
A ƙarshe dai kakakin gwamnati, Rene Sadi ya fitar da sanarwa ta musanta raɗe-raɗin a hukumance inda ya ƙara da cewa shugaban zai koma ƙasar "cikin ƴan kwanaki masu zuwa".
Sannan babban jami'in ofishin da ke kula da shugaban ƙasar wanda ke tare da shi a Geneva, ya nanata cewa Biya yana cikin ƙoshin lafiya".
Kamaru tana riƙe da wani muhimmin wuri, a matsayin hanyar zuwa Chadi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Baya ga fafutukar murƙushe ayyukan masu iƙirarin Jihadi a tafkin Chadi, tana kuma ƙoƙarin shawo kan matsalar rikici a yankunanta da ke magana da Turancin Ingilishi.
Biya dai shugaba ne da bai cika halartar tarukan shugabannin Afirka ba.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ko a gida, da yanayin jawabinsa na taka-tsan-tsan da kuma furuci na aiki da hankali, Biya ya kwashe tsawon shekaru yana zaɓar mutanen da suke tafiyar da harkokin gwamnati da kuma kula da bayanai masu muhimmanci zuwa ga Firaminista.
Jita-jitar mutuwarsa lamari ne da lokaci zuwa lokaci ake yi, galibi saboda rashin jin ɗuriyarsa.
Amma wannan salo na yin luf ya yi hannun riga da hanyar da ya bi ya hau karagar mulki a 1982, tare da wanda ya gada, Ahmadou Ahijdo, inda ya yi alkawarin samar da sauyi kafin ya yi wa kujerar shugabanci riƙon da babu wani mai ƙalubalantarsa ko kuma zanga-zanga da ya iya kaɓar da ita.
Tun nasarar da ya yi bayan tsallake rijiya da baya a zaɓen 1992, Biya ya yi ta doke abokan karawarsa a siyasa wataƙila saboda taimakon da yake samu daga murɗe zaɓe da kuma rarrabuwar kai tsakanin ƴan hamayya.
A yanzu, yayin da wa'adin mulkin Biya karo na bakwai ke ƙarewa a Nuwamban 2025, magoya baya suna ƙara roƙonsa da ya yi tzarce.
Masu suka na ganin lokaci ya kai da za a miƙa ragamar shugabancin Kamaru ga matasa da za su iya magance matsalolin ƙasar su kuma duba damarmakin samar da cigaba cikin sauri ta hanyoyi daban-daban.
A 2016, malamai da lauyoyi a yankuna biyu da ke amfani da Turancin Ingilishi, kudu maso yamma da arewa maso kudu, sun yi zanga-zanga kan yadda aka gaza tabbatar da ƴancin Turanci da ayyukan jama'a yadda ya kamata.
Da a ce Biya yana mayar da martani cikin gaggawa da wani tsari mai karamci da kakkausar murya cikin tsarin garambawul, wataƙila zai iya magance rashin gamsuwar mutane tun da wuri kuma magance afkawa cikin mummunan artabu tsakanin jami'an tsaro da mayaƙa da ke neman ɓallewa.
Daga bisani Biya ya gabatar da wasu sauye-sauye domin biyan buƙatun yankunan da ke amfani da Turancin Ingilishi da kuma fadin ƙasar don miƙa iko ga majalisun yanki.
Sai dai wasu lokutan mutane suna daɗewa kafin su ga sauyi a ƙasa - ba a kafa irin wannan tsarin ba sai shekaru da dama bayan da amincewa da dokar ta asali.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai wasu ƴan Kamaru ba su da matsala da salon Biya na tafiyar da shugabancinsa da ƙudirinsa na bai wa Firaiministoci dama su tafiyar da wasu ayyuka na yau da kullum.
Suna ganin rawar da yake takawa a matsayin mai tattare da alama kusan kamar sarki.
A ranar 15 ga watan Agusta, misali, ya je Boulouris da ke Cote d'Azur a Faransa inda ya yi jawabi cike da bayani na tsawon minti 12 a wani taro na ƴantar da kudancin Faransa daga ƴan Nazi - wani aiki da sojoji da dama daga yankunan Faransa da Afirka suka ba da gudummawa.
Duk da rashin ganinsa a kai a kai a Younde, babban birnin Kamaru, yawanci ya kan koma ƙauyensa da ke kudanci ko wurin da ya fi son zama, otal ɗin Intercontinental Geneva - Biya ya cigaba da ɗaukan muhimman shawarwarin siyasa da dabaru.
Babban mai tsaron ƙofa a fadar shugaban ƙasa ta Etoudi shi ne Sakatare Janar na fadar shugaban, Ferdinand Ngoh Ngoh.
Wani tsarin mulkin Biya, a matsayinsa na shugaban ƙasa, yake ɓoye harkokinsa, yana janyo cece-kuce game da manufarsa ga zaɓen 2025 da kuma waɗanda suke iya gadar shi.
Sai dai wasu manyan fitattu a gwamnatin da ke samun bayanai da wuri kamar Laurent Esso da Rene Sadi, a yanzu sun wuce matsayin matasa.
Akwai ƙungiyoyin nuna goyon baya da ke son a miƙa ragama ga babban ɗan shugaban Franck Biya, ɗan kasuwa - duk da cewa Franck a karan kansa bai taɓa nuna sha'awar shiga siyasa ba ko ma ya ɓala burinsa kan gaka.
Amma a zamanin da ake ciki a Afirka, inda rashin gamsuwa da harkokin siyasa ke ƙaruwa, musamman a tsakanin matasan birni, yunƙurin cigaba da zama kan mulki na iya zuwa da haɗarurruka.
A Gabon mai maƙwabtaka, sojoji sun hamɓarar da shugaba Ali Bongo a shekarar da ta gabata bayan da gwamnatin ta yi murɗiya a zaɓen 2023 domin ba shi damar ci gaba da mulki karo na bakwai duk da rashin lafiyar da yake fama da ita.
Sannan lokacin da shugaban Senegal Macky Sall ya bayyana Macky Salla a matsayin wanda zai gaje shi, ba a zaɓe shi ba saboda masu zaɓe sun kaɗa ƙuri'a ga ɗan hamayya kuma matashi Bassirou Diomaye Faye.
Biya da makusantansa na iya samun ƙwarin gwiwa cewa za su iya kaucewa waɗannan lamura. Amma hakan na buƙatar nazartar ra'ayoyin jama'a musamman a tsakanin matasa da masu matsaiktan arziki da ke zaune a manyan birane kamar Yaounde da Doula.
Paul Melly manazarci ne da ke tare da shirin Afirka Programme a Chatham House a Landan.











