Ranar Mata Duniya: 'Yadda nake ɗaukar nauyin karatun 'yan mata masu talla kusan 100'

Bayanan bidiyo, Hajiya Munira Sulaiman Tanimu ta ce tun 2015 gidauniyarta take taimaka wa mutane.

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Yau ce ranar Mata ta Duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta keɓe domin tunawa da irin rawar da ya kamata iyaye mata suke takawa a tsakanin al’umma.

Taken bikin ranar ta wannan shekara shi ne 'Zabi wani kalubale guda domin tunkararsa’.

Albarkacin wannan maudu’in ranar ne BBC Hausa ta je garin Garaku da ke Keffin jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya, domin gane wa idanunta yara matan da gidauniyar Green Heart Impact Foundation ta yi ikrarin raba su da tallace-tallace a kan tituna, ta kuma dauki nauyin karatunsu na shekara shida.

Hajiya Munira Sulaiman Tanimu wadda ita ce shugabar gadauniyar ta ce yanzu haka tana daukar nauyin ilmin ‘ya’ya mata marasa galihu kimanin 100 a arewacin Najeriya.

Dangane kuma da inda take samun kudaden yin wannan hidima, Munira ta ce " ni 'yar kasuwa ce saboda haka ina ware kaso 10 na kudaden da nake samu a duk wata domin hidimar wadannan yara.

Muna daukar nauyin wadannan yara daga kudin makarantarsu zuwa abincinsu da katifunsu da zannuwansu da sabulun wankansu, da ma komai da komai har zuwa lokacin da za su kammala makarantar sakandare bayan shekara shida."

Burin Munira shi ne ganin yara mata sun daina tallace-tallace domin nan gaba su tsaya da kafafunsu.

Daukar Hoto: Abdulsalam Usman Abdulkadir

Rahoto: Usman Minjibir