Ina ne yankin Tuddan Golan kuma me ya sa Hezbollah da Isra'ila ke taƙaddama a kansa?

Lokacin karatu: Minti 5

Wani mummunan hari kan filin wasan ƙwallon ƙafa da ke yankin Tuddan Gola da Isra'ila ta mamaye ya ta'azzara barazanar aukuwar sabon yaƙi tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon.

Isra'ila ta ce Hezbollah ce ta kai harin, zargin da ƙungiyar ta musanta.

Me ya faru a harin na Tuddan Golan (Golan Heights)?

A yammcin wata Asabar 27 ga watan Yuli, wani makami ya faɗa garin Majdal Shams, inda ya kashe yara 12 'yan ƙabilar Druze marasa rinjaye.

Shi ne hari mafi muni a ciki da kewayen Isra'ila tun bayan fara musayar wuta tsakaninta da Hezbollah a watan Oktoba.

Saboda yadda ya shafi ƙananan yara, harin ya ja fusata mutane a Isra'ila da kuma duniya baki ɗaya.

Isra'ila ta ce Hezbollah ce ta kai harin da wani makamin roka da Iran ta samar, wanda aka harba babu nisa daga Lebanon. Amurka ma ta zargi Hezbollah.

Amma ƙungiyar ta musanta duk wani hannu a cikinsa.

Wace ce Hezbollah?

Ita dai kungiyar Hezbollah ta musulmai mabiya mazhabar Shi'a ce, tana da karfi sosai a fannin siyasa da ikon yawancin manyan sojin Lebanon.

A shekarar 1980 manyan masu karfin fada a ji na 'yan Shi'a a Iran suka kafa kungiyar, da nufin kalubalantar Isra'ila. A wancan lokacin sojojin Isra'ila sun mamaye kudancin Lebanon a lokacin yakin basasar kasar.

An dama da Hezbollah a lokacin zaben 1992, a nan ne ta zama babbar mai fada-a-ji a bangaren siyasa.

Dakarun kungiyar sun kai munanan hare-hare kan dakaruin Isra'ila da na Amurka. A lokacin da Isra'ila ta janye daga Lebanon, kungiyar Hezbollah ta yi amfani da wannan damar tare da cewa ita ce ta fatattake su.

Tun daga lokacin, Hezbollah ta tara dubban mayaka da kafa wani kataren wurin adana makamai masu linzami a kudancin Lebanon.

Kungiyar ta ci gaba da kalubalantar Isra'ila musamman a iyakar kasasshen biyu.

Kasashen Yamma da Isra'ila da kungiyar kasashen larabawa da wasu daga ciki sun ayyana Hezbolla a matasayin ta 'yan ta'adda.

A shekarar 2006, cikakken yaki ya barke tsakain Isra'ila da Hezbollah, lokacin da Hezbollah ta kai mummunan samama a iyakar Isra'ila.

Sojojin Isra'ila sun mamaye kudancin Lebanon, lamarin da ya sa fargaba ga Hezbollah. Amma duk da hakan, sun yi nasara sakamakon kara yawan mayakan da suke da su da kuma samun manyan makamai na zamani masu inganci.

Ana ganin ƙungiyar na da makaman roka da masu linzami 200,000, da jiragen kai hari marasa matuƙa. Daban take da dakarun sojin ƙasar Lebanon, hasali ma ta fi su ƙarfi.

Haka nan, Hezbollah na da tasiri a gwamnatin Lebanon ɗin ta yanzu.

Ina ne Tuddan Golan kuma me ya sa Isra'ila ke iko da shi?

Tuddan Golan ko kuma Golan Heights a Turance, wani yanki ne mai cike da duwatsu a kudu maso yammacin ƙasar Syria wanda ya kai har arewa maso gabashin Isra'ila.

Yayin Yaƙin Gabas ta Tsakiya na shekarar 1967, Isra'ila ta ƙwace yankin da ya kai girman murabba'in kilomita 1,200 (460 square miles) na Tuddan Golan, inda daga nan ne Syria ta kai mata hari.

Isra'ila ta yankin a 1981, matakin da akasarin ƙasashen duniya ba su amince da shi ba. Sai a 2019 gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump ta amince da ikon Isra'ila kan yankin.

Syria ta ce yankin mallakinta ne kuma ta ci alwashin ƙwato shi, yayin da Isra'ila ke cewa yankin na da muhimmanci game da tsaron ƙasarta kuma zai cigaba da kasancewa ƙarƙashin ikonta har abada.

Isra'ilawa masu mamaye kusan 20,000 ne ke zaune a Tuddan Golan ɗin, wanda kuma ke ɗauke da filayen jirgin sama na sojojin ƙasar da kuma tashoshin tsaro. Sai dai dokokin ƙasashen duniya ba su amince da gidajen ba, duk da cewa Isra'ila na ƙalubalantar hakan.

Su wane ne al'ummar Druze?

Al'ummar Druze Larabawa ne da akasarinsu ke zaune a ƙasashen Lebanon, da Isra'ila, da Syriya, da Jordan. Wasu daga cikinsu na zaune a yankin ɗaruruwan shekaru.

Mazauna yankin sun koma ƙarƙashin Isra'ila a watan Yulin 1967 daga na Syria, lokacin da Isra'ilar ta mamaye akasarinsa. Garin Majdal Shams ne mafi girma cikin garuruwa huɗu da Druze suka fi rinjaye a cikinsu.

Isra'ila ta yi wa duka mazauna yankin tayin shaidar zama 'yanƙasa, sai dai yawansu sun zaɓi cigaba da zama 'yan Syria.

Kusan kashi 20 cikin mutanen yankin kusan 21,000 sun karɓa ko kuma sun gaji shaidar zama 'yan Isra'ila. Waɗanda ma suke da shaidar zama 'yan Syria na da takardun zama a Isra'ila, inda suke da haƙƙoƙi iri ɗaya ban da 'yancin kaɗa ƙuri'a.

Baya ga Tuddan Golan, akwai kuma 'yan Druze 110,000 da cikakkun 'yan Isra'ila ne. Su ne ƙabila mafi girma da ba Yahudawa ba waɗanda kuma ke shiga aikin soja na hidimar ƙasa.

Akwai 'yan ƙabilar Druze kusan miliyan ɗaya a duniya, kodayake akwai saɓani kan ƙiyasin. Addininsu wani nau'i ne na Shia, wanda ke da nasa sharuɗɗan da kuma salon ibadar.

Me ya sa ake ganin Hezbollah ce ta kai hari kan Golan?

Hezbollah ta kai wa sansanonin sojin Isra'ila hari kwana ɗaya bayan harin da Hamas ta kai cikin Isra'ilar ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Ta ce tana taya Falasɗinawa yaƙi ne.

Tun daga lokacin, ɓangarorin biyu suka fara musayar wuta akai-akai, wanda ya tilasta wa dubban mazauna Lebanon da Isra'ila guduwa daga gidajensu.

Jami'an tsaron Isra'ila sun ce makamin da ya kashe yaran ɗaya ne cikin waɗanda aka harba kan wurare da dama a yankin na Golan. Harin ya biyo bayan wanda Isra'ila ta kai ne da ya kashe mayaƙan Hezbollah huɗu a Lebanon.

Akasarin hare-haren Hezbollah sun faɗa arewacin Isra'ila ne, da kuma 'yan kaɗan a kan Golan. Amma kuma ta sha kai wa sansanonin sojan Isra'ila hari a wani yanki mai suna Shebaa ko kuma Tsaunin Dov na Golan ɗin da ke maƙwabtaka da Majdal Shams.

Mece ce alaƙar wannan da Hamas da kuma yaƙin da ake yi a Zirin Gaza?

Hezbollah na taimaka wa Hamas, wadda ke yaƙi da Isra'ila tun daga 7 ga watan Oktoba, lokacin da mayaƙanta suka tsallaka cikin ƙasar kuma suka kashe aƙalla mutum 1,200 da kuma sace mutum 251 zuwa cikin Gaza.

Hezbollah ta fara kai iyakantattun hare-hare kan Isra'ila ita ma daga ɓangaren arewaci kwana ɗaya bayan hakan, kuma tun daga lokacin ɓangarorin ke musayar wuta.

Duka Hamas da Hezbollah na samun goyon bayan Iran (duk da cewa Hamas ƙungiya ce ta 'yan Sunni, Hezbollah kuma ta 'yan Shia). Duka suna cikin rukunin abin da Iran ke kira da "dakarun kare-kai", wani ƙawancen ƙungiyoyi masu manufa ɗaya da Iran ɗin ke mara wa baya kuma suke adawa da Isra'ila da Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Hezbollah ba ta shiga yaƙin Gaza kai-tsaye ba kuma ta ce za ta dakatar da buɗe wuta idan aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila.