Me ya sa Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran hari, kuma yaushe yaƙin zai ƙare?

    • Marubuci, Olivia Ireland
  • Lokacin karatu: Minti 4

Rikici ya ɓarke a Gabas ta Tsakiya bayan kashe jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei, a wasu hare-haren da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar.

Bayan harin, shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci al'ummar Iran su tuntsurar da gwamnati.

A matsayin martani, Iran ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a wurare da dama na yankin, kamar ƙasashen Isra'ila da Bahrain da Kuwait da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Jordan da Saudiyya da tsibirin Cyprus, har ma da jiragen dakon man fetur da ke ratsawa ta mashigar Hormuz.

Haka nan ma ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran da ke a Lebanon ta shiga faɗan, inda ta harba rokoki zuwa cikin Isra'ila daga sansanoninta da ke cikin Lebanon.

Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan cibiyoyin Hezbollah a Lebanon.

Me ya sa Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran hari?

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce manufarsu ita ce "domin tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba."

"Za mu lalata makamansu da ƙona masana'antun haɗa makamansu da ke ƙarƙashin ƙasa. Wannan masana'anta sai an wayi gari babu ita,'' kamar yadda ya bayyana cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar.

Ya kuma gargaɗi gargaɗi dakarun Iran su ajiye makamansu domin samun "kariya" ko kuma su fuskanci mutuwa.

Trump ya buƙaci al'ummar Iran su tsara kansu da kyau ta yadda za su kifar da gwamnati, inda ya ce: "Idan mun gama ku ƙwace gwamnatinku. Wannan gwamnati za ta zama taku. Zai iya yiwuwa wannan ce dama ɗaya tal da za ku iya samu."

Wannan aikin soji da Amurka ta ƙaddamar, wanda ta yi wa laƙabi "Operation Epic Fury" ya zo ne bayan tsawon makonni Trump na barazanar ƙaddamar da yaƙi kan Iran idan ta ƙi amincewa da sabuwar yarjejeniyar nukiliya.

Iran ta sha nanata cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne.

Cibiyar tsara aikin sojin Amurka ta ce manufarta ita ce "lalata tsarin tsaron gwamnatin Iran, ta hanyar zaɓen wurare da suka fi zama barazana."

Daga farko, firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Amurka da Isra'ila sun ƙaddamar da "shirin kawar da abin da ke barazana ga wanzuwar ƙasarsa".

Iran ta bayyana harin da aka kai mata a matsayin "takalar faɗa kuma wanda ya saɓa wa doka" kuma ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare a faɗin yankin.

Yadda Iran ta mayar da martani

Ira ta jefa makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa zuwa Isra'ila, da wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya wadanda ke da alaƙa da Amurka, da wani sansanin sojin Birtaniya da ke Cyprus da kuma jiragen ruwa da ke ratsawa ta bakin iyakar Iran.

Dakarun juyin juya hali sun sanar cewa sun kai farmaki a kan cibiyoyin gwamnari da na soji a birnin Tel Aviv da sauran wurare. Haka nan kuma an kai hari a wani ynaki na fararen hul a Beit Shemesh, lamarin da ya kashe mutum 9.

Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta sanar cewa wani jirgi maras matuƙi fa kai hari kan sansaninta da ke Akrontiri, da ke Cyprus. Sai dai babu wanda aka kashe ko ya ji rauni a harin, amma duk da haka ma'aikatar ta ce an kwashe wasu mutane daga sansanin.

Haka nan Iran ta kai hari kan ƙasashen Qatar, Bahrain, Jordan, Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa, waɗanda dukkaninsu suna da sansanin sojin Amurka a cikinsu, haka nan ma Iran ɗin ta kai hari kan ƙasashen Oman da kuma Saudiyya.

Amurka da ƙasashen yankin Gulf duk sun yi Allah-wadai da hare-haren da Iran ɗin ta kai wa ƙasashen Gulf.

An kakkaɓo wasu jiragen yaƙin Amurka a Kuwait, ranar Litinin, wanda Amurka ta bayyana a matsayin kuskure ne daga abokan ƙawance.

Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da mutuwar sojojinta shidda a yaƙin.

Yaushe yaƙin zai ƙare?

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce hare-haren da ake kaiwa a Iran "za su ci gaba ba tare da ƙaƙƙautawa ba a tsawon mako," amma daga baya ya nuna alamar cewa abin zai iya ci gaba.

A ranar Lahadi Trump ya faɗa wa jaridar New York Times cewa Amurka da Isra'ila za su iya ci gaba da ƙaddamar da hare-haren tsawon mako huɗu zuwa biyar.

"Da farko muna tunanin a kai mako huɗu zuwa biyar, amma za mu iya ci gaba har fiye da hakan," kamar yadda Trump ya faɗi a fadar White House ranar Litinin.

Haka nan a ranar Asabar, firaiministan Isra'ila Benja,min Netanyahu: "Za mu ci gaba da wannan yaƙi har zuwa lokacin da ya kamata."

Ya zuwa yanzu an soke dubban tashin jirage a yankin, wannan ne lokacin da aka fi fuskantar irin haka tun bayan annobar korona.

Kamfanin sufurin jiragen sama na Emirates da ke Hadaddiyar Daular Larabawa ya dakatar da zirga-zirga na wani ɗan lokaci, sai dai kamfanin ya ce zai ci gaba da "ƙwarya-ƙwaryar sufuri daga ranar Litinin.

Filin jirgin sama na Dubai ya sanar da “sake ci gaba da aiki rabi da rabi” daga daren ranar Litinin.

Jirage sun rika tashi daga birnin Doha amma ba sa sauka, kasancewar Qatar ta rufe sararin samaniyarta.

Kamfanin sufuri na Virgin Atlantic ya soke tafiyarsa guda biyu zuwa birnin London a ranar Litinin, daya daga Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, daya kuma daga Riyad na Saudiyya. Sauran jiragen kuma an sauya musu wurin sauka.

Kamfanin sufuri na British Airways ya soke safara zuwa birnin Tel Aviv da Bahrain sannan ya ce “yana lura da abin da ke faruwa a koda yaushe.”

Kafar yada labarai ta gwamnatin Kuwait ta ce hukumar sufurin jirgin sama ta kasar ta sanar da dakatar da sufurin jirgin sama zuwa Iran har sai yanda hali ya yi.