Yaƙin kasuwanci ya turnuƙe tsakanin China da Amurka - Me zai faru?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Yvette Tan, Annabelle Liang da Kelly Ng
- Aiko rahoto daga, Singapore
- Lokacin karatu: Minti 5
Yaƙin kasuwanci da ƙasashen Amurka da China ke tafkawa ba shi da alamun sassautawa bayan Beijing ta ci alwashin "ganin bayan lamarin" tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya lashi takobin sake lafta wa ƙasar ƙarin haraji.
Yanzu haka Trump ya ayyana harajin kashi 104% kan China, lamarin da zai sa kayayyakin China da ake shigarwa Amurka su dinga biyan kashi 104 idan aka haɗa da na baya da Trump ɗin ya sanar.
Wayoyin hannu masu basira, da sinadaran haɗa batiri, da kayan wasan yara, da na'urorin game, su ne mafi yawan kayan da China ke shigarwa Amurka. Amma kuma wasu abubuwan da yawa.
Yayin da wa'adin da Trump ya bayar ke shirin cika, wane ne zai fara zubar da makamansa?
"Kuskure ne a yi tunanin China za ta bayar da kai ta cire harajin da saka ita kaɗai," a cewar Afredo Montufar-Helu, wani babban mai bincike a sashen China Center na cibiyar The Conference Board.
"Ba wai kawai zai sa China ta zama raguwa ba, zai jawo Amurka ta ƙara neman wasu buƙatun. Yanzu mun kai wata gaɓa da za ta iya sakawa a daɗe cikin rikicin."
Kasuwannin hannun jari sun karairaye a duniya a makon da ya gabata lokacin da Trump ya sanar da ƙarin harajin kan kusan dukkan ƙasashen duniya.
A gefe guda kuma, China ta ƙaƙaba wa Amurka nata harajin na kashi 34 cikin 100, kuma Trump ya yi barazanar ƙarin kashi 50 idan China ba ta janye nata ƙarin ba.
Rashin tabbas ɗin na da yawa, inda ake tunanin wasu haraje-harajen na shirin fara aiki ranar Laraba. Akasarinsu za su shafi ƙasashen nahiyar Asiya ne. Haraji kan China zai zama kashi 54, sai kuma Vietnam (46) da Cambodia (49).
Wane martani ke mayarwa kan harajin?
China ta mayar da martani kan sawun farko na harajin da nata na ramuwar gayya kan wasu kayayyakin Amurka da ake shiga da su, da ƙayyade wasu ma'adanai, da kuma ƙaddamar da bincike kan ko kamfanonin Amurka kamar Google na daƙile sauran.
Yanzu ma ta sanar da ƙarin harajin yayin da take shirin zama da gagarumin ƙari.
Ta rage darajar kuɗinta na yuan domin ta ƙara yawan kayan da take fitarwa, kamfanonin da ke da alaƙa da gwamnati kuma na sayen kadarori a wani yunƙuri na kwantar da hankalin kasuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shirin tattaunawa tsakanin Japan da Amurka zai iya kwantar da hankalin masu zuba jari da ke neman farfaɗowa daga asarar da suka yi a makon nan.
Amma rikici tsakanin China da Amurka - wadda ta fi kowacce ƙasa fitar da kayayyaki a duniya - na ci gaba da jawo fargaba.
"Abin da muke gani shi ne wasa mai taken wane ne ya fi wani jure raɗaɗi. Mun daina magana kan wata riba ko amfani," in ji Mary Lovely, ƙwararriya kan alaƙar kasuwanci tsakanin China da Amurka a cibiyar Peterson Institute da ke binrin Washington DC.
Duk da jan ƙafar da tattalin arzikinta ke yi, "tabbas China za ta iya jure wa raɗaɗin ba domin guje wa nuna amincewa da abin da ta bayyana da harin Amurka," a cewarta.
Idan aka ƙaƙaba wa kayayyakin China haraji, hakan zai shafi hanyoyin samun kuɗin 'yan ƙasar masu yawa.
Abu ne mai wuya a iya cewa ga ranar da "harajin zai shafi rayuwar 'yan ƙasa amma dai nan kusa ne," a cewar wani ƙwararre Mista Coller. Ya ƙara da cewa Shugaba Xi "na fuskantar zaɓi mai wuya saboda tafiyar hawainiya da tattalin arzikin China ke yi".
Zai iya shafar kowa
Ba China ce kawai za ta ji raɗaɗin abin ba.
A cewar ofishin kasuwancin Amurka, Amurka ta sayo kayan dala biliyan 438 daga China a 2024, inda ita kuma ta kai kayan dala biliyan 143.

Asalin hoton, Getty Images
Babu tabbas game da inda Amurkar za ta nemo kayan da za ta maye gurbin na China cikin ƙanƙanin lokaci.
Ƙasashen biyu na da alaƙa sosai ta hanyoyi da yawa a fannin tattalin arziki - akwai kuɗaɗen zuba jari masu yawa daga ɓangarorin biyu, kamar yadda Deborah Elms ta bayyana, shugabar sashen kasuwanci a cibiyar Hinrich Foundation da ke Singapore.
"Akwai hanyoyin da ƙasashen za su iya lahanta junansu. Saboda haka zuwa yanzu abin bai yi muni ba tukunna, amma dai akwai hanyoyin da hakan za ta iya faruwa."
Sauran ƙasashen duniya sun zira ido domin ganin inda China za ta kai kayan da aka hana ta shigarwa Amurka.
Za su ƙare ne a kasuwannin nahiyar kudu maso gabashin Asiya, in ji Deborah. Kuma su ma waɗannan ƙasashe "na da nasu harajin da aka saka musu da kuma tunanin su ma inda za su kai nasu kayan domin sayarwa".
Ta yaya hakan zai ƙare?
Ba kamar yaƙin kasuwancin da suka yi a wa'adin Trump na farko ba, "ba a san abin da ke jawo wannan ƙarin haraje-harajen ba, kuma da wuya a iya hasashen inda lamarin zai ƙare daga nan," kamar yadda Roland Rajah ya yi bayani daga cibiyar Lowy Institute.
China na da hanyoyin da za ta iya ramawa, in ji shi, kamar ƙara rage darajar kuɗinta ko kuma matsa wa kamfanonin Amurka.
"Abin tambayar a nan shi ne za su iya yin haƙuri? Akwai ramuwa domin gudun raini, akwai kuma ramuwar yi wa abokin hamayya lahani. Babu tabbas ko China za ta kai ga wannan matakin. Ƙila ta yi hakan."

Asalin hoton, Getty Images
Wasu ƙwararru sun yi imanin cewa Amurka da China za su iya hawa teburin tattaunawa. Trump bai yi magana da Xi ba tun bayan komawa mulki wa'adi na biyu.
"Ina ganin Amurka na wuce gona da iri," in ji Elms. Sai dai ba ta amince 100 bisa 100 ba game da iƙirarin Trump cewa kasuwar Amurka na da riba sosai ta yadda babu ƙasar da za ta ƙi yin biyayya.
"Ta yaya za a kawo ƙarshen lamarin," a cewarta. "Lallai na damu da hanzarin da ake yi wajen rura wutar yaƙin. Kalubalen na da yawa a nan gaba kuma haɗarin da ke ciki na da girma sosai."











