Yadda APC da ADC ke sabinta rijistar mambobinsu

Lokacin karatu: Minti 2

Jam'iyyun siyasa a Najeriya sun ƙara ƙaimi wajen sabinta rijartar mambobinsu yayin da wa'adin da aka gindaya domin kowacce ta miƙawa hukumar zaɓen ƙasar cikakkiyar rijistar ke kawo jiki.

Wannan na daga cikin shirye-shiryen tunkarar baban zaɓen ƙasar na 2027.

A ƙarƙashin sabon jaddawalin zaɓen da hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta fitar, ana buƙatar jam'iyyun siyasar ƙasar su gabatar da cikakkiyar rijistar mambobinsu ya zuwa ranar 2 ga watan Afirelun 2026.

Umarnin da INEC ta bai wa jam'iyyun siyasar na daga cikin tanadin dokar zaɓen Najeriya ta 2026, wadda ke neman inganta yadda jam'iyyun siyasar ƙasar ke gudanar da harkokin su na cikin gida da kuma samar da tsari mai kyau na fitar da ƴan takara a cikin jam'iyyun.

Wannan na zuwa ne yayin da wasu masu sharhi ke gnin cewa jam'iyyun na da ƙarancin kayan aiki na cika ƙa'idar hukumar zaɓe (INEC) wadda ke neman rijistar mambobin jam'iyyun siyasar ya zamo ta hanyar amfani da fasahar zamani, musamman ta la'akari da ƙurarren lokacin da aka ware domin wannan aiki.

Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar ta ce ta fara aikin sabinta rijistar mambobin nata, wanda ta ce yaa gudana cikin nasara a dukkan mazaɓun ƙasar ciki harda na Abuja babban birnin Najeriya.

Sanarwar da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar Felix Moka ya wallafa a shafinta na X, ta ce aikin zai samar da cikakkiyar rijistar mambobin APC na ƙasar, ya kuma tabbata jam'iyyar ta cika ƙa'idar shiga zaɓe mai zuwa.

Ya yi bayanin cewa tsaffin ƴaƴan APC da kuma sabbi ne suka yi wannan rijista ta amfani da lambar katinsu na ƴan ƙasa wato NIN.

APC ta ce wannan dama ce ga dukkan ƴan Najeriya da suka cika shekara 18 su shiga dama ta shiga a dama da su a fagen siyasar ƙasar, musamman a wannan lokaci da jam'iyyar ta ce tana aiwatar da sabon tsarin bunƙasa fahimtar juna tsakanin mambbinta.

Itama jam'iyyar adawa ta ADC ta soma rajistar inda a cikin wani bayani da ta fitar mai dauke da sa hannu sakataren watsa labaranta na ƙasa Bola Abdullahi, ta bayyana cewa ta fara aikin mambobinta ta hanyar latironi domin tunkarar manyan zabukan 2027 da ma na share fage a nan gaba kadan.

Jam'iyyar ta ce a yanzu haka dubban 'ya'yanta a fadin Najeriya na ci gaba da yin rajistar.

Jam'iyyar ta ADC da ke gaba-gaba a jam'iyyun adawar kasar ta bayyana cewa sai wadanda suka yi cikakkiyar rajista da ita kuma aka dauki bayanansu ne za su shiga zabukanta na share fage.

Faisal Kabir shi ne mai magana da yawun jam'iyyar ta ADC a Najeriya kuma ya shaidawa BBC cewa ''Babu abin da za mu ce sai godiya, yadda ƴan Najeriya suka fito suka nuna cewa suna tare da ADC, domin ni jiya na yi tunanin ma dukkan ƴan Najeriya ne suke jam'iyyar ADC.''

Ya ce rijistar ta su ta bayar da mamaki, kuma ta zarce wadda jam'iyyar APC mai mulki ke yi.

''Kowa zai je mazaɓar shi ya yi rijista, kuma muna yin shi online yadda kowa zai iya ɗaukar wayar hannunsa ya yi cikin kwanciyar hankali.''