Mece ce USAID kuma me ya sa Trump ya dage sai ya rusa ta?

Sajad yaro ne mai shekara bakwai da iyayensa suka bata a lokacin ambaliyar ruwa da aka fuskanta a Pakistan - yana cikin milyoyin yaran da USAID ke taimakawa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sajad yaro ne mai shekara bakwai da iyayensa suka bata a lokacin ambaliyar ruwa da aka fuskanta a Pakistan - yana cikin milyoyin yaran da USAID ke taimakawa
    • Marubuci, Sean Seddon
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ana cikin rashin tabbas kan makomar hukumar agaji ta Amurka bayan ma'aikata sun ce an hana su shiga wurin aiki sannan gwamnatin Trump na shirin hadesu wuri guda da ma'aikatar harkokin waje.

Hukumar bada agaji ga kasashen duniya ta Amurka, USAID za ta ci gaba da aiki a matsayin wani bangare na ma'aikatar harkokin waje, sai dai tsarin ya kunshi rage kudaden da take kashewa a ayyukanta da ma'aikata, a cewar kafar CBS da ke da hadin-gwiwa ko hulda da BBC.

A ranar Litini, Sakataren harkokin waje, Marco Rubio ya zargi shugabancin USAID da zagon-kasa tare da jaddada cewa shi ne mukadasshin shugabanta a yanzu.

Shugaba Donald Trump na Amurka da kuma daya daga cikin manyan masu bashi shawarwari, attajiri Elon Musk, sun jima suna sukar ayyukan hukumar.

Amma kuma yanke hukunci kawo karshen ayyukanta wani abu ne na daban da babu shakka zai yi matukar tasiri a ayyukanta na agaji a fadin duniya.

Mece ce USAID kuma me take yi?

Hukumar bada agaji ta Amurka, USAID an kirkire ta a shekarun 1960 domin taimaka wa ayyukan agaji a madadin gwamnatin Amurka a kowanne yanki na duniya.

Tana da ma'aikata dubu 10, wanda kashi biyu bisa uku na aiki a ketare. Tana da cibiyoyi a sama da kasashe 60, sannan tana ayyuka daban-daban a sauran kasashe.

Sai dai galibin ayyukanta wasu kungiyoyin take bai wa kudi su aiwatar, nata shi ne sa ido da tabbatar da cewa an kashe kudaden bisa tsari.

Ayyukanta na da dimbin yawa. Misali, USAID ba tallafin abinci kadai take bayarwa a kasashe masu fama da yunwa ba, tana kuma aiki wajen gane inda za a fuskanci fari, da kuma inda za a bukaci agajin gaggawa na yiwuwar karancin abinci a nan gaba.

Galibin kasafin kudin USAID ana kashe su ne a fannin lafiya, irin su rigakafin Polio a kasashen da cutar ke yaduwa da kuma taimakawa wajen dakile yaduwar cututtuka da ake yiwa kallon annoba.

Sashen BBC Media Action mai fadakarwa da kuma bunkasa ayyukan 'yan jarida a kasashe masu tasowa, da ke samun tallafi daga kungiyoyi, na samun tallafi daga USAID.

Bayan wani rahoto da aka fitar a 2024, ya nuna USAID ta ba wa sashen tallafin dala miliyan 3.23, wanda shi ne tallafi na biyu mafi yawa da sashen ya samu a wannan shekarar.

Nawa USAID ke ci wa gwamnatin Amurka?

Wasu bayanai na gwamnati, sun nuna cewa Amurka ta kashe dala biliyan 65 kan ayyukanta na agaji a 2023.

An raba wadannan kudade ne tsakanin ma'aikatu da hukumomi, amma kasafin USAID ya kwashe sama da rabin kudin da ya kai dala biliyan 40.

Galibin kudaden an kashe su ne a yankin Asiya, kudu da hadamar Saharar Afirka da Turai - kan ayyukan agaji na Ukraine.

Amurka ta fi kowacce kasa ta duniya kashe kudi a ayyukan agaji.

Idan aka sa a jeren kididdiga, Burtaniya ce ta hudu wajen kashe kudi a fannin agaji. A 2023, ta kashe fam biliyan 15.3 - wanda bai fi kaso ɗaya bisa huɗu na kudaden da Amurka ta kashe ba.

Me ya sa Donald Trump da Elon Musk ke son rufe USAID?

Trump ya jima yana sukar yadda ake kashe kudaden Amurka ga kasashen ketare kuma ya sha cewa kwalliya ba ta wani biyan kudin sabulu ga wadanda kudaden harajinsu ake kwashewa, ma'ana kudden 'yan kasa Amurka ne. Ya sha ambato USAID yana cewa shugabaninta ma ba su da hankali.

Kawo karshen ayyukan hukumar da alama zai samu goyon-baya. Kuri'un jin ra'ayi ya sha nuna cewa Amurkawa na son a rage kudaden da ake kashewa kasahen ketare.

A cewar rahoton Chigaco Council on Global Affairs, tun shekarun 1970 Amurka ke adawa da yadda kasar ke kashewa ketare kudadensu.

Daya daga cikin matakan Trump bayan hawa mulki shi ne sanya hannu kan dokar zartarwa da ke dakatar da duk irin wadannan kashe-kashe kudin na tsawon wata uku domin sake nazartar ayyukansu.

Elon Musk da Donald Trump

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Elon Musk da Donald Trump sun kasance masu sukar yada ake kashe kudaden kasar a ketare

Shirye-shiryen da suka hada da samar da magunguna ga kasashe matalauta da samar da ruwan sha mai tsafta an dakatar da su a dare guda. Wani ma'aikacin agaji ya fada wa BBC cewa dakatar da ayyukan tamkar "anyi girgizar kasa ne a kasashen da suke taimakawa".

Rashin jituwa tsakanin fadar White House da USAID ya ta'azzara a karshen mako lokacin da masu yi wa Elon Musk aiki - wanda Trump ya daurawa alhaki sanya ido da rage kudaden da ake kashewa a kasafin tarayya - an datse su daga samun bayanan na kudaden USAID a hedikwatarta. Nan take aka samu rahoton dakatar da manyan jami'ai biyu da maye gurbinsu, a cewar rahotanni.

A ranar Litinin, Musk - da ke zuba bayanai a shafinsa na X, mallakinsa - ya ce; "Kan batun USAID, mun bibbiyi abin tare da shugaban kasa kuma mun yanke hukunci rufeta."

Shafin USAID ya daina aiki kuma an fadawa ma'aikatanta su zauna a guda a ranar Litinni.

Shin Donald Trump zai iya rufe USAID?

Duk da cewa fadar White House nada matukar tasiri a ayyukan USAID, karfin rushe ta ya wuce nan.

USAID ta kafu ne bayan majalisa ta samar da doka ta taimaka ketare a 1961. Dokar ta tilasta kafa hukuma ta gwamnati da za ta rinka taimaka wa ayyukan jin-kai a ketare.

Bayan nan, shugaba a wancan lokaci John F Kennedy ya kafa USAID ta hanyar bada umarnin zartarwa. An sake amincewa da wata doka a 1998 wanda ya tabbatar da kafuwar USAID a matsayin mai cikakken 'yancin ayyukanta.

A takaice dai, Shugaba Trump ba zai iya rusa hukumar lokaci guda ba kawai ta hanyar sanya hannu a umarnin zartarwa, kuma duk wani yunkuri da ya kaucewa doka na iya tilasta a kalubalance shi a gaban kotu da majalisa.

Military personnel loading equipment onto the back of a plane

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Cikin ayyukan baya-bayanan da USAID ta aiwatar akwai taimakawa Turkiyya da tallafi a lokacin da suka fuskanci zabtarewar kasa

Kawo karshen aikin USAID na nufin zai majalisa ta shiga batun - kuma jam'iyyar Reublican ta Trump rinjaye kadan take da shi a majalisun kasar biyu.

Daya daga cikin abin da gwamnatin Trump ke dubawa shi ne yiwuwar mayar da USAID wani bangare a ma'aikatan harkokin ketare, wanda dama adawar ita ce ta kasance mai zaman kanta.

Kuma irin wannan tsari babu mamaki ya samu shiga ganin cewa a 2020, Firaministan Burtaniya, Boris Johnson ya hade ma'aikatar harkokin ketare da Ofishin da ke kula da huldar kasashen ketare.

Mene ne tasirin rusa USAID?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

La'akari da yawan kudaden da Amurka ke kashewa a wannan bangare, ko wane irin sauyi kan yadda ake kashe kudi babu shakka za a ga tasirinsa a fadin duniya.

Ayyukan USAID sun hada da samar da kafar roba ga sojojin da aka jikkata a yankin Ukraine, da tsaftacce yankunan da suka fuskanci annoba da shawo kan Ebola a Afirka. Tasiri abu ne da za a ji a duniya.

Bayan sanarwar dakatar da ayyukan hukumar na kwanaki 90, Sakataren harkokin waje, Marco Rubio ya ce, 'kowacce dala' da ake kashewa dole a bibbiya domin tabbatar da cewa an yi adalci kuma Amurka ta gamsum haka zalika cigabanta.

'Yan siyasa daga jam'iyyar Democratic sun ce matakin ya saba ka'ida kuma sun ce hakan zai yi tasiri ga harkokin tsaro, inda suka bada misali da abin da ya faru a gidan yarin Syria, da ake tsare da dubban mayakan IS, da mutane suka rinka barin aiki saboda katse kudaden da ake basu na wani lokaci.

Trump ya bayyana karara cewa yana son duk kudaden da ake kashewa harkokin ketare ya zo daidai da muradun Amurka na fifita bukatar 'yan kasa da basu fifiko.

Sai dai kuma ana diga ayar tambaya kan nawa to Amurka za ta rinka kashewa kan harkokin ketare a shekaru masu zuwa nan gaba, tunda Musk ya nuna cewa shi da Trump burinsu shine rage bilyoyin kudade da gwamnati ke kashewa a kasafinta.