Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda yaƙin Iran zai iya shafar aikin Umrah
Ƴan Najeriya maniyyata aikin umrah a ƙasar Saudiyya cikin watan Ramadan sun shiga halin rashin tabbas saboda yadda yaƙin da Isra'ila da Amurka ke yi da Iran ke neman ya shafi tafiyar su aikin.
Yaƙin na ci gaba da tilasta wa mahukunta rufe sufurin jiragen sama a wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya shafi ayyukan kamfanoni masu jigalar matafiya da kuma maniyyata aikin Umrah.
Miliyoyin musulmai ke halartar aikin Umrah a Saudiyya a cikin Ramadan, inda a 2025 kacal fiye da mutane miliyan 122 suka yi aikin, kamar yadda ƙidaddiga ta nuna.
Amma zaman ɗar-ɗar da aka shiga a Gabas ta tsakiya, wanda ya janyo rufe wasu muhimman filayen jirgin sama da ake bi domin jigilar maniyyata ya jefa ƴan Najeriya masu niyyar zuwa aikin Umrah na tuninin ko aikin ba zai yiwu ba.
Ƙasashen Iran da Iraq da Israel da Syria da Kuwait da Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa duk sun sanar da rufe filayen jirgin sama na ɗan wani lokaci bayan Amurka da Isra'ila sun ƙadaddar da jerin hare-hare kan Iran, lamarin da ya durƙusar da sufurin jirgin sama a Gabas ta Tsakiya.
Wannan lamari ya jefa fargaba a zukatan maniyyata daga Najeriya, saboda tsoron abin da zai iya hana su damar gudanar da wannan ibada.
Kawo yanzu dai hukumomin Saudiyya ba su sanar da rufe filayen jirgin saman ƙasar ba, amma akwai fargabar cewa hare-haren da Iran ke kai wa zasu iya shafar jigila zuwa ƙasa mai tsarki.
Tun daga lokacin da rikicin gabas ta tsakiya ya soma tafiye-tafiyen jirgen sama sun funkanci cikas. Wannan lamari dai ya haifar da gagarumin cikas ga maniyyata da ke shirin zuwa ko komawa gida daga Umrah a kasar Saudiyya, kuma babu tabbacin yuwar hakan muddin hare-haren da Amurka da Isra'ila da Iran suka ci gaba.
Alhaji Zaharaddeen Abubakar na daga cikin maniyyata da ke jiran zuwa umrah a kasar ta Saudiyya, ya kuma shaidawa BBC cewa fargabar su ba ta wuce yadda wasu sun riga sun kama ɗakuna kuma suna da duk takardun tafiya amma babu hali.
''Wanda ya ke can (Saudiyya)kuma, ya gama aikin ibadar shi zai dawo, idan jiragen da ke can ba za su tashi ba, ka ga shima abin fargaba ne.'' In ji Alhaji Zaharaddeen.
Sai dai ya jaddada cewa tunda aikin ibada ne, ba za a gajiya ba in dai aka samu dama.
Alhaji Zaharaddeen Abubakar ya kuma nemi hukumomi a Saudiyya su ɗauki mataki domin tabbatar da ganin musulmai daga sassan duniya sun samu damar zuwa aikin Umrah ba tare da matsala ba.
Ya ce ''Lokacin aikin hajjin bara da ya wuce, a daidai lokacin an yi faɗa tsakanin Iran da Isra'ila, wanda maniyyata na Iran su ma sun samu itrin wannan matsala wanda Saudiyya ta ɗauki nauyin su tare da samar masu wajen zama, kuma hakan ya sa ba su samu wani ƙalubale ba har lokacin da aka dakatar da wannan yaƙin,
To yanzun ma fatan mu shi ne ya zama an samu kulawa ta musamman.''
Alhaji Musa Rabi'u Muhammed shi ne shugaban kamfanin da ke shirya tafiye-tafiye na Murna Travel Agency da ke jihar Kano a Najeriya, kuma ya shaidawa BBC cewa ''akwai mutanenmu wanda har sun shiga jirgi yana shirin tashi , amma dole aka dawo aka sauke su, yanzu haka suna gida.
''Duk wani jirgi wanda yake a nan gabas ta tsajiya, to wannan matsala ta shafe shi.'' in ji Alhaji Musa Rabi'u.
Ya ƙara da cewa a iya sanin shi babu wata fargaba a yanzu, amma a duk lokacin da ya faɗa a birnin Jiddah, nan fargaba ta ke.
Kawo yanzu dai wasu jiragen sun tashi daga ƙasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da Italiya da Switzerland, amma an soke tashin wasu jirage da dama.
Amurka da Isra'ila dai na ci gaba da kai munanan hare-hare a Iran.