Mai haƙa ƙabarin da 'aiki ke hana shi barci' saboda yaƙin Sudan

Asalin hoton, Ken Mungai / BBC
- Marubuci, Barbara Plett Usher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Khartoum
- Lokacin karatu: Minti 5
Sojojin gwamnatin Sudan sun ƙwace iko da Khartoum, babban birnin Sudan kimanin shekara biyu bayan dakarun RSF sun fatattake su. BBC ta samu shiga cikin kariyar sojojin na Sudan domin ganin yadda ta kaya a lokacin.

Mutanen Sudan ne dai suke shan wahalar yaƙin, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, tare da jefa wasu yankunan ƙasar cikin yunwa da bala'i.
A cikin ƴan watannin nan ne sojojin gwamnatin ƙasar suka ƙwace iko da arewaci da gabashin da tsakiyar babban birnin ƙasar, Khartoum.
Wannan yunƙurin sojojin ya faro ne tun daga makon jiya.
An zagaya da wakilan BBC domin ganin yadda ake gwabzawa a arewacin Khartoum a tsakar dare.
Mun ga sojojin a lokacin da suke shirye-shiryensu, cike da ƙarfin gwiwa suna waƙe-waƙe domin shirin faɗawa birnin.
Da sanyin safiya suka kusa, ko da yammar washegari, sun riga sun ƙwace iko da manyan wuraren RSF, wanda hakan ya sa sojojin da suke kudu maso yamma na birnin suka kawo ɗauki ga sojojin hedkwatar da arewaci.
A ranar Alhamis, sojojin sun samu nasarar kai wani hari kan jerin-gwanon motocin dakarun RSF da suke ƙoƙarin ficewa daga fadar shugaban ƙasar, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Wani faifan bidiyo da sojojin suk fitar ya nuna yadda jirage marasa matuƙa suke ɓarin wuta a kan motocin, da kuma yadda wuta ke tashi, wanda wataƙila na bama-baman da mayaƙan RSF suke tafiya da su ne.
Fadar gwamnatin na da matuƙar muhimmanci a siyasar ƙasar, domin a ciki ne shugaban ƙasa da iyalansa suke rayuwa.

Asalin hoton, Ken Mungai / BBC
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani mutum da yake ƙoƙarin ƙarfafa gwiwar sojojin shi ne Abidin Durma, wanda fitaccen mai aikin haƙa ƙabari ne a garin Omdurman, wanda ke kusa da birnin Khartoum.
Yana cikin maso yi wa sojojin ƙasar fatan alheri, inda yake kiran yaƙin da "yaƙin kare mutunci."
Amma kullum yana ganin yadda yaƙin ke cin rayukan fararen hula.
Durma jika ne a iyalan Mahdi, wanda yake cikin waɗanda suka kafa ƙasar Sudan a ƙarni na 19.
Iyalansu ne suka kafa maƙabartar Ahmed Shafi, wanda yake cikin tsofaffain maƙabartu a Omdurman.
Yanzu maƙabartar, wadda Durma ya kwashe gomman shekaru yana aiki ya fara zama wuri mai tayar da hankali.
An ƙara faɗaɗa maƙabartar da kimanin hekta huɗu, da jerin ƙaburbura nan wasu da suna, wasu babu. Sannan wari kawai kake ji da ka shiga cikin maƙabartar.
Durman ya shaida min cewa shi da masu taya shi suna binne "gawarwaki tsakanin 25 zuwa 30 zuwa 50 a kullum."
Wannan bai rasa nasaba da cewa sauran maƙarbatun ba a iya zuwa a lokacin da yaƙin ke zafi a Omdurman, birnin da yake ciki da masu gudun hijira, kuma kiwon lafiya a birnin ya zama sai a hankali.

Asalin hoton, Ken Mungai / BBC
Durman ya nuna min wani babban ƙabari da aka binne wasu gawarwakin da harin sama ya kashe a wata makaranta.
A wani ɓangaren maƙabartar, gawarwakin waɗanda aka kashe ne a wani hari ta sama da aka kai a wata kasuwa a watan Janairu, inda aka kashe mutum 120.
An faɗa mana cewa dakarun RSF ne suka kai harin a yankin wanda sojojin ƙasar suka fi yawa a Omdurman. Amma da RSF ɗin da sojojin ƙasar sun zarge su da aikata laifukan yaƙi - an zargi sojoji da kisan kiyashi a wasu wuraren.
Ana kawo gawarwakin ne daga asibiti, inda suke kiransa su shaida masa domin ya shirya.
"Ana kawo su muke binne su saboda ba mu da isasshen firji da za mu adana gawarwaki," in ji Durman.
"Ba mu samun lokacin barci har mun gama binne gawar ƙarshe da aka kawo," in ji shi, "sannan bayan na fara barcin da misalin awa 1 ko minti 15, sai in ji kira. Da an kira sai ina taso kamar yanzu, ka ga daga zuwa har an kawo gawarwaki huɗu."
"Muna ganin gawarwakin da aka kashe da harsasai da waɗanda hare-hare da sama suka kashe, wasu suna zaune a gidajensu aka kashe su. Kashe-kashen sun yi."
Yana cikin jawabi sai ga wani kirar a wayarsa za a kawo wata gawar.

Asalin hoton, Ken Mungai / BBC
Sallar gawa kuma ya zama ruwan dare a garin al-Mabrouka, garin da ke kusa da ke kusa da yammacin al-Thawra na Omdurman, wanda ya raba tsakanin dakarun RSF da sojojin gwamnatin ƙasar Sudan.
Wasu mutane sun taru domin jaje ga Abazar Abdel Hamis a wani masallaci, suna ɗaga hannu suna addu'o'i.
Kafin wannan ranar, mun samu Abdel Hamid a wajen adana gawarwaki na asibiti inda ya je ɗauko gawarwakin ɗan'uwansa da surukarsa. An kashe su ne a hanyarsu ta kai ƴarsu makaranta.
A cikin gidan kuma, mun ga wata ƙaramar yarinya mai suna Omnia tana kuka.
Tana hannun mahaifiyarta ne lokacin da wani hari ya riske su, wanda ya kashe iyayenta, amma cikin ikon Allah ta tsira da rauni a ƙafarta.
Yanzu an mayar da ita marainiya tare da ƴanuwant guda uku.
Na shiga cikin wasu waɗanda suka taru a wani ɗaki domin jimamin rasuwar, kamar yadda suke yi idan an kashe wani a yaƙin.
Daily we are losing our children. The students cannot settle, there is no studying. There is always a state of fear - we are always in a state of sadness"
"A ƙarƙashin gado muka ɓoye da aka fara harbe-harben," in ji Ilham Abdel Rahman, lokacin da aka tambaye ta yadda suke kare ƙananan cikinsu.
"Wani bam ya sauko a gidanmu, inda ya kashe yarinyar maƙwabciyarmu a ƙofar gida."
Hawa Ahmed Saleh ta ce, "idan an yi ruwan bama-bamai da safiya, sai mu tafi kasuwa da yamma."
"Idan ba mu ji harbe-harben ba, sai mu zauna muna jiran tsammani. Yaranmu kullum suna cikin firgici da tashin hankali."
Idan sojojin ƙasar suka tabbatar da kasancewarsu a babban birnin ƙasar, za a samu sauƙin ruwan bama-baman.
Sai dai za a cigaba da yaƙin a wasu sassan na Sudan, kuma yaƙin zai cigaba da zama zukatan ƴan ƙasar na tsawon lokaci.













