Nau'in abincin da ya kamata a bai wa yara 'yan kasa da shekara biyar

Kwanaki 200 na farkon kowane jariri da aka haifa suna da muhimmanci matuƙa.

Bincike da dama sun nuna cewa duk abin da ya samu jariri a wannan lokaci zai iya yin tasiri tsawon rayuwarsa daga tashi zuwa girmansa.

Masana da dama wadanda suka hada da likitoci da masana abinci mai gina jiki a Brazil da BBC ta tattauna da su, sun bayyana muhimmancin bai wa yaro abinci mai gina jiki lokacin da yake tasawa.

Likitocin sun ce abinci da ya kamata a bai wa yaro bayan shekara biyar da haihuwarsa shi ne abincin da ke da sinadaran iron da zinc da iodine da vitamin A da sauransu.

Ga dai nau'ukan abinci masu gina jiki da ya kamata ku bai wa ƴaƴanku.

Nonon uwa

Dr Jose Nelio Cavinatto, wani likitan yara na asibitin Albert Einstein ya ce bai kamata a watanni shidan farko na haihuwar jariri a ba shi ruwa ko shayi ba, illa nonon uwa kadai.

Nonon uwa shi ne abinci da ke dauke da sinadarai da za su iya kare yaro daga cututtuka kamar amai da gudawa da matsalar numfashi da sauransu wanda hakan zai rage musu barazanar kamuwa da cutar asma ga manya da kuma ciwon sikari da ƙiba.

Likitan ya ce iyaye ne ya kamata su kula da jariransu ta hanyar ba su nono ta hanyar cin abinci mai gina jiki kamar ganyayyaki da cin ƙwai guda daya a rana, da kifi guda daya a mako saboda su samu isasshen abinci da zai gyara musu ƙwaƙwalwa.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da shawarar cewa a riƙa bai wa jariri ruwan nono zalla na tsawon shekara biyu ko fiye.

Kungiyar likitocin yara a kasar Brasil, ta ce ya kamata a fara bai wa yaro abinci bayan wata shida da haihuwarsa.

Sun ce ya kamata abincin ya ƙunshi ganyayyaki da nama da kuma mai.

Lafiyayyen abinci

Masana sun ce ya kamata uwa ta mayar da hankali kan irin abinci mai gina jiki da ƴaƴanta za su ci.

Sun ce ya kamata uwa ta raba abincin zuwa guda biyu sannan ta zaɓi wanda ya dace da za ta bai wa yaronta.

Wata jami’ar Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya a Brasil, Stephanie Amaral, ta ce abu ne da ya dace a bai wa yaro abinci mai kyau wanda ba sarrafa shi aka yi ba, inda ta ce hakan zai rage shan kayan zaƙi kamar sikari da wasu abubuwa a jikin yaro.

Ganyayyaki da ‘ya’yan itace

Likitoci sun bayyana cewa ya kamata kashi 50 na abincin da yara ke ci ya kasance ganyayyaki da kuma ‘ya’yan itace.

Ganyayyaki na dauke da sinadaran vitamin da mineral da sauransu.

‘Sinadarin iron na da matukar amfani ga kwakwalwa yaro a lokacin da yake girma,’ a cewar Monica Moretzsohn, wata likitar yara.

Ta ce idan ba a bai wa yaro abinci mai gina jiki ba hakan zai janyo wahala wajen koyon karatu ko kuma aiki.

Sinadarin Folic na da muhimmanci ga rayuwar yaro, inda rashin sa zai janyo wasu abubuwa ga jariri.

Likitar ta ƙara da cewa rashin vitamin A na iya janyo makanta.

Dangin hatsi

Ana bukatar abinci dangin hatsi ya kai kashi 25 a jikin yaro. Abinci kuma da suka hada da masara da shinkafa da alkama da biredi da doya da kuma rogo.

A cewar Dr Nelio Cavinatto, wadannan dangin abinci na da muhimmanci sosai ga lafiyar yara saboda suna dauke da vitamin da sauransu.

Abincin na samar da garkuwa da ta kamata wadda ke taimaka wa wajen girman yaro.

Rashin lafiyayyen abinci kan janyo ciwon sikari da na zuciya da kuma ƙiba.

Nama da ƙwai

Likitoci da ƙwararru kan abinci mai gina jiki sun bayar da shawar cewa abu ne mai muhimmanci a bai wa yaro nama da ƙwai a cikin abinci, inda suka ce ya kamata ya kai kashi takwas.

Irin nama da ake bukata shi ne naman kaza da na shanu da kuma kifi a cewar masana.

‘Nama na dauke da sinadarin iron, inda naman saniya ma yake daya daga cikin abubuwa da ke samar da vitamin B12’.

Rashin wannan dangin abinci kan janyo matsaloli da kuma rashin kuzari lokacin tashin yaro.

‘Ya'yan itace

‘Ya'yan itace na da muhimmanci matuƙa ga yaro, inda ya kamata a bai wa yaro lokacin karin kumallo ko kuma bayan cin abinci a kowane lokaci.

Kungiyar likitocin yara ta Brazil, ta bayar da shawarar cewa abu ne mai kyau a riƙa bai wa yara daga shekara daya zuwa biyar ‘ya’yan itace sau uku a kowace rana.

Ta kuma ba da shawarar cewa a riƙa ba su abin sha dangin ‘ya’yan itace. Amma masanan sun ce ka da a maye gurbin ruwan da suke sha da ‘ya’yan itacen.

Dangin madara

Masana abinci mai gina jiki sun ce da zarar jariri ya kai shekara daya, ya kamata a riƙa ba shi nonon uwa da abinci dangin madara sau uku a rana da kuma bai gaza kilogram 120 ba, har sai sun kai shekara biyar.

Madara da nono abinci ne mai kyau na sinadarin calcium.

Sinadarin calcium na da muhimmanci ga lafiyar jariri bayan na haife shi har zuwa tashinsa saboda lokacin ne ƙasusuwa ke fita a jikinsa.

Rashin sinadarin calcium kan janyo matsala a fitar hakorin jariri.

Dr Jose Nelio Cavinatto, da ya kasance likitan yara, ya bayar da shawarar cewa mutane su guji baiwa jariri nonon Saniya lokacin da yake dan shekara daya.