Waɗanne albarkatun ƙasa ne Trump ke son Amurka ta kwasa daga Ukraine?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Rebecca Thorn
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Marubuci, Anna Kundirenko
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Ukraine
- Marubuci, Navin Singh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service Environment correspondent
- Lokacin karatu: Minti 6
Ukraine ta amince da sharuɗɗan gagarumar yarjejeniyar da za ta bai wa Amurka damar iko da wasu ma'adanan ƙasa na Ukraine, kamar yadda firaiministan Ukraine ya tabbatar.
Ukraine na fatan cewa yarjejeniyar - wadda za ta bai wa Amurka iko da wani ɓangare na kuɗaɗen da ke fitowa daga Ukraine - za ta ƙarfafa wa Amurka gwiwar kare Ukraine idan wani yaƙin ya sake ɓarkewa da Rasha bayan tsagaita wuta da ake sa ran cimmawa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yarjejeniyar za ta taimaka wa mutanen Amurka "su dawo da kudin da suka kashe" na tallafin da suka tura wa Ukraine a lokacin yaƙi, tare da bai wa Ukraine ƙwarin gwiwar "yaƙi" da Rasha.
Dagewar da Trump ya yi kan yarjejeniyar ya tabbatar da muhimmancin waɗannan ma'adanai masu ƙaranci a duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Waɗanne ma'adanai ne masu wahalar samu?
"Ma'adanai masu daraja" na nufin wasu tarin ma'adanai guda 17 da ke ƙunshe da wasu sanadarai waɗanda ake amfani da su a harkar ƙere-ƙeren zamani.
Waɗannan ma'adanai na da muhimmanci sosai wajen ƙera wayoyin salula, da kwamfuta da kayan aikin asibiti da sauran su.
Ma'adanan sun haɗa da: Sc – scandium, Y – yttrium, La – lanthanum, Ce – cerium, Pr – praseodymium, Nd – neodymium, Pm – promethium, Sm – samarium, Eu – europium, Gd – gadolinium, Tb – terbium, Dy – dysprosium, Ho – holmium, Er – erbium, Tm – thulium, Yb – ytterbium, Lu – lutetium.
Ana kiran su "masu wuyar samu ne kasancewar ba kasafai ake samun su da yawa a wuri ɗaya ba duk kuwa da cewa akwai su a kusan kowane yanki na duniya.
Waɗanne ma'adanai Ukraine ke da su?
Ukraine na da 21 daga cikin sanadarai 30 da Tarayyar Turai ta bayyana a matsayin "abubuwan sarrafawa masu matuƙar amfani", wanda ya kai kashi 5% na irin waɗannan ma'adanai da ake da su a faɗin duniya.
Akasarin yankunan da ke da arziƙin waɗannan ma'adanai na yankin da akasarinsa a yanzu ke ƙarƙashin ikon Rasha ne.

Masana na cewa duk da cewa an gano wurare da dama da za a iya samun irin waɗannan ma'adanan ƙasa, za su kasance masu amfani ne idan an same su da yawa jibge a wani wuri ta yadda za a iya cin gajiyarsu.
"Ƙiyasin da aka yi a yanzu ƙiyasi ne kawai," in ji Adam Webb, wani masanin albarkatun ƙasa.
"Akwai jan aiki a gaba kafin a tabbatar cewa akwai isassun ma'adanan a ƙarƙashin ƙasa waɗanda za a iya amfana da su."

Game da sauran ma'adanan ƙasa da ke jibge a Ukraine, Jaridar Forbes a Ukraine ta ce kashi 70% na ma'adanan na jibge ne a yankin Donetsk da Dnipropetrovsk da kuma Luhansk. Saboda haka suna a yankuna ne da Rasha ta mamaye kuma har yanzu take iko da su.
Baya ga ma'adanai masu wuyar samu, Ukraine kuma tana da ma'adanan da ake kira 'masu matuƙar muhimmanci', kamar Lithium.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Ukraine ta ce ƙasar na da ma'adanin Ukraine da yawansa ya kai tan 450,000 jibge a ƙasar. Ba a haƙo shi ba duk kuwa da cewa akwai shirye-shiryen yin hakan.
Rasha ta mamaye aƙalla yankuna biyu da ke da yawan ma'adanin lithium: wato Shevchenkivske da ke Donetsk da kuma Kruta Balka da ke yankin Berdyansk.
Yankin Kirovohrad mai arziƙin lithium har yanzu na ƙarƙashin ikon Ukraine.
Me ya sa Trump ya ƙwallafa rai kan ma'adanan?

Asalin hoton, Getty Images
Abin da ya sanya Amurka ke son yin iko da kuma haƙo ma'adanai masu muhimmanci na Ukraine shi ne domin yin gasa da China, wadda a yanzu ita ce ta gaba a duniya wajen samar da irin waɗannan ma'adanai.
A tsawon gwamnan shekaru da suka shuɗe, China ta kasance jagora wajen haƙowa da sarrafa ma'adanan ƙasa masu muhimmanci, inda take da kashi 60 zuwa 70% na samar da ma'adanan, kuma tana da ƙarfin sarrafa kashi 90% na irin waɗannan ma'adanai da duniya ke buƙata.
Akwai yaƙinin cewa dogaron da Amurka ke yi da China kan wannan ɓangare abu ne da zai damu gwamnatin Trump - bisa la'akari da tsaro da kuma tattalin arziƙi.
Ana buƙatar irin waɗannan ma'adanai wajen ƙere-ƙren abubuwan fasaha masu matuƙar muhimmanci - kamar motoci masu amfani da lantarki da kuma kayan aikin soji.

Asalin hoton, Getty Images
'Ruɗani', in ji Navin Singh Khadka, wakilin kare muhalli na BBC
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A bayyane za a ga cewa wannan tamkar wani ruɗani ne.
Trump ya bayar da umarnin faɗaɗa samar da makamashi mai gurɓata muhalli, inda ya yi watsi da tsare-tsaren makamashi maras gurɓata muhalli. Amma kuma a lokaci guda yana son samo 'ma'adanan ƙasa masu matuƙar muhimmanci' - waɗanda ke da matuƙar muhimmanci a ƙoƙarin komawa amfani da makamashi maras gurɓata muhalli - daga kowane wuri da ya ga zai iya.
Waɗannan ma'adanai su ne tubalin da ake buƙata wajen samar da lantarki da makaman soji da kuma abubuwan sufuri, har ma da ƙirƙirarriyar basira (AI).
Trump ya sanar da faɗaɗa harkar Ƙirƙirarriyar Basira (AI) a Amurka. Kuma hakan zai buƙaci samun ma'adanai masu matuƙar muhimmanci masu ɗimbin yawa - musamman ma'adanin copper, da silicon, da palladium da sauran ma'adanai masu wahalar samu.
Kuma dama a yanzu samar da waɗannan ma'adanai masu matuƙar muhimmanci ya yi ƙasa, lamarin da ya sanya ƙoƙarin duniya na komawa amfani da makamashi mai tsafta ke tafiyar hawainiya.

Asalin hoton, Getty Images
Masana na cewa kakagidan da China ta yi a ɓangaren samar da ma'adanai masu matuƙar muhimmanci, ciki har da masu wahalar samu, shi ne babban dalilin da ya sa Amurka ke son yin iko da ma'adanan Ukraine.
Saboda ƙoƙarin da ta yi wajen samar da fasahar a tsawon shekaru, a yanzu China ce ke iko da harkar samar da tataccen sinadaran graphite da dysprosium ɗari bisa ɗari.
Sai kuma kashi 70% na samar da ma'adanin cobalt da kuma kashi 60% na tataccen ma'adanin lithium da manganese, in ji Hukumar kula da tsaftataccen makamashi ta duniya.
Haka nan China ɗin ce a kodayaushe ke samar da ma'adanai masu ƙaranci a doron ƙasa, kuma tana iko da wuraren haƙo ma'adanai da dama a faɗin duniya, inda ta mallaki manya-manyan filayen haƙo ma'adanai a Afirka, da Asia da Kudancin Amurka.
Yanzu Amurka na kallon yankuna kamar Ukraine da Greenland a matsayin wuraren da za ta yi amfani da su domin cike gurbin wuraren da take samun irin waɗannan ma'adanai.

Asalin hoton, Getty Images











