Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Majalisar dokokin Kano ta gabatar da ƙudurin tsige mataimakin gwamnan jihar
Majalisar dokokin jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam, bisa wasu zarge-zarge da aka gabatar a kansa a gaban majalisar, ranar Alhamis.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawal Hussaini ne ya gabatar da ƙudurin tsige mataimakin gwamnan kan zarge-zarge da suka haɗa da almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin da ya shugabanci wasu hukumomin gwamnati.
A kan haka ne majalisar ta ce, kamar yadda doka ta tanada, ta yanke shawarar sanar da mataimakin gwamnan game da matakin da ta fara ɗauka na tsige shi.
A watan Janairu ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir ya sanar da sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a matakin tarayya, daga jam'iyyar NNPP, wadda ya lashe zaɓe ƙarƙashin ta a shekarar 2023.
Sai dai mataimakin nasa Aminu Abdulsalam bai bi shi zuwa jam'iyyar ta APC ba.
Wannan ya haifar da muhawara, inda wasu daga cikin manyan masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar suka fara neman mataimakin gwamnan ya sauka daga muƙamin nasa.
Ƴan majalisa 38 daga cikin 40 na majalisar dokokin jihar Kano ne suka gabatar da ƙudurin a zauren majalisar.
Laifukan da ake tuhumar Aminu Abdulsalam
Manyan ƙorafe-ƙorafen da majalisar ta gabatar, kamar yadda shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin ya bayyana sun ƙunshi batu ne na "cin amanar aiki da cin amanar gwamnati a matsayin kwamshinan ƙananan hukumomi tsakanin 2023 zuwa 2025 yayin da kuma yake a matsayin mataimakin gwamnan jihar'.
Lawal Hussaini ya ce: "Yayin shugabancin ma'aikatar ƙananan hukumom a matsayin kwamishina Aminu Abdulsalam "ya shiga dumu-dumu wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati da aka ware wajen tafiyar da lamurran ƙananan hukumomi, inda aka yi amfani da su wajen yin wasu abubuwa waɗanda ba su ne maƙasudin ware kuɗaden ba.
Laifukan su ne:
- Tsakanin shekara ta Yuni 2023 zuwa Janairu 2024 ya karɓi kuɗi daga ƴan kwangila har naira miliyan 1.5 daga kowace ƙaramar hukuma, wato miliyan 66 a kowane wata, har na tsawon wata bakwai. Wanda hakan ne nufin ya karbi naira miliyan 462, wadanda ya yi amfani da su kan abubuwa na ƙashin kansa.
- Tsakanin watan Janairun zuwa Yulin 2024 ya karɓi wasu kudade da sunan gudanar da wasu ayyuka na musamman, waɗanda suka kai miliyan 3,250 daga kowace ƙaramar hukuma 142.2 na tsawon wata shida, wanda jimilla ya kai naira miliyan 726.
- Cin amanar ofis, ta hanyar yin amfani da ofishinsa wajen sanya ƙananan hukumomi su bai wa kantin sayar da magani na Novomed kuɗi har naira miliyan 440.
A cewar takardar, wannan ya zama cin amanar al'umma, da zagon ƙasa ga ayyukan ofishinsa da kuma zubar da ƙimar gwamnati a idon al'umma.
Takardar ta ce wannan ya saɓa da tsarin adalci da ake buƙatar gani daga mai riƙe da muƙamin mataimakin gwamna.
Abin da tsarin mulkin Najeriya ya ce kan tsige gwamnan
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi bayanin yadda ake aiwatar da tsige gwamna a ƙasar daga mataki zuwa mataki, kamar yadda Barista Audu Bulama ya tabbatarwa BBC.
Ya ce ''Matakai guda shida ne kundin tsarin mulki ya gindaya cewa sai an bi su kafin gwamna ko mataimakinsa ya tsigu a Najeriya.''
Masanin shari'ar ya yi bayanin matakan kamar haka:
Rubutacciyar sanarwa.
Kundin mulkin Najeriya ya ce dole a samu sa hannun aƙalla ɗaya bisa uku na ƴan majalisar dokokin jihar da suka rubuta takardar sanarwa cewa suna da zarge-zarge a kan gwamna, kuma su rubuta dalla-dalla cewa ga irin abubuwan da suke zargin gwamnan. Za su rubuta asikar tasu ne ga shugaban majalisar dokokin jihar, wanda shi kuma a cikin kwana bakwai doka ta yi tanadin lallai ya sanar da gwamna sammacin.
Kaɗa ƙuri'a majalisa
Mataki na biyu shi ne inda majalisar za ta yi zama kuma dole sai an samu kashi byu bisa uku na jimillar ƴan majalisa da suka amince cewa sun yarda a binciki gwamna game da zargin da ake masa.
Rubutawa alƙalin alƙalai na jihar
Shugaban majalisa zai rubutawa alƙalin alƙalai na jihar cewa kashi biyu bisa uku na ƴan majalisa sun buƙaci a binciki gwamna kan wasu zarge-zarge domin haka yana neman alƙalin ya kafa abinda ake kira ''kwamitin mutum bakwai''. Kundin mulki ya fayyace cewa alƙalin alƙalan ne kawai zai iya kafa wannan kwamiti na mutum bakwai kuma kundin mulkin ya ƙayyade cewa lallai sai sun zamo nagartattun mutane, ba ƴan siyasa ba, ba ma'aikatan gwamnati ba kuma waɗanda basu goyon bayan kowanne ɓangare na dambarwar.
Bincken kwamiti
Kundn mulki ya bai wa wannan kwamitin mutum bakwai wa'adin wata uku ya gudanar da bincikensa. Kuma a cikin binciken nasu dole ne a bai wa gwamna cikakkiyar dama ya kare kanshi.
Rubuta wa majalisa
Idan kwamitin ya gama aikin binciken, sai ya rubutawa majalisa cewa kodai ya samu gwamna da laifin da ake zarginsa da aikatawa ko kuma akasin hakan.
Zabe tsakanin ƴan majalisa
Mataki na shida shi ne inda majalisa za ta kaɗa ƙuri'a domin amincewa da tsige gwamnan. Wannan kuma yana faruwa ne bayan kwamitin mutum bakwai ya tabbatar cewa ya samu gwamnan da laifi. Duk da haka majalisar za ta zaɓe domin samun rinjayen kashi biyu bisa uku kafin amincewa da tsige gwamnan. Idan kuma kwamitin mutum bakwai ya rubuto cewa bai samu gwamna da laifi ba, to majalisar ba zata kaɗa ƙuri'ar ƙarshe ta shige gwamnan ba.