Hancin robar da zai iya sanar da ku abincin da zai sa ku gudawa

Raz Jelinek, daga dama tare da dalibinsa Nitzan Shauloff, sun nuna na'urar da ke iya gano kamshi a hancin na zamani

Asalin hoton, Sensifi

Bayanan hoto, Raz Jelinek, daga dama tare da dalibinsa Nitzan Shauloff, sun nuna na'urar da ke iya gano kamshi a hancin na zamani
    • Marubuci, Stav Dimitropoulos
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology reporter

Kowane hanci yana da kusan sinadaran sunsuno kamshi guda 400 da suke iya gano kusan kamshi kala triliyan daban-daban.

Samar da kimiyya mai irin gwanancewar sunsuna irin haka, ba karamin jan aiki ba ne.

Amma da taimakon ci gaban da ake samu a bangaren kirkirarriyar basira ta AI, sabuwar na’urar hanci mai suna e-nose - na’urar sunsuna mai karfi da ke iya ganowa da taskance kamshi-sun fara samun ingancin aiki da sauri da sakamako mai kyau.

Masu son sabuwar kirkirar suna cewa fasahar za ta inganta hanyoyin yaki da yunwa.

Daya daga cikin ƙwayoyin cuta da suka fi janyo gurɓacewar abinci da suka fi illa ita ce ƙwayar bakteriya ta salmonella da E. Coli.

Dukkansu biyun nan suna da “lantarki” a tattare da su, inji Farfesa Raz Jelinek, wanda yake cikin wadanda suka kirkiri na’urar hanci mai suna 'Sensifi' kuma Farfesan ilimin sanadarai a Jami’ar Gurion da ke Negev a Isra’ila. “Suna da na'urar aikawa da lantarki a tattare da su.”

Na’urar ta e-nose wadda wani kamfanin Isra’ila ya assasa, tana dauke da wasu karafa guda biyu masu isar da lantarki da aka lullube da ƙananan sinadaran carbon.

Su ne suke sunsuno kamshi ko kuma duk abin da bacteria ta fitarwa da ake kira volatile organic compounds (VOC).

Latas din da ya gurbace na daga cikin manyan abubuwan da ke batawa mutane ciki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Latas din da ya gurbace na daga cikin manyan abubuwan da ke batawa mutane ciki
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kowane bacteria na fitar da warin ne na daban, wanda shi kuma yake fitar da alama daban a na’urar Sensifi din. Sai a nada alamar da ta fito ta hanyar amfani da kirkirarriyar fasahar AI, wadda ita kuma za ta duba rumbunta domin gano ko akwai irinsa da aka taba nada a baya.

Na’urar Sensifi da aka kaddamar a farkon shekarar nan an kirkire ta ne da burin yaki da gurbacewar abinci. Babban Jami’in Gudanarwar kamfanin,Modi Peled ya ce masu kamfanonin sarrafa abinci dole sai sun aika da abincinsu a musu gwajji, sannan su jira kwanaki kafin sakamako ya fito.

Amma ta hanyar amfani da na’urar Sensifi, e-nose, masu kamfanonin za su iya yin gwajin da kansu, sannan an ce ana samun sakamko a kasa da awa daya. Har yanzu ba su fitar da farashin na’urar ba, amma sun bayyana cewa zai zo da sauki. Kamfanin ya bayyana cewa za su samu kudade ne ta hanyar kudin shiga manhajarsu wato subscription.

“Hanyar gwajin abinci daya ake bi na kusan shekara 40 zuwa 50,” inji Peled. “Idan ba yanzu, fasahar AI ba ta shiga bangaren gwajin abinci ba.”

Gurbacewar abinci na daga cikin manyan matsaloli a duniya. A Amurka, mutum miliyan 48, ko kuma duk mutum daya a cikin shida suna rashin lafiya saboda gurbacewar abinci. Daga cikin su, an kwantar da 128,000 a asibiti, sannan 3,000 sun rasu.

A Birtaniya, an kiyasta cewa an samu rahoton cutukan cin abinci mai guda miliyan 2.4 duk shekara, sannan ana samun mutuwa akalla 180.

“Mutane za su rika cewa wancan naman, ko kaji ko kifin ne suka ja mana,” inji Mista Peled. “Amma idan ka lura da abin da ya jawo mutuwa a sanadiyar cutar a Amurka a shekara biyar zuwa goma da suka wuce, za ka ga nau’in latis din romaine ne.

“Sannan yadda ake kara samun karuwar kamfanoni na taimakawa wajen gurbacewar abinci.”

A kamfanin na NTT Data Business Solution da ke Jamus, sun samar da hanyar da za su koyar da kirkirarriyar fasahar da na’urar e-nose din amfani da coffee.

A wani gwaji guda daya, masu gwajin sun kwashe kwana uku suna zuba hodar coffe din a kusa da masunsunin AI din. Sai ita kuma kirkirarriyar fasahar ta AI ta sunsuna tare da gane coffe din a cikin sakamako uku-mai kyau, mara kyau (wanda aka gurbata da sinadarin vinegar) da kuma hodar da babu coffee din a ciki baki daya.

“Wari ba wai iskar gas ba ne kawai, hada-haden iskokin gas ne,” inji Adrian Kostrz, manajan kirkire-kirkire na kamfanin.”Sannan a lokuta da dama akwai bambanci a yadda na’urar ke sunsuno abubuwa.”

Na’urorin sunsuna na NTT an tsara su ne kamar hancin mutane. Suna amfani da coffe da sauran nau’ukan abinci wajen koyar da kirkirarriyar fasaharsu gane na’ukan abinci da kuma gane ko sabon abinci ne kuma bai lalace ba, wanda kamfanin ke amfani da, “ma’aunin warin abinci.”

Hancin roba na NTT

Asalin hoton, NTT Data

Bayanan hoto, Hancin roba na NTT

Tsarin shi ne na’urar e-nose din ba wai za a yi amfani da ita ba ne kawai wajen sunsuna gurbataccen abinci, har da gane ingancin abinci-mai kyau ko ya lalace. Wannan zai taimaka wa masu kantunan abinci su gane abincin da ya kamata su fara sayarwa, musamman wadanda a jikinsu babu lokacin lalacewarsa a rubuce.

“Sanin ma’aunin warin abinci zai taimaka wa masu abincin wajen tsara hada abincin da adana shi da ma tun a wajen girbi da gyara shi da kyau,” inji Mista Kostrz.

Sai dai wasu masa fasahar AI sun bayyana cewa duk da cewa na’urar e-nose na aiki da kyau, ba za su samu kasuwa sosai ba domin akwai alamar kamfanonin abinci da dama ba za su iya saya ba.

“Idan kana maganar kawo hanyar gano ingancin abinci ne, daga girbi da adana shi zuwa kai shi ga kwastomomi, dole ka kuma yi tunanin yadda hakan zai shafi kasuwancin masu abinci,” inji Vincent Peters, Babban mai tsare-tsare na kamfanin kirkirarriyar fasaha ta Inheritance AI da ke Amurka.

“Shin za a iya cigaba da kasuwancin idan ya zama dole a yi amfani da fasahar? Shin masu ruwa da tsaki a bangaren za su yi amfani da shi?shin za a samu riba?”

Shu kuma wani masanin fasahar AI din, Kjell Carlisson na kamfanin Domino Data Lab da ke San Francisco ya ce matsalar ita ce dole na’urar ta e-nose na bukatar tsari daban ne a duk wajen da za a yi aiki da shi. “Wannan aiki ne mai wahalar gaske musamman kasancewar kamfanonin abinci ba su saba amfani da kimiyya da fasaha ba,” inji shi.

Sai dai duk da haka, wadannan batutuwa ba ana fito da su ba ne domin karya gwiwar masu assasa na’urar.