'Muna iya kawo ƙarshen al'adar auren wuri a wannan ƙarni'

Asalin hoton, THE OBAMA FOUNDATION
- Marubuci, Megha Mohan da Yousef Eldin da kuma Emma Ailes
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, MATA 100 NA BBC
Uku daga cikin mata mafi ƙarfin faɗa-a-ji a duniya sun shaida wa BBC cewa suna son ganin an kawo ƙarshen auren wuri a cikin wannan ƙarni na al'umma.
Lauya kuma 'yar fafutuka Uwargidan tsohon shugaban Amurka, Michelle Obama, da lauya mai fafutukar kare 'yancin ɗan'adam Amal Clooney da mai ƙoƙarin taimakon jama'a Melinda French Gates sun sanar da kafa wani ƙawance tsakanin gidauniyoyinsu a Bara, domin yaƙi da matsalar.
A yadda al'amura suke tafiya yanzu haka, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa nan da shekara 300 mai zuwa, ba za a iya kawar da al'adar auren wuri ba.
Sai dai tsohuwar Uwargidan Shugaban ƙasar Misis Obama ta faɗa wa BBC cewa: "Batu ne da za a iya shawo kansa ko a gobe ma."
Matan uku sun zanta da Sashen Mata 100 na BBC a lokacin wata ziyara a ƙasar Malawi da Afirka ta Kudu.
"Ku yi min afuwa" cewar Lucy 'yar shekara 26, a lokacin da take ƙoƙarin danne hawayen da ke son zubo mata. "Ina jin shauƙi."
Lucy na cikin ɗakin karatu na makarantar sakandiren 'Yan mata ta Ludzi a lardin tsakiyar Malawi. Jami'an leƙen asirin Amurka suna tsaye daga waje, a ƙarƙashin jajayen bishiyoyi jazur da ke harabar makarantar.
Ta kammala jawabi kenan a kan muhimmancin barin 'yan mata a makaranta, da kuɓutar da su daga ƙaddarar auren tsofaffi masu nisan shekaru, kafin kwatsam shauƙi ya turnuƙe ta.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A zagaye da tebur, uku ne daga cikin mata mafi ƙarfin faɗa-a-ji wajen ayyukan jin ƙan ɗan'adam a duniya - Melinda French Gates da Amal Clooney da kuma Michelle Obama -sun kasa kasaƙe suna sauraron labarinta.
A cewar ƙungiyar Girls Not Brides, Malawi na ɗaya daga cikin ƙasashen da aka fi auren wuri a Gabashi da Kudancin Afirka, inda aka ba da rahoton cewa kashi 42% na 'yan mata 'yan shekara 18 tuni an yi musu aure. A Lardin Mchinji, inda makarantar 'Yan Mata ta Ludzi take, kashi 33% na 'yan mata ne aka ba da rahoton sun samu juna biyu kafin su kai shekara 18, kuma suka bar makaranta.
Lucy na iya zama ɗaya daga cikin waɗannan 'yan matan. Mahaifinta ya so ta bar makaranta tana 'yar shekara 14, amma ta ƙeƙasa ƙasa, daga bisani ne ta zama budurwa ta farko a ƙauyensu da ta shiga jami'a. Yanzu, da digirinta a fannin ilmi, ita ce shugabar lardinsu ce ta AGE Africa, wata ƙungiya da ke samar da tallafin karatu ga 'yan mata masu rauni Malawi, ƙasar da ba kyauta ba ne ilmin sakandire. Lucy ta kasance ɗaliba a ƙarƙashin wannan shiri, kuma a yanzu tana taimaka wa 'yan mata kamarta.

Asalin hoton, OBAMA FOUNDATION
Mahaifiyarta ta cika da murna bisa ga bajintarta, Lucy ta ce, ko da yake farin cikin mahaifinta bai kai nata ba. Ta ce har yanzu yana ƙoƙarin yadda zai fahimci 'yarsa mai 'yancin cin gashin kanta Ba da labarin duka wannan, yana matuƙar cika ta da murna..
Tsohuwar Uwargidan Shugaban Amurka da ke zaune a hannun hagun Lucy, ta yi magana. "Ko za ki kai wa mahaifinki saƙona? Idan kun gamu kika gan shi, ki faɗa masa Michelle da Barack Obama na matuƙar alfahari da ke, da kuma irin macen da kika zama."
Lucy ta ɗago kai, cike da murmushi. A hannun daman Lucy a zaune, lauyar kare 'yancin ɗan'adam ta duniya Misis Clooney ce. "Kuma ki faɗa masa kin samu lauya a yanzu," ta ƙara da cewa.
Bayan sanar da ƙawancen haɗin gwiwarsu na yaƙi da auren wuri a bara, Michelle Obama da Amal Clooney da kuma Melinda French Gates sun kai ziyara ƙasashen Malawi da Afirka ta Kudu, don yayata ayyukan da ƙungiyoyi a tsakanin al'umma da suka mayar da hankali kan wannan fanni ke yi, da kuma ganawa da 'yan mata da mata, waɗanda lamarin ya shafi rayuwarsu.
Ƙungiyar Misis Obama da ke mayar da hankali a fannin bunƙasa ilmi, Girls Opportunity Alliance, tuni da ma ta gano cewa 'yan mata a faɗin duniya suna barin makaranta, saboda sun ɗauki ciki da kuma auren wuri.
Misis Clooney na aiki don tabbatar da ganin 'yan mata a yankunan karkara sun san da 'yancinsu, yayin da aikace-aikacen Melinda French Gates masu yawa suka mayar da hankali wajen bunƙasa harkokin lafiya - ciki har da yin magani ga 'yan matan da suka gamu da larurori bayan sun haihu da ƙuruciyarsu.
Dukkansu suna cike da zaƙuwa game da kare 'yancin mata da 'yan mata, don haka ƙawance ne wanda da ma can kamar tun fil'azal ya dace.
"Ƙawancen ne na ainihi da abota tsakaninmu mu uku," lauya mai kare haƙƙin ɗan'adam a duniya Misis Clooney ta faɗa wa Shirin Mata 100 na BBC.
"Da farkon tattaunarmu da Gidauniyar Gates, na ce: 'Kuna aiki mai girman gaske kan batun tabbatar da adalci tsakanin jinsi, amma akasari ba kwa amfani da doka a matsayin wani kayan aiki. Kuna duba kan batun tattalin arziƙi, sannan kuna duba kan batun kula da lafiya. Mai yiwuwa muna iya ƙulla wani ƙawance?'"

Asalin hoton, OBAMA FOUNDATION
Mis Melinda Gates wadda ta sanya 'yan matan sakandiren Ludzi shewa da tafi lokacin da ta ce zuwanta Malawi na biyar kenan, ta ce aikinsu tare wata muhimmiyar shawara ce, da fannonin ƙwarewar da suka yi tarayya da juna, za su ƙara musu gogewa.
"Mata, in jin a halitta da ma sun fi aiki a tare ne," ta faɗa wa BBC. "Na zanta da ɗumbin mata, waɗanda sun girme ni kuma sun kasance manyan shugabanni a kamfanoninsu. Akwai nadamar da suke yi cewa ba su yi aiki cikin haɗin gwiwa da sauran mata ba. Ba su janyo mata sun ɗago su tare da su ba. Rukunin al'ummar da muke ciki - Michelle da ni shekaru ne kusan zango ɗaya - mun so mu janyo kowa da kowa, ya taso tare da mu."
'Yan mata miliyan 12
A cewar Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (Unicef), 'yan mata da matan da ke raye miliyan 650 ne waɗanda suka yi aure suna 'yan ƙasa da shekara 18. Kuma yanzu haka akwai 'yan mata fiye da milyan 12 duk shekara da ake yi sanya su a lalle da sunan aure a faɗin duniya.
Kudancin Asiya da Kudu da Hamadar Sahara ne suka fi ko'ina yawan auren wuri a duniya, sai dai wannan ba matsala ba ce da ta tsaya kawai a kudancin duniya ba, jihohin Amurka ba su iyakance shekarun aure ba, matuƙar dai akwai yardar iyaye.
Wasu ƙasashen, kamar Malawi suna da dokokin kawo sauyi da suka haramta aure ga yarinyar da ba ta kai shekara 18 ba, ko da yake waɗannan suna gamu da tarnaƙin al'adu da aka daɗe ana fama da shi.
A ranar Litinin, bayan ziyarar da 'yan fafutukar uku suka kai, Shugaba Lazarus Chakwera ya ba da sanarwar ba da ƙarin kuɗi ga wani shirin kawo ƙarshen wuri na ƙasar. Kafin yanzu, mutane ƙalilan aka taɓa gurfanarwa gaban shari'a saboda sun keta dokar.










