Mene ne taron COP30 kuma me ya sa yake da muhimmanci?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Mark Poynting
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Climate reporter, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Shugabannin duniya za su taru a wani babban taro da Majalisar Ɗinkin Duniya za ta ɗauki nauyi domin tattauna hanyoyin da za su bi domin magance matsalolin sauyin yanayi.
Za a yi taron na COP30 ne shekara 10 bayan yarjejeniyar yaƙi da matsalolin sauyin yanayi da aka tsara a birnin Paris, inda aka amince ɗumamar yanayi ba zai haura matakin 1.5 a ma'aunin celcius ba.
Mene ne taron COP30?
COP30 taron sauyin yanayi ne na Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 30, inda ƙasashen duniya ke zama domin tattauna batutuwa da suka shafi sauyin yanayi.
COP na nufin "Conference of the Parties". "Parties" a nan na nufin kusan ƙasashe 200 da suka sa hannu a yarjejeniyar sauyin yanayi ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta shekarar 1992.
Yaushe za a yi taron COP30?
Za a yi taron COP30 ne daga ranar Litinin 10 ga Nuwamba zuwa Juma'a 21 ga watan Nuwamba.
Amma shugabannin ƙasashen duniya za su zauna a ranakun Alhamis 6 ga Nuwamba da Juma'a 7 ga watan na Nuwamba.
A ina za a yi taron?
A ƙasar Brazil za a yi taron, wanda shi ne karon farko da za a yi taron a babban birnin ƙasar.
Ƙasashen da suke cikin yarjejeniyar ne suke cire ƙasa guda ɗaya da za su gudanar da taron, amma ana zagayawa ne kamar yadda ake yi a gasannin ƙwallon ƙafa.
Amma kai taron birnin Belem a wannan karon ya haifar da matsala saboda rashin ingantattun hanyoyi da rashin otel masu kyau a birnin.
Wasu wakilan sun fuskanci matsala wajen neman masauki, lamarin da ya sa ake tunanin ƙasashe marasa ƙarfi za su fara rasa damar ɗaukar nauyin taron.
Su wane ne mahalarta taron?

Asalin hoton, Getty Images
Wakilai daga ƙasashen duniya za su halarci taron, amma har zuwa yanzu akwai shugabannin ƙasashen duniya da dama da ba su tabbatar da zuwansu ba.
Sannan har yanzu babu tabbacin irin wakilcin da Amurka za ta tura.
Jim kaɗan bayan rantsar da shi a watan Janairu, Trump ya yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar Paris.
Ya taɓa irin wannan yunƙurin a wa'adinsa na farko, amma sai Joe Biden ya fasa bayan ɗarewarsa mulki a 2021.
Bayan ƴansiyasa da za su halarci taron, akwai masana diflomasiyya da ƴanjarida da ƴan gwagwarmaya da suka za su haɗu domin tattaunawa.
Me ya sa taron ke da muhimmanci?
Taron na COP30 ya zo a daidai lokacin da ake matuƙar buƙatar lalubo hanyoyin fuskantar matsalolin sauyin yanayi.
A birnin Paris a shekarar 2015, kusan ƙasashe 200 ne suka amince a yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa ɗumamar yanayi ba ta haura matakin 1.5 ba a ma'aunin celsius.
Amma akwai alamomin da ke nuna cewa ɗumamar za ta iya haura matakin 2 a ma'aunin na celsius.
Duk da amfanin da makamashi mara illa irin su amfani da hasken rana na ƙaruwa sosai, har yanzu tsare-tsaren ƙasashen duniya sun gaza ɗaura ɗambar cika yarjejeniyar ta Paris.
Me za a tattauna a taron COP30?
Ana sa ran za a tattauna ne kan samar da tsare-tsaren da za su inganta yarjejeniyar da aka cimmawa a tarukan COP na baya:
Makamashi mara illa
A taron COP28 a 2023, ƙasashen duniya sun amince a fara komawa amfani da makamashi mara illa.
Kuɗi
A taron COP29, ƙasashe masu arziki sun amince su ba ƙasashe masu tasowa aƙalla $300bn zuwa 2035 domin taimakonsu wajen magance matsaloliln sauyin yanayi. Amma kuɗin ya yi kaɗan matuƙa idan aka kwatanta da abin da ƙasashen ke nema.
Haka kuma an tsara za a nemi kusan dala triliyan 1.3 daga kamfanoni masu zaman kansu, amma hakan bai samu ba.
Yanayi
Wani abin da ake tunanin za a tattauna a taron shi ne yunƙurin assasa asusun kula da yanayi da za a kira "Tropical Forests Forever Facility"
Za a samu canji?
Taron dai yana fuskantar ƙalubale babba musamman saboda yanayin ƙarfin ikon Trump da kuma lura da irin yadda bai ba taron muhimmanci ba.
A jawabinsa na Majalisar Ɗinkin Duniya a watan Satumba, Shugaban Amurka ya ce zai ci gaba da haƙo mai da gas, kuma ya yi watsi da wasu tsare-tsaren Biden na sauyin yanayi.
A watan Oktoba Amurka ta yi ƙafar ungulu kan yunƙurin yaƙi da fitar da sinadarai da suke jawo ɗumamar yanayi a duniya.
Wasu ƙungiyoyin fafutika kamar Greta Thunberg sun zargi tarukan COP na baya da rashin takaɓus wajen tilasta ƙasashe da kamfanoni masu zaman kansu wajen ɗaukar matakan da suka dace.
Sai da Majalisar Ɗinkin Duniya na nanata cewa akwai nasarori da dama aka samu dag tarukan na baya, kuma za a ɗaura ne daga inda aka tsaye.











