Tsoro, fargaba da wahala: 'Bala'in da muka gani a yaƙin Sudan'

Alawia Babiker Ahmed a garin Tawila
    • Marubuci, Anne Soy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Deputy Africa editor
  • Lokacin karatu: Minti 5

Alawia Babiker Ahmed mai shekara 19 ta yi ɓari a lokacin da take gudu da ƙafa domin tsira daga ƙazamin yaƙin basasa da ya ɗaiɗaita yankin Darfur na yammacin Sudan.

''Ina ta zubar da jini a kan hanya,'' ta gaya wa BBC, kafin ta ƙara da cewa, ta ga ma mutanen da suka ma fi ta shiga tsaka-mai-wuya, waɗanda yanayinsu ya fi nata a wannan lokaci da take tafiyar kwana uku ta nisan kilomita 70, cikin fargaba da tashin hankali daga birnin el-Fasher da aka yi wa ƙawanya zuwa ɗan ƙaramin garin Tawila.

Alawia ta bayyana yadda ita da ƴan'uwanta suka ga wani ɗan ƙaramin yaro yana kuka kusa da mahaifiyarsa wadda ta rasu tana yashe a gefen titi, a daidai lokacin da su kuma suke ta kauce wa hare-hare ta sama da 'yanbindiga.

Alawia ta ce ta ɗauki yaron, ita kuwa gawar uwar suka rufe ta, suka ci gaba da tafiya.

Sudan ta faɗa bala'in yaƙin basasa tun bayan da faɗa ya ɓarke tsakanin rundunar sojin ƙasar da dakarun RSF, a watan Afirilu na 2023.

Lamarin da ya haddasa ɗaya daga cikin bala'i da mutane suka taɓa faɗawa, inda sama da mutum miliyan 12 suka tsere daga gidajensu.

Darfur ta kasance yankin da nan da nan rikici kan tashi, inda RSF ke iko da yawancin yankin, in banda birnin el-Fasher wanda ya ci gaba da kasancewa a hannun rundunar sojin ƙasar da ƙawayenta.

Birnin el-Fasher ya sha ruwan bama-bamai a yayin da RSF ke ƙoƙarin kama shi.

A watan Afirilu RSF ɗin ta sanar da shirin kafa gwamnati domin zama kishiya ga gwamnatin soji, abin da ya haddasa fargaba cewa hakan zai kai ga rarraba ƙasar.

Alawia ta ce yayin da faɗan ya tsananta ake ta ruwan bama-bamai a watan da ya gabata, dole ita da mutanen gidansu suka tsere a ƙafa zuwa Tawila da ke yamma da el-Fasher.

Yayanta Marwan Mohamed Adam, mai shekara 21, ya gaya wa BBC cewa mayaƙan da ke da alaƙa da RSF sun ci zarafinsa a hanya inda suka lallasa shi da duka, har suka yi masa fashin 'yan abubuwan da yake ɗauke da su.

Marwan ya ce ya tsira daga hannun gungun ne saboda ya yi musu ƙarya daga inda ya fito.

Ya ce maharan sun ɗebe matasan da suka gaya musu cewa daga el-Fasher suke suka je suka harbe su.

''Saboda haka a lokacin da suke yi min tambayoyi na ce musu daga Shaqra nake - wanda zango ne a kan hanyar zuwa Tawila,'' in ji shi.

Hoton Marwan Mohamed Adam
Bayanan hoto, Marwan Mohamed Adam na son ya je ƙasar waje ya zauna
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Za ka ji tsoro da fargaba, kana cikin tashin hankali, ka ji kamar ma ka riga ka mutu," in ji Marwan mai shekara 21, a hirarsa da BBC, inda ya ƙara da cewa ya ga gawawwaki uku a kan hanya.

Wata matar, Khadija Ismail Ali, ta gaya wa BBC cewa "ga gawawwaki nan yashe a titi."

Ta ce an kashe mutum 11 'yan gidansu a lokacin da ake yi wa el-Fasher ruwan makamai ta sama, kuma ƙananan yara uku sun mutum a lokacin tattakin da suka yi na kwana huɗu daga birnin zuwa Tawila.

"Yaran sun rasu ne sakamakon ƙishirwa a hanya," in ji Khadija.

'Yanbindiga masu alaƙa da dakarun RSF sun kai hari kan ƙauyen iyalinta, el-Tarkuniya, a watan Satumba da ya wuce, inda kuma suka sace musu amfanin gona.

A lokacin suka tsere zuwa sansanin Zamzam inda ake fama da yunwa, daga nan kuma suka ƙara gaba zuwa el-Fasher yanzu kuma zuwa Tawila.

Ƙungiyar bayar da agajin lafiya - Alima ta ce ƴanbindiga sun ƙwace filaye da gonakin yawancin iyalai a lokacin da suka kai musu hari.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa waɗanda suke zuwa Tawila, yawanci yara tuni sun kamu dacutar tsananin yunwa.

Alawia ta ce 'yar uwarta ta jefar da ɗan abincin da suka yi guziri a lokacin da suke neman tsira daga hare-haren sama da suka gamu da su bayan sun wuce Shaqra.

"Ɗan wani guntun wake ne da ya rage da ɗan gishiri muka riƙe a hannunmu domin ciyar da yara," ta ce.

Mata da yara da matasa a kan kura na barin garin Zamzam

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yankin Darfur ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda yaƙin basasar Sudan ya fi shafa

Haka suke ta tattaki ba tare da ruwa ko abinci ba, har suka haɗu da wata mata da ta ce musu za su iya samun ruwa a wani ƙauye da ke kusa.

Tawagar tasu ta tashi cikin dare domin ci gaba da tafiya zuwa wannan ƙauye, to amma ba su san cewa ashe suna yanki ne da ke ƙarƙashin ikon mayaƙan RSF ba.

"Mun gaishe su, amma kuma ba su amsa mana ba. Sun umarce mu, mu zauna a ƙasa, suka bincike kayanmu," in ji Alawia.

Mayaƙan sun karɓe kuɗin da muke riƙe da su fan 20,000 (na Sudan) (daidai da dala 33), gaba ɗaya kuɗin da iyalan ke da shi, tare da tufafi da takalman da suke ɗauke da su.

"Takalmana ba su da kyau amma duk da haka suka ƙwace su," in ji Alawia.

Ta ƙara da cewa mayaƙan RSF sun ƙi su ba su ruwa, saboda haka suka ci gaba da tafiya har sai da suka kai ƙauyen el-Koweim.

A can suka hangi wata rijiya da mayaƙan RSF ke tsare da ita.

"Mun roke su, su ba mu ruwa aƙalla ko don yaron nan maraya, amma suka ƙi," in ji Alawia.

Ta ƙara da cewa ta matsa domin ta je rijiyar amma mayaƙan suka mangare ta.

Iyalan sun ci gaba da tafiya haka a galabaice cikin ƙishirwa har sai da suka kai Tawila, inda isarsu ke da wuya sai Alawia ta zube ƙasa, nan da nan aka garzaya da iya asibiti.

An sallame ta bayan an yi mata magani. Haka shi ma yayanta Marwan an yi masa maganin raunukan da ya ji a lokacin da mayaƙan suka yi masa duka.

Alawia ta ce daga nan ne suka shiga neman dangin wannan yaron da suka ceto, bayan sun same su, suka danƙa musu shi.

A yanzu Alawia da iyalanta na zaune a Tawila, inda wasu iyalai suka karɓe su, suka ba su masauki a gidansu.

"Yanzu dai rayuwa mun gode wa Allah, amma muna da fargabar yadda za ta iya kasancewa a nan gaba," Alawia ta shaida wa BBC.

Marwan ya ce yana son ya tafi ƙasar waje domin ya samu damar ci gaba da karatunsa, ya kuma fara sabuwar rayuwa.

Wannan shi ne abin da miliyoyin 'yan ƙasar ta Sudan suka yi, saboda yadda yaƙin da ba shi da alamar ƙarewa, ya ɗaiɗaita rayuwarsu.

Taswirar da ke nuna yankunan da ke hannun kowane ɓangare a yaƙin na Sudan