Mutharika - Yadda shugaban da kotu ta kora ya sake komawa kan mulki a Malawi

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
- Marubuci, Wedaeli Chibelushi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Shekara biyar bayan kotu ta sauke shi daga kan mulki, Peter Mutharika zai koma kan kujerar bayan lashe zaɓen shugaban ƙasar Malawi.
Mutharika, wanda ya shugabanci Malawi daga 2014 zuwa 2020 ya samu nasara ne a zaɓen da aka gudanar cikin makon da ya gabata, inda ya kayar da daɗaɗɗen abokin hamayyarsa, shugaba Lazarus Chakwera mai ci.
Mutherika ya shaida wa masu kaɗa ƙuri'a lokacin da yake yakin neman zaɓe cewa rayuwa ta fi daɗi a zamaninsa - Malawi ta fuskanci matsalolin tattalin arziƙi mafi muni tun bayan da Chakwera ya hau mulki.
Bayan shekara biyar da kotu ta sauke shi daga mulki a wani hukuncinta, Peter Mutharika zai sake komawa karagar mulki a matsayin shugaban ƙasar Malawi.
Mutharika, wanda ya yi mulki daga 2014 zuwa 2020, ya samu nasara ne kan babban abokin hamayyarsa Lazarus Chakwera a zaɓen da aka gudanar makon da ya gabata.
A lokacin yaƙin neman zaɓe, Mutharika ya faɗa wa al'umma cewa rayuwa ta fi daɗi a ƙarƙashin mulkinsa - Malawi ta fuskanci ɗaya daga cikin lokuta mafiya tsauri a fannin tattalin arziki a tun bayan hawa mulki Mista Chakwera.
Sai dai shi ma mulkin Mutharika mai shekara 85 na da nasa naƙasun, daga zarge-zargen cin hanci da kuma dalilin da ya kawo ƙarshen wa'adin mulkinsa na farko.
Wannan ne karo na huɗu da ya yi takarar shugaban ƙasa, amma tun da farko bai yi niyyar shiga siyasa ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wanda aka haifa a 1940 a yankin Thyolo, ya taso ne a hannun malaman makaranta biyu kuma ya koyi son koyarwa.
"Na taso ne a cikin dangin da na tarar da iyayena malamai ne, ni ma kuma na shafe rayuwata a ɓangaren koyarwa a jami'o'i bakwai da ke nahiyoyi uku," a cewar Mutharika yayin wani jawabi a Jami'ar Oxford a 2017.
Ya halarci sakandaren Dedza Secondary School da ke tsakiyar Malawi, wadda aka sani da rainon 'yansiyasa, kuma ya karanci fannin lauya a shekarun 1960 a jami'ar Yale da ke Amurka.
Daga baya Mutharika ya zama farfesa a fannin dokoki tsakanin ƙasashen duniya. Ya shafe shekaru da yawa wajen koyarwa a jami'o'in Amurka da Tanzania da Uganda da Habasha.
Mutharika ya tsunduma siyasa a 2004, lokacin da ɗan'uwansa Bingu ya zama shugaban ƙasa.
Ya koma gida domin kama aiki a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara a 2009, sannan aka zaɓe shi ɗanmajalisa a jam'iyya mai mulki ta Democratic Progressive Party (DPP).
Ya yi ministan shari'a a gwamnatin yayansa, da ministan ilimi, da kuma ministan harkokin waje.

Asalin hoton, WireImage via Getty Images
Mutharika ya samu mulki cikin kwanciyar hanklai, amma rikici ya taso a 2010 yayin da ake hasashen Bingu na shirin naɗa shi ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyar DPP a zaɓen 2014.
"Duk mako akan tara shugabanni su dinga yabon Peter Mitharika a talabijin...Mutane da yawa ba su jin daɗi idan aka duba wannan son kai ƙiriƙiri," kamar yadda ɗanjaridar Malawi Francis Chuma ya wallafa a jaridar The Guardian.
Sai kuma a 2012 da aka samu hatsaniya wajen miƙa mulki a watan Afrilun 2012.
Shugaban ƙasar ya kamu da bugun zuciya, inda ya mutu yana shekara 78. Kundin mulkin ƙasar idan shugaban ƙasa ya mutu mataimakinsa ne zai hau mulki, amma kuma Bingu ya ɓata da mataimakiyarsa Joyce Banda, tun kafin lokacin saboda shirin ɗora Mutharika a mulki.
Jam'iyyar DPP ta kori Banda daga jam'iyyar, wadda ta kafa sabuwar jam'iyya mai suna People's Party (PP), amma ta ƙi sauka daga muƙamin mataimakiyar shugaban ƙasa.
Magoya bayan jam'iyyar sun yi yunƙurin kauce wa tsarin mulki wajen ɗora Mutharika a kan mulkin, amma Banda ta yi nasarar zama mace ta farko shugabar Malawi.
An tuhumi Mutharika da laifin cin amanar ƙasa bayan zargin sa da shirin ɓoye gawar ɗan'uwansa domin hana Banda kama aiki a matsayin shugabar ƙasa.
Ya musanta zarge-zargen, kuma an janye su bayan an zaɓe shi shugaban ƙasa a 2014, inda ya doke Banda da Chakwera bayan lashe kashi 36 cikin 100 na ƙuri'u.
A 2018, hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasar ta zargi Mutharika da karɓar rashawar kuɗin ƙasar biliyan 2.8 da aka ware domin samar wa 'yansandan ƙasar abinci.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Bayan haka ya nuna cewa ba zai sake neman mulkin ƙasar ba, amma ya mamayi mutane lokacin da ya shiga takarar wannan karon, yana mai cewa magoya baya ne ke son ya ceto ƙasar.
Tun bayan da Mutharika ya bar ofis, hauhawar farashi ta ƙaru zuwa sama da kashi 30 cikin 100.
Yayin yaƙin neman zaɓe a shekarar nan, ba a fiya ganin Mutharika a bainar jama'a ba.
Kamfanin labarai na Faransa AFP ya siffanta shi da mutum mai "shuru-shuru", yayin da jaridar Mail & Guardian ta Afirka ta Kudu ta ce mutum ne da "ya fi son zama da littafi sama da shiga harkokin siyasa".
Mutharika na da 'ya'ya uku da matarsa ta farko Christophine ta haifa, wadda ta rasu a 1990. A watan Yunin 2014, ya auri tsohuwar 'yarmajalisa Gertrude Maseko.











