Abin da muka sani kan girgizar ƙasar Afghanistan wadda ta kashe mutum 600

Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Ma'aikatar cikin gida ta gwamnatin Taliban ta ce sama da mutum 600 ne suka mutu sanadiyyar wata mummunar girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.0 a gabashin ƙasar Afghanistan.

Girgizar ƙasar, wadda ba ta yi zurfi a cikin ƙasa ba, ta kai zurfin kilomita takwas, a wani yanki da ke da nisan kilomita 27 daga Jalalabad, birnin na biyar mafi girma a ƙasar.

Haka nan an ji motsin ƙasa har a birnin Islamad na ƙasar Pakistan, wanda ya ke da nisan kimanin kilomita 400 daga inda girgizar ta faru.

Yana da matuƙar wahala a tantance iyakar mutanen da lamarin ya rutsa da su da kuma ɓarnar da girgizar ta yi kasancewar yankin na da nisa kuma babu layin sadarwa mai ƙarfi.

An yi amannar cewa lamarin ya fi shafar lardin Kunar. Majiyoyi sun tabbatar wa BBC cewa a wani ƙauye ɗaya mutum 20 sun mutu, kuma wasu 35 sun jikkata.

Aikin ceto zai kasance mai matukar wahala kasancewar kashi 90 cikin dari na yankin yana da yawan tsaunuka.

Hanyoyin zuwa yankin sun kasance marasa girma, sannan kuma da dama daga cikin hanyoyin sun toshe sanadiyyar zabtarewar ƙasa wadda girgizar ta haifar.

Des soldats talibans et des civils transportent des victimes du tremblement de terre vers une ambulance à l'aéroport de Jalalabad, en Afghanistan, le 1er septembre 2025.

Asalin hoton, Reuters

Yankin da lamarin ya faru na cikin jimami ne bayan ambaliyar ruwa da ta fada masa a cikin ƙarshen mako.

Gwamnatin Taliban ta roƙi ƙungiyoyin ƙasashen duniya su taimaka mata wajen ayyukan ceto, musamman ta hanyar taimakawa da jirage masu saukar ungulu domin a samu kai wa ga wurare masu wahalar zuwa.

Mutane a wurare da dama da ke yankin sun rinƙa jin motsin ƙasa a cikin daren da ya gabata.

Wani mazaunin yankin mai suna Polad Noori, ɗan shekara 28 ya ce ya kwana tsaye a ƙofar gida domin gudun kada ya shiga ciki gini ya fado masa.

Ya shaida wa Sashen Afghan na BBC cewa sau 13 ƙasar tana jijjigawa a cikin dare, lamarin da ya sanya mutane da dama suka yi cirko-cirko a kan tituna.

"Ban taɓa ganin girgizar ƙasa mai tsanini irin wannan ba a rayuwata," in ji shi.

Hotunan yadda girgizar ƙasar ta tagayyara mutane

Hotuna daga ƙauyen Mazar Dara, lardin Kunar, sun nuna yadda mutanen da girgizar kasar ta ranar Lahadi suka yi sansani a wani fili domin samun mafaka.

Mutanen da girgizar ƙasa ta rutsa da su a Afghanistan

Asalin hoton, Reuters

Mutanen da girgizar ƙasa ta rutsa da su a Afghanistan

Asalin hoton, Reuters

Masu aikin ceto

Asalin hoton, x.com/@ARCSAfghanistan

Bayanan hoto, Masu aikin ceto

Me ya sa ake yawan samun girgizar ƙasa a Afghanistan?

Des personnes récupèrent leurs biens parmi les décombres de leur maison dans le district de Zinda Jan, touché par un tremblement de terre, à Herat, en Afghanistan, le 10 octobre 2023.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, MDD ta bayyana cewa girgizar ƙasa da aka samu a 2023 ta hallaka kimanin mutum 1,500
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Afghanistan na yawan fuskantar girgizar ƙasa kasancewar tana a wani yanki ne da ke a tsakiyar inda farantar ƙarƙashin ƙasa na duniya suka haɗu, wato farantan India da na Eurasia.

A watan Oktoban 2023, girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.3 ta faru a lardin Herat da kudancin ƙasar, inda ta kashe mutum 1,500, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar.

Ta kasance mai muni saboda ta faru ne a sama-saman ƙasa, inda take da zurfin kilomita 14 kacal a cikin ƙasa.

Girgizar ƙasar da ta faru ranar Lahadi ta faru ne a sama-sama, fiye da ta 2023, inda wannan ta faru a wuri mai zurfin kilomita takwas kacal.

Haka nan mutane a Afghanistan na cikin hatsarin shiga ibtila'i idan girgizar ƙasa ta faru kasancewar suna mafi yawa suna yin gine-gine ne da katakai ko bulon ƙasa wadanda ba su da ƙwarin jure wa girgizar.

Haka nan ana samun ɓarna sosai sanadiyyar zabtarewar ƙasa da girgizar ƙasar ke haifarwa a wurare masu yawan tuddai, waɗanda sukan rushe gidaje da tsohe hanyoyin rafuka.

Haka nan zabtarewar ƙasar na tsohe hanyoyi, lamarin da ke hana kai kayan agaji zuwa ƙauyuka masu nisa.