Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya samu shugabannin Hamas tun bayan fara yaƙi a Gaza?
- Marubuci, Raffi Berg & Lina Alshawabkeh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, London & BBC News Arabic, Amman
- Lokacin karatu: Minti 6
Tun bayan fara yaƙi a Zirin Gaza sakamakon harin da ƙungiyar Hamas ta kai cikin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023, an yi ta kai wa shugabanninta hari da ake zargin Isra'ila da yi. An kashe wasu, wasu kuma na nan da ransu.
Ga jerin abubuwan da suka faru da wasu daga cikin fitattun jagororoin ƙungiyar.
Ismail Haniyeh
Ana kallon Ismail Haniyeh a matsayin jagoran Hamas mafi girma.
An kashe shi ne, kamar yadda rahotonni suka nuna a wani hari ta sama, a kan wani gida da yake zama yayin ziyararsa a Tehran ranar 31 ga watan Yulin 2024. Iran ɗin da kuma ƙungiyar Hamas sun zargi Isra'ila da aikata kisan gillar.
Haniyeh - wanda shahararren mamban ƙungiyar ne tun a shekarun 1980 - Isra'ila ta taɓa tsare shi a gidan yari shekaru uku a 1989 lokacin da take daƙile boren Falasɗinawa.
Sai kuma ya koma gudun hijira a wani yanki tsakanin Isra'ila da Lebanon tare da wasu shugabannin Hamas a 1992.
Ya koma Gaza bayan shekara ɗaya. An naɗa shi shugaban sashen addini na Hamas a 1997, wanda ya taimaka masa wajen kafa ikonsa.
Shugaba Mahmoud Abbas ya naɗa Haniyeh firaministan Falasɗinu a 2006 bayan Hamas ta lashe akasarin kujeru a zaɓen majalisa. Amma an sauke shi sakamakon tashin hankali a Gaza, inda Hamas ta kori jam'iyyar Fatah ta Abbas daga Zirin Gazan.
Haniyeh ya ƙalubalanci sauke shi a matsayin "wanda ya saɓa wa doka" kuma Hamas ta ci gaba da mulkin Gaza.
An zaɓe shi a matsayin shugaban sashen siyasa na Hamas a 2017, abin da ya sa ya zama kamar wani mafi girman shugaba.
A 2018, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Haniyeh a matsayin ɗanta'adda.
Ya koma ƙasar Qatar da zama tsawon shekaru da suka wuce.
Yahya Sinwar
Yahya Sinwar ne shugaban Hamas a cikin Zirin Gaza. Isra'ila ta yi amannar cewa shi ne ya jagoranci kai harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
An haifi Sinwar a sansanin 'yan gudun hijira da ke Khan Younis a cikin Gaza a 1962.
Shekara ɗaya bayan kafa Hamas a 1987, ya kafa sashen tsaron ƙungiyar, wanda ya dinga kai farmaki ga masu haɗa kai da Isra'ila a cikin Falasɗinawa.
Isra'ila ta kama Sinwar sau uku a baya. An yanke masa ɗaurin rai da rai har sau huɗu a 1988 saboda kitsa garkuwa da kuma kashe Isra'ilawa biyu da kuma kashe Falasɗinawa huɗu.
Sai dai kuma a 2011, yana cikin Falasɗinawa 1,027 da Isra'ila ta saki a matsayin musayar sojanta da Hamas take tsare da shi a Gaza tsawon shekara biyar.
Ya koma Hamas a matsayin babban jagora kuma aka naɗa shi shugaban sashen siyasa a Gaza a 2017.
A 2015, Amurka ta saka Sinwar cikin baƙin littafinta na "yan'ta'addan duniya".
Ba a taɓa ganin Sinwar ba tun bayan fara yaƙin na watan Oktoba. An yi amannar har yanzu yana cikin Gaza.
Mohammed Deif
Mohammed Deif ya jagoranci rundunar Izz al-Din al-Qassam Brigades, ɓangaren soji na Hamas.
Shi ne mutumin da Isra'ila ta fi nema, kuma an kashe shi a wani hari da Isra'ila ta kai a watan da ya gabata, in ji Isra'ilar. Amma Hamas ba ta tabbatar da hakan ba.
Deif wanda ba a sani ba sosai, ya zama ƙwararre a wajen Falasɗinawa amma kuma mutum mai rayuka da yawa a wajen Isra'ila.
Isra'ial ta kulle shi a gidan yari a 1989 yayin boren Falasɗianwa na farko kuma aka sake shi shekara ɗaya da rabi bayan haka. Jim kaɗan bayan haka, ya kafa bataliyar al-Qassam Brigades da zimmar kama sojojin Isra'ila.
Ya kuma taimaka wajen gina hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da suka bai wa Hamas damar ɓulla cikin Isra'ila daga Gaza.
Isra'ila na zargin Deif da kitsa harin bamabamai kan bas-bas da suka kashe Isra'ilawa a 1996, da kuma kamawa da kashe sojojinta uku a tsakiyar shekarun 1990.
Hukumar Falasɗinawa ta kama shi a 2000 amma sai ya gudu wata bakwai bayan haka.
Ya zama mutumin da Isra'ila ta saka a gaba amma kuma ba a iya sanin inda yake ba tun daga lokacin.
Mafi girman yunƙurin kashe shi da aka yi shi ne a 2002: Ya tsira amma kuma ya rasa idonsa ɗaya. Isra'ila ta ce ya kuma rasa ƙafa ɗaya da hannu ɗaya, kuma wai ba ya iya magana da kyau.
Isra'ila ta sake yunƙurin kashe shi yayin wani hari a Gaza a 2014, amma ta kashe matarsa da 'ya'yansa biyu.
Isra'ila ta ce ta kashe shi a wani hari da ta kai kan wani gida a Khan Younis ranar 13 ga watan Yuli.
Marwan Issa
Hamas ba ta tabbatar da iƙirarin Fadar White House ta Amurka ba cewa an kashe Marwan Issa, mataimakin kwamandan bataliyar Izz al-Din al-Qassam Brigades, yayin wani hari a watan Maris na 2024.
Mai bai wa gwamnatin Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sulivan ya ce dakarun sojin Isra'ila ne suka kashe shi bayan rahotonnin kafofin yaɗa labarai a Isra'ila sun ce ya mutu ne a hari kan hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat.
Kafin ba da rahoton kisan nasa, shi ne mutumin da Isra'ila ta fi nema, kuma an jikkata shi lokacin da Isra'ilar ta yi yunƙurin kashe shi a 2006.
Sojin Isra'ila sun tsare shi a yayin boren Falasɗinawa na farko tsawon shekara biyar saboda alaƙarsa da Hamas.
Jiragen yaƙin Isra'ila sun taɓa ragargaza gidansa har sau biyu yayin samamen da suka kai a 2014 da 2021, inda aka kashe ɗan'uwansa.
Ba a san siffarsa ba har sai a 2011, lokacin da ya shiga wani hoton rukuni da aka ɗauka na musayar fursunoni.
Khaled Meshaal
Khaled Meshaal da aka haifa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka kafa ƙungiyar ta Hamas.
Bisa umarni kai-tsaye daga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, hukumar leƙen asiri ta Isra'ila Mossad ta yi yunƙurin kashe Meshaal a 1997 lokacin da yake zaune a Jordan.
Dakarun Mossad sun shiga Jordan ɗauke da fasfon ƙarya na Canada kuma aka yi wa Meshaal allura mai ɗauke da guba yana tsaka da tafiya a gefen titi.
Hukumomin Jordan sun gano yunƙurin kisan kuma suka kama dakarun na Mossad.
Tsohon Sarkin Jordan Hussein ya nemi firaministan Isra'ila ya ba da maganin allurar da aka yi wa Meshaal.
Bayan matsin lamba daga Shugaban Amurka Bill Clinton, Netanyahu ya bayar da maganin bayan ya ƙi tun da farko.
Meshaal da ke zaune a Qatar, ya je Gaza a karon farko a 2012. Shugabanni da mazauna Gaza sun fita domin tarɓarsa.
Hamas ta zaɓi Haniyeh domin maye gurbin Meshaal a matsayin shugaban sashen siyasarta a 2017, sai kuma Meshaal ya zama shugaban sashen amma a ƙasashen waje.
Mahmoud Zahar
An haifi Mahmoud Zahar a Gaza a 1945, mahaifiyarsa 'yar Masar ce, mahaifinsa kuma Bafalasɗine.
Yana cikin shugabannin Hamas na siyasa.
Ya yi makaranta a Gaza kuma ya yi karatun jami'a a Alƙahira na Masar. Ya zama likita a Gaza kafin daga baya Isra'ila ta kore shi saboda aniyarsa ta zama ɗansiyasa.
An tsare Mahmoud Zahar a gidan yari a 1988. Yana cikin mutanen da Isra'ila ta fitar daga yankin a 1992, inda ya shafe shekara ɗaya a yankin da ke tsakanin Lebanon da Isra'ilar.
Bayan Hamas ta lashe zaɓen Falasɗinawa na 2006, Zahar ya zama ma'aikacin ma'aikatar harkokin waje a gwamnatin su Ismail Haniyeh kafin a sauke shi daga muƙamin.
Isra'ila ta yi yunƙurin kashe Zahar a 2003, lokacin da wani jirgi ya jefa bam a kan gidansa da ke birnin Gaza. Harin ya ji masa ƙananan raunuka amma ya kashe babban ɗansa Khaled.
Ɗansa na biyu Hossam, wanda mamba ne a bataliyar al-Qassam Brigades, ya rasu a harin Isra'ila na 2008 a Gaza.