An kafa kwamitin duba madatsun Najeriya don kaucewa iftila'in ambaliyar ruwa

Asalin hoton, Weather monitor
Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamitin kwararru da zai yi nazarin halin da dukkan madatsun ruwan kasar ke ciki bayan fashewar madatsar Alau a jihar Borno.
Wannan dai na daga cikin kudurorin da aka cimma a taron majalisar zartarwar kasar da aka yi a ranar Litinin 23 ga watan Satumbar 2024, karkashin jagorancin shugaban Bola Ahmed Tinubu.
Ministan yada labarai na Najeriya, Alhaji Mohammed Idris, ya shaida wa BBC cewa, a kowanne lokaci idan abu ya faru mara dadi ko kuma wanda za a dauki darasi a kansa, to gwamnati kan sake lamarin don kaucewa sake afkuwar hakan.
Ya ce, "Ba dai-dai bane idan an samu makamancin abin da ya faru a Maiduguri a yi shiru kamar babu abin da ya faru, hakan ne ya sa majalisar zartaswa ta kasa ta yi tunanin cewa ba kawai maganar madatsar ruwa ta Alau ba, akwai bukatar a sake duba duk wata madatsar ruwa da ke cikin Najeriya."
Ministan yada labaran ya ce, "Kwamitin da aka kafa yanzu zai sake duba dukkan madatsun ruwan don tabbatar da cewa ba a sake samun afkuwar irin abin da ya faru a Maiduguri ba."
"Duk yawan madatsun ruwan da muke da su a kasarnan, gwamnati na da halin da za ta iya duba su, sannan kuma an kafa kwamitin ya yi wannan aikin ne ba don daminar bana ba kawai, har shekaru masu zuwa."
Alhaji Mohammed Idris, ya ce a yanzu duk abin da ya kamata gwamnati ta yi za ta yi, kuma dangane da batun cikakken bayani a kan wannan kwamiti ma'ana su wa ya kunsa nan gaba duk za su sanar.
Ya ce, "Abin da zan fada kawai shi ne shugaban wannan kwamiti na duba madatsun ruwan shi ne ministan albarkacin ruwa da kuma tsaftar muhalli, sauran ‘yan kwamitin kuma za a ji su a gaba."
Gomman mutane ne suka rasa rayukansu wasu miliyan biyu kuma suka rabu da muhallansu sakamakon wannan fashewar madatasar ruwa ta Alau.
Birnin Maiduguri ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau, lamarin da ya haddasa ruwan ya malale dubban gudaje da makarantu da asibitoci da tituna da gine-ginen gwamnati da ma babban asibitin koyarwa na jihar da ma jami’ar jihar.
Bayanai sun ce lamarin ya fi muni a unguwannin Fori da Galtimari da Gwange da kuma Bulabulin.
Kazalika ambaliyar ambaliyar ta shafi gidan adana namun daji, lamarin da ya sa dabbobi suka fita kan titunan suna gararamba.
Ambaliyar dai ita ce mafi muni a jihar Borno cikin shekaru 30.














