Yadda ƙananan na'urorin tace ruwa ke kawo wa al'ummomin Afirka sauƙi

Na'urorin tace ruwa na kamfanin UpEnergy na taimaka wa ƙananan yara a Uganda da sauran ƙasashe don samun tsaftataccen ruwan sha

Asalin hoton, UpEnergy

Bayanan hoto, Na'urorin tace ruwa na kamfanin UpEnergy na taimaka wa ƙananan yara a Uganda da sauran ƙasashe don samun tsaftataccen ruwan sha
    • Marubuci, Soo Min Kim
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Nicholas Mukiibi kan shiga damuwa kan matsalar ruwan sha a kowace rana a garin Kawempe na ƙasar Uganda.

Samun tsaftataccen ruwan sha matsala ce ta yau da kullum a wasu ƙasashen Afirka, inda a wasu lokuta al'umomin yankin ke amfani da zaɓi biyu don samar wa kansu tsaftataccen ruwa.

Hanyoyin kuwa su ne sayen ruwan roba ko tafasa ruwan da aka ɗebo daga rijiya, waɗanda dukkansu hanyoyi ne masu matuƙar tsada.

“Buhun gawayi ya kai 80,000 zuwa 90,000 na kuɗin Uganda, kwatantkwacin dala 21 zuwa 24'', in ji Nicholas, yana mai cewa hanyoyi ne da ba kowa ne zai iya jurewa ba.

A 2021, abubuwa sun sauya wa Nicholas, a lokacin da ya ga na'urar tsaftace ruwa da wani abokinsa ke amfani da ita.

An samu na'urar ne daga wani kamfanin makamashi mai suna UpEnergy.

“Na ɗauki tsawon kwanaki, ina shan ruwa daga na'urar tsaftace ruwa ta abokinai, kuma ban yi jinya ba, daga nan na yanke shawarar sayen na'urar don amfanin gidanmu'', in Nicholas.

An asayar da na'urar tsaftace ruwan sha ta UpEnergy a kan shillings 50,000, (dala 13).

A yanzu Nicholas ya shafe fiye da shekara uku yana amfani da na'urar. ''Na'urar tana da sauƙi, kuma ba ni da fargabar kamuwa da cututtuka, daɗin daɗawa kuma ba ta canja ɗanɗanon ruwa,'' in ji shi.

Nicholas ya ja ra'ayin abokansa har biyar don sayen na'urar, saboda yadda ya ji dadin amfani da ita. "Da kuɗii ƙalilan za ka mallake ta, amma za ta yi maka amfani mai yawan gaske,'' kamar yadda ya ce.

Injiniyoyin kamfanin UpEnergy na kafa na'urorin tsaftace ruwan sha a makarantun Afirka

Asalin hoton, UpEnergy

Bayanan hoto, Injiniyoyin kamfanin UpEnergy na kafa na'urorin tsaftace ruwan sha a makarantun Afirka
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amfanin na'urorin tsaftace ruwan sha na UpEnergy ba su tsaya ga gidaje kawai ba.

Ana amfani da su a makarantun ƙasashen Malawi da Zambia da kuma Tanzania - inda cututtukan da ake ɗauka ta hanyar ruwan sha suka yi katutu tsakanin ɗalibai - kamfanin UpEnergy ya samar da na'urorin tsaftace ruwan sha.

Waɗannan na'urori kan tsaftace ruwan sha, domin amfanin ɗalibai a makarantun waɗanann ƙasashe.

Kamfanin da samar musu na'urorin kyauta a makarantun, kuma sukan zo da tabbbacn inganci na shekara biyar.

“Nakan yi jinya sakamakon shan gurɓataccen ruwan da ke ɗiba daga tuƙa-hutar da ke kusa da makarantarmu,'' in ji Elestina Tembo, ɗalibi a makarantar furamare ta Mchinji Mission a Malawi.

“Ban taɓa samun gudawa sakamakon tuƙa-huta ba, kuma ban taɓa fashi sakamakon haka ba''.

“An samu sauyi dangane da yawan zuwan ɗalibai makaranta,'' in ji Zacharia Phiri, shugaban makarantar. “Duka ɗalibai da malamai kowa na cikin ƙoshin lafiya, kuma suna ci gaba da zuwa makaranta.''

Na'urar tace ruwan sha a makarantar furamare ta Mchinji Mission a Malawi ta kawo sauyi mai inganci kan yawan zuwan makaranta

Asalin hoton, UpEnergy

Bayanan hoto, Na'urar tace ruwan sha a makarantar furamare ta Mchinji Mission a Malawi ta kawo sauyi mai inganci kan yawan zuwan makaranta

“Ba za ka kafa na'ura kawai ka barta ba tare da kula ba,” in ji Lafelle Shiomitsu, daraktan kamfanin UpEnergy a Uganda. “Muna aiki hannu da hannu da al'ummar garuruwan da muke saka na'urorin don tabbatar da ana kula da su, domin su ci gaba da aiki yadda ake buƙata.'' Wannan ko ya haɗa da yawan ziyartar su, da yin gyare-gyare da wayar da kan mutane kan amfani da su.

Kamfanin UpEnergy, ya ce na'urorin nasa kan samar da tsaftataccen ruwan sha ga mutane kusan 90,000, da kuma ruwan amfanin gidaje ga kudan mutum 100,000.

Ta hanyar haɗa kai da mutanen gari kamfanin na da burin taimaka wa al'umomi marasa galihu don rage musu hatsarin da ke tattare da amfani da gurɓataccen ruwa.

“Na'urorin UpEnergy kan taimaka wa ɗalibai 1,500 da kuma ilahirin mutanen ƙauyenmu,” in ji Zacharia. “Duka mun amfana daga ruwan da na'urorin tace ruwan, kuma muna fatan samun ƙaton tanki domin adana ruwan da suke tacewa domin amfanin al'umarmu.''

Gidauniyar Bill & Melinda Gates ne suka ɗauki nauyin wannan maƙala.