Ko ya kamata a riƙa zubar da ruwan da aka tafasa shinkafa?

Lokacin karatu: Minti 3

Shinkafa na ɗaya daga cikin abincin da aka fi amfani da shi a Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Amma a yanzu, ɗabi'a ta girke-girke ta canza yadda ake sarrafata inda yawancin mutane ke dafa shinkafar har sai ta kusan dahuwa, sannan su sauke su tace ruwan kafin su ƙara maidata wuta domin ta kammala dahuwa.

Wannan hanya ta zama ruwan dare, musamman ga masu tunanin cewa hakan na taimakawa wajen cire datti ko kawar da ƙwayoyin cuta

Sai dai masana kimiyyar abinci na gargaɗin cewa wannan dabi'a na iya rage amfanin shinkafa ga jikin ɗan'adam kamar yadda ƙwararre a harkar abinci Dr. Awwal Musa ya bayyana wa BBC.

Ya ce irin wannan hanya na iya rage yawan sinadaran gina jiki da shinkafa ke ɗauke da su.

A cewarsa, "idan aka dafa shinkafa har ta kusan dahuwa sannan aka sauke aka tace ruwa mai kaurin da ke cikin shinkafar, yawancin sinadaran da suke narkewa a ruwa suna ɓacewa."

"Idan aka yi wa shinkafa haka, ba ta da wani amfani mai yawa ga lafiyar jiki kamar yadda ya kamata," in ji shi.

Ya ƙara da cewa, shinkafa, musamman wadda ba a cire ɓawon gaba ɗaya ba wato brown rice, har da ma wadda aka cire ɓawon na ɗauke da sinadaran da ke taimaka wa jiki wajen ayyukan yau da kullum.

"Waɗannan sinadarai suna narkewa a ruwa a lokacin da ake dafa shinakafar, saboda haka, idan aka tafasa shinkafa sannan aka zubar da ruwan, to kamar ana zubar da wasu daga cikin muhimman abubuwan da jiki ke buƙata ne," in ji ƙwararren harkar abincin.

Waɗanne sinadarai ne ke cikin shinkafa?

Dr Awwal ya ce shinkafa na ɗauke da muhimman sinadarai wanda za a amfana da su idan ba a zubar da ruwan da aka tafasa shinkafa ba da suka haɗa da nau'ukan Vitamin B kamar

  • Sinadarin Thiamine B1 wanda ke taimaka wa jiki wajen canza abinci zuwa sinadarin kuzari kuma yana tallafa wa lafiyar jijiyoyi.
  • Sinadarin Niacin B3 wanda ke taka rawar gani wajen narkar da abinci da kula da lafiyar zuciya.
  • Sinadarin Pyridoxine B6 mai taimakawa wajen samar da sinadarin 'red blood cells' da kuma gyaran ƙwayoyin halitta.
  • Folate B9 wanda ke da muhimmanci wajen samar da kuzari da kuma taimaka wa mata masu juna biyu wajen kariya ga jariri.

Baya ga Vitamin, masanin ya kuma ce shinkafa na ɗauke da wasu muhimman sinadarai da suka haɗa da:

  • Sinadarin dusa wato fibre da ke taimaka wa wajen narkar da abinci da inganta lafiyar hanji.
  • Sinadarin magnesium wanda ke taimaka wa tsoka da jijiyoyi su yi aiki yadda ya kamata.
  • Sinadarin Iron mai taimakawa wajen samar da jini.
  • Selenium mai ƙarfafa garkuwar jiki.
  • Maganesium kuma na taimaka wajen inganta ƙashi.

Masanin cimakan ya ce waɗannan sinadaran na aiki tare wajen ba jiki kuzari da inganta lafiyar fata da ƙarfafa garkuwar jiki da kuma taimaka wa wajen samar da jini da inganta aikin kwakwalwa. "Saboda haka, duk wata hanya ta girki da ke rage su, na iya rage amfanin abincin."

Yaya ya kamata a tsaftace shinkafa?

Tambayar da mafi yawan mutane ke yi ita ce ta ya ya za a tsaftace shinkafa ba tare da cire ko rage sinadaranta ba?

A cewar Dr. Musa, hanya mafi dacewa ita ce tsaftace shinkafa kafin girki maimakon zubar da ruwan bayan ta kusan nuna.

Ya bayyana matakai kamar haka wajen tsaftace shinkafa.

  • Tsince tsakuwa ko tarkace daga cikin shinkafar da hannu.
  • Wanke ta da ruwa sau ɗaya ko biyu domin cire ƙura.
  • Wajen dafawa kuma, za a zuba ruwa gwargwadon yadda shinkafar take a tukunya, idan kuma ruwan ya tsotse kafin ta dahu, a ƙara ruwa kaɗan kaɗan har sai shinkafar ta dahu.

Waɗannan matakan na taimaka wa shinkafa ta dahu ba tare da rasa sinadaranta ba, kamar yadda ƙwararren ya bayyana.

Dr Awwal ya kuma ce idan har mutum yana so dole sai ya tafasa shinkafar ta kusan dahuwa kafin ya tace ya wanke kuma ya mayar a wuta, to ya kamata ya tabbatar da cewa akwai wasu na'ukan abinci da zai haɗa da shinkafar da za su ba da waɗannan sinadarai kamar ganye da nama da kifi ko ƙwai da dai sauransu.

"Waɗannan su ne za su maye gurbin abin da aka rasa."