'Ban san halin da mijina makaho yake ciki ba a ambaliyar Maiduguri'

Bayanan bidiyo, 'Ban san halin da mijina makaho yake ciki ba a ambaliyar Maiduguri'
Lokacin karatu: Minti 1

Mutanen da ambaliyar Maiduguri ta raba da gidajensu kuma suke samun mafaka a sansanonin 'ƴan gudun hijira, na kakowa a kan rashin abinci.

Da dama cikin ƴan gudun hijirar mata ne da ƙananan yara.

Wasu da BBC ta zanta da su a ɗaya daga cikin sansanonin da aka tanada sun ce abincin da ake kai wa ba ya isa, kuma babu ƙwaƙƙwaran tsarin wajen rabawa, abin da ya sa, masu rauni da dama ba sa iya samu.

Gwamnatin jihar Borno ta ce kimanin mutum miliyan biyu ne ambaliyar ruwan ta shafa.

Wata uwa ta ce har yanzu ba ta ji ɗuriyar mijinta mai larurar rashin gani da ta baro a gida ba, inda ta kuɓuto da ƴaƴansu bayan ambaliyar ruwan ta fi ƙarfinsu.