Barcelona na neman Micky van de Ven, an bai wa Arsenal amsa kan Esposito

Lokacin karatu: Minti 2

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona na shirin ƙara ƙaimi wajen ƙoƙarin sayen ɗan wasan bayan Tottenham Hotspur, Micky van de Ven, mai shekara 24, inda ake sa ran za ta matsa lamba domin ɗauko ɗan wasan na ƙasar Netherlands a lokacin bazara mai zuwa.(Sport Spanish)

Ƙungiyar Manchester United na shirin miƙa sabuwar yarjejeniya mai tsoka ga kyaftin ɗinta, ɗan wasan tsakiya na Portugal Bruno Fernandes, wadda za ta kai har fam 400,000 a mako. Sai dai ɗan wasan mai shekara 31 zai yanke hukunci kan makomarsa a Old Trafford ne bisa ko ƙungiyar ta samu gurbin shiga gasar UEFA Champions League. (Mirror)

Makomar ɗan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, a Manchester United na nan daram, yayin da tattaunawa kan sabuwar kwantiragi ke ci gaba (Mail)

An shaida wa Arsenal cewa Inter Milan ba za ta sayar da matashin ɗan wasanta, ɗan Italiya Pio Esposito, mai shekara 20, ba ko da a kan kowane farashi. (Gazzetta dello Sport)

Ƙungiyar Juventus na shirin ci gaba da neman ɗan wasan gaba na Faransa na Paris Saint-Germain Randal Kolo Muani, mai shekara 27, wanda a yanzu yake zaman aro a Tottenham. (Calciomercato)

Aston Villa F.C. na daga cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan tsakiya na Wales Harry Wilson, mai shekara 28, wanda kwantiraginsa da Fulham F.C. zai ƙare a bazara. (Fabrizio Romano)

Ana sa ran Brentford za ta sallami 'yan wasa har guda biyar a bazara, ciki har da ɗan wasan tsakiya na Portugal Fabio Carvalho, mai shekara 23. (The I)

Manchester United ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan tsakiya na Ingila Mason Mount, mai shekara 27, duk da sha'awar da Aston Villa da Fulham ke nunawa. (Football Insider)

Juventus na ganin ta samu ci gaba wajen tsawaita kwantiragin ɗan wasan gabanta na Serbia Dušan Vlahović, mai shekara 26, wanda yarjejeniyarsa za ta ƙare a bazara. (Tuttosport)

Tattaunawa kan sabunta kwantaragin ɗan wasan tsakiya na Austria Konrad Laimer a Bayern Munich ta tsaya cik saboda bambancin da ke tsakanin ɓangarorin biyu kan sharudda. (Sky Sports Germany)