Shin tattaunawar sulhu za ta kawo ƙarshen yaƙin Sudan?

    • Marubuci, by Jeremy Howell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5
Dakarun sojin Sudan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dakarun sojin Sudan yayin da suke tsare wani wuri a yankin gabashin ƙasar.

A ranar Larabar da ta gabata ne Amurka ta yi ƙoƙarin gayyato wakilai daga ɓangarori biyu da ke yaƙin Sudan domin tattauna yadda za a kawo ƙarshen yaƙin ƙasar a birnin Geneva.

Yaƙin wanda aka fara tun cikin watan Afrilun 2023 ya haifar da matsaloli daban-daban masu yawa kan fararen hula fiye da miliyan 25.

To sai dai, rundunar sojin Sudan, wadda ke jagorancin ƙasar, ta ce ba za ta tura wakilai zuwa zaman ba.

To me zaman zai cimma, idan har babu wakilan rundunar sojin ƙasar?

Me ya janyo yaƙin basasar Sudan?

Shugaban Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ke jinjana wa dandazon jama'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A shekarar 2021 ne Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ƙwace mulkin ƙasar

A shekarar 2021 ne, Shugaban rundunar sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya ƙwace mulkin ƙasar a wani juyin mulki.

A lokacin juyin mulkin, ya samu taimakon Janar Mohamed Hamdan Dagalo, da aka fi sani da “Hemedti”, wanda shi ne shugaban rudunar dakarun RSF masu sanye da kayan sarki.

Daga nan ne shugabannin biyu suka fara samun saɓani kan raba iko tsakaninsu, da kuma makomar tallafin kuɗin da ake bai wa rundunar RSF. A watan Afrilun 2023 saɓanin ya rikiɗe zuwa yaƙin basasa.

A yanzun dakarun RSF ne ke iko da mafi yawan sassan Khartoum, babban birnin ƙasar, da mafi yawan yankunan lardin Darfur da ke yammacin ƙasar, da kuma jihar Al Jezira wadda ke samar da mafi yawan kayan amfanin gona a ƙasar.

A ɗaya bangaren kuma rundunar sojin Sudan ce ke iko da gabashi da arewacin ƙasar.

A yanzu haka kuma ɓangarorin biyu na tsaka da fafatawa da juna a ƙoƙarinsu a karɓe iko da El Fasher, babban birnin arewacin Darfur da kuma wasu yankunan birnin Khartoum.

General Mohamed Hamdan Dagalo, also known as "Hemedti"

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohamed Hamdan Dagalo, da ka fi sani da "Hemedti", na samun goyon bayan ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma sojojin Hayar Rasha, kamar yadda rahotonni suka nuna.

Duka ɓangarorin biyu na samun goyon bayan ƙasashen waje, waɗanda ke taimaka musu ci gaba da yaƙin.

Rundunar sojin ƙasar na samun goyon bayan ƙasashen Saudiyya da Masar, yayin da Iran ke samar mata da makamai. Ita RSF na samun goyon bayan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Haka rahotonni sun nuna cewa kamfanin sojojin hayar Rasha, Wagner na da alaƙa da RSF, to sai dai ta musanta taka kowace irin rawa a yaƙin.

Wace wahala yaƙin basasar ya janyo a ƙasar?

Sudanese refugees arrive by lorry in South Sudan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yaƙin na Sudan ya tilasta wa kusan mutum miliyan 11 barin gidajensu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce “fararen hula na cikin mummunar halin tagayyara” a Sudan, inda mutum miliyan 21 - kusan rabin al'ummar ƙasar - na cikin ''mummunar yunwa”.

Kusan mutum miliyan 11 ne suka rasa muhallansu.

Fiye da mutum 750,000 ne ke kan hanyar faɗa wa yunwa, kamar yadda alƙaluman hukumar samar da Abinci suka nuna.

An ƙiyasta cewa mutum 16,650 ne aka kashe a yaƙin, kamar yadda cibiyar ACLED mai tattara alƙaluman rikice-rikice ta bayyana.

An zargi duka ɓangarorin da ke yaƙin da aikata laifukan yaƙi, ciki har da fyaɗe mai yawa da azabtarwa da kuma kisan kiyashi kan fararen hula.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yaƙin sudan da ''rikicin da ba za manta da shi ba'' sannan kuma ta yi kiran gaggauta tsagaita wuta, a matsayin hanya ɗaya da za ta takaita bazuwar ƙarin yunwa.

Mutanen da suka guje wa rikici a kudu maso gabashin Sudan na samun tallafin abinci daga wata gidauniya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Miliyoyin 'yan Sudan na buƙatar talafin abinci saboda yaƙin

Me ya sa sojojin ƙasar suka ƙi halartar zaman?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wakilin Amurka na musamman a Sudan, Tom Perriello, ya shafe tsawon watanni yana ƙoƙarin janyo hankalin shugannin sojin ƙasar da na RSF domin tattaunawa ƙeƙe-da-ƙeƙe.

An tsar cewa za a fara tattaunawar a ranar 14 ga watan Agusta a birnin Geneva, inda gwamnatocin ƙasashen Saudiyya da Swizerland za su jagoranci zaman.

Haka kuma zaman zai samu halartar masu zanya idanu da suka haɗa da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ke gyon bayan RSF, da kuma Masar wadda ke goyon bayan Rundunar sojin ƙasar, da kuma Majalisar Dinkin Duniya da Ƙungiyar Haɗin kan Afirka.

Rundunar RSf ta ce za ta tura wakilai zuwa tattaunawar, to amma ita rundunar sojojin ƙasar ta ƙi.

"Janar al Burhan ya sha faɗin cewar 'babu sulhu, tsakaninsa da RSF a yanzu,'' kamar yadda Alan Boswell na ƙungiyar 'International Crisis Group' ya shaida wa BBC.

"Ya ce ba zai tura wakilai zuwa zaman ba, har sai an ayyana Rundunar sojin ƙasar a matsayin waɗanda ke jagorancin halastaccyar gwamnatin ƙasar, to sai RSF ta ƙi amincewa da hakan''. Wannan wani saɓani ne da jami'an diplomasiyya ba za su iya warwarewa ba.

Akwai kuma wani dalilin da ya sa Janar al-Burhan ya ƙi halartar zaman, kamar yadda Alex Vines na Chatham House, ya bayyana wa BBC.

"Rundunar sojin ƙasar na son a yi sulhun ne a matsayn wadda ke da ƙarfi,'' in ji shi, Ina tunanin za ta samu wata dama, idan ta halarci tattaunawar a wannan a matsayi.

Haka kuma Janar Burhan ya saurari koken gamayyar manyan hafsoshin sojin ƙasar da 'yan siyasar da yake jagoranta a gwamnatinsa, in ji Mista Vines, kuma mafi yawansu na adawa da yaƙar RSF.

Hayaki na tashi a wajen birnin Khartoum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A yanzu haka ana ci gaba da gwabza faɗa a wajen birnin Khartoum.

Me tattaunawar za ta cimma?

Amurka ta ce ko Sojojin Sudan ba su tura wakilai ba, za ta iya ci gaba da tattaunawar.

"Za ta yi magana da masu goya wa ɓngarorin biyu a yaƙin wata MAsar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa waɗanda ta yi amanna za su isar musu da saƙon da aka tattaunar," in ji Mista Boswell.

"Idan aka samu nasarar cimma matsaya, to akwai yiwuwar su tilasta wa ɓangarorin da faɗa da juna su y aiki da yarjejeniyar da aka cimma."

A baya an yi jarjejeniyoyn zaman lafiya da dama da ba su yi nasara ba.

Tun daga watan Mayun 2023, wata guda bayan ɓarkewar rikicin, Saudiyya da Amurka suka ɗauki nauyin zaman sulhu a birnin Jedda na Saudiyya.

Bangarorin biyu sun sha amince da ƙudurin tsagaita wuta, amma daga baya sai su ci gaba da yaƙin.

"A taƙaice samun zaman lafiya a Sudan abu ne da sai an dage," in ji Mista Vines. "To sai dai wannan ba dalili ne na rashin yin wani yunƙuri ba," in ji shi.