Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
China da Rasha: Me ya sa ƙawayen Iran ba su kai mata ɗauki ba?
- Marubuci, Global Journalism team, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
Bayan Birtaniya ta amince Amurka ta yi amfani da sansanin sojin samanta a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran, kallo ya fara komawa kan irin tallafi ko goyon bayan da Tehran za ta samu daga ƙawayenta na ƙasashen waje.
Ana dai ganin Rasha da China a matsayin ƙasashe biyu da suke da alaƙa mai kyau ta kasuwanci da diflomasiyya da ma tsaro da Iran, amma yanayin rikicin ne zai iya tantance irin yadda ƙasashen biyu masu ƙarfi za su iya takawa.
Abin da aka yi tsammani daga Rasha
Wakilin BBC a Rasha, Sergei Goryashko ya ce Moscow na taka-tsantsan ne domin gujewa faɗawa cikin yaƙin gadan-gadan.
Kakakin fadar gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov ya bayyana takaicin ƙasar kan ta'azzarar yaƙin, inda ya ce duk da cewa an fara fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran, sai da "matsalar ta rincaɓe."
Ya ƙara da cewa Moscow na yawan tattaunawa da shugabannin Iran da ma sauran ƙasashen yankin Gulf da yaƙin ya shafa.
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta yi Allah-wadai da abin da ta kira "hare-haren da ba su dace ba" a Iran da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar, sannan ta soki abin da ta bayyana da kisan gillar siyasa da "farautar" shugabannin ƙasashe masu ƴanci.
A ranar Lahadi, Shugaba Vladimir Putin ya aike da saƙon jajensa ga Shugaban Iran Masoud Pezeshkian bisa kisan Jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, lamarin da ya bayyana da "tsantsar tauye ƴancin ɗan'adam da yi wa dokokin ƙasa da ƙsa karan tsaye."
Sai dai duk da haka, Rasha ba ta fito ƙarara ta soki Shugaban Amurka Donald Trump ba, kuma ta ci gaba da godiya ga ƙoƙarin Amurka wajen sa baki a yaƙin Ukraine.
Da aka tambaya Peskov kan yadda Rasha za ta aminta da Amurka, sai ya ce, "ita Rasha da kanta kawai ta yarda, sannan muradunta kawai take karewa."
Waɗannan muradun na ƙashin kan ne wataƙila suka sa har yanzu taimakon Rasha a Iran ya zama tamkar a teburin mai shayi, duk da kasancewar Iran ta taimaka wa Rasha matuƙar gaske a yaƙinta da Ukraine, inda ta riƙa ba ta gudunmuwar jirage marasa matuƙa da sauransu, kamar yadda wakilanmu ya ruwaito.
Haka kuma Rasha ta bayyana a baya cewa ba za ta iya sadaukar da abubuwa sosai ba domin ƙawarta, misali abin da aka gani a Venezuela da Syria ko kuma a lokacin da aka yi yaƙin kwana 12 tsakanin Isra'ila da Iran a shekarar 2025.
Yarjejeniyar Rasha da Iran da aka shiga a ranar 17 ga watan Janairun 2025 ya ƙunshi raba bayanai da haɗakar tsaro "domin tabbatar da tsaron yankin" amma babu inda suka amince su kai wa juna agaji a lokacin da ɗaye ke cikin yaƙi.
Haka kuma alaƙar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu ba wata babba ba ce, inda kasuwancin da ke tsakaninsu bai haura dala biliyan huɗu zuwa dala biliyan biyar ba.
Iran ta karɓi jiragen horo na Yak-130 da helikwaftocin Mi-28, sannan suna sa ran samun jiragen yaƙi na Su-35, amma har yanzu Rasha ba ta amince ta ba ta makaman tsaron sararin samaniya na Verba ba.
Jirage marasa matuƙa na Shahed na Iran sun taimaka wa Rasha matuƙa a yaƙinta da Ukraine, amma daga bara sai Moscow ta ƙara ƙaimi wajen haɗa jiragenta marasa matuƙa masu yawa, wanda hakan ya sa ta rage dogaro da jiragen na Iran.
Sai dai duk da haka, a wajen Moscow, Iran na da matuƙar muhimmancin da ba za ta so ta bari ta dusƙushe ba, amma kuma ba ta da muhimmancin da za ta shigar mata yaƙi gadan-gadan. Duk da cewa komai zai iya canjawa a gaba, amma dai a yanzu taimakon Rasha zai kasance a baki ne kawai.
China ta fi taka rawa a tattalin arziki
China ta yi matuƙar Allah-wadai da kisan Ayatollah Ali Khamenei, sannan dama can Beijing ta daɗe tana sukar matakin Amurka na canja shugabanni a ƙasashen duniya.
Daga ciki manyan abubuwan da ke ƙunshe a alaƙar China da Iran akwai alaƙar kasuwanci, kamar yadda wakilin BBC Shawan Yuan na China ya bayyana. China ce babbar ƙawar kasuwancin Iran, musamman a ɓangaren makamashi.
Duk da shekarun da Iran ta yi a ƙarƙashin takunkuman Amurka, Beijing ce ta kasance gaba-gaba wajen ƙarfafa tattalin arzikin Iran wajen sayen man fetur ta bayan fage.
A 2025 misali, China ce ta saya sama da kashi 80 na man fetur da Iran ta sayar, sannan kuɗin shiga da ta samu daga kasuwancin man fetur ɗin ya taimaka wajen inganta tattalin arzikinta da kuma samun kuɗin saye da ƙera makamai.
Yejejeniyar kasuwanci na shekara 25 da ƙasashen biyu suka shiga a 2021 ne ya ƙara inganta alaƙar da ke tsakanin ƙasashen, inda China ta yi alƙawarin zuba jarin biliyoyi a ɓangaren ababen more rayuwa da sadarwa a Iran.
Irin rawar China a baya
A tarihi, yawanci rawar da China ke takawa a duk lokacin da aka samu tashin-tashina tsakanin Iran da Isra'ila ko Iran da Amurka na kasancewa ne cikin hikima da taka-tsantsan.
A lokutan baya, ciki har da yaƙin kwana 12 da aka gwabza tsakanin Iran da Isra'ila a 2025, China kira ta yi a tsagaita wuta, sannan ta zargi "wata ƙasar waje da rura rikicin," wanda nuni take ga tsare-tsaren Amurka, kamar yadda wakilinmu na ruwaito.
A rikice-rikicen Iran da Isra'ila na baya, China ta kasance garkuwa ta diflomasiyya ga Iran ta hanyar amfani da ƙarfinta na hawa kujerar naƙi ko kuma barazanar amfani da ƙarfin wajen rage matakan Majalisar Ɗinkin Duniya. Amma duk da haka, China ba ta taɓa bayar da agajin soji kai-tsaye ba.
Idan aka samu gwamnati mai goyon bayan ƙasashen yamma a ƙasar Iran, hakan zai zama babbar barazana ga China, domin ba makamashi kaɗai Tehran ke ba ta ba, har ma da taimaka mata wajen rage ƙarfin Amurka a yankin Larabawa.
Idan gwamnatin Iran ta samu matsala, hakan zai raunana yunƙurin faɗaɗa iko da Moscow da Beijing suka daɗe suna hanƙoro.
Yanzu dai Beijing za ta cigaba da taka rawarta ne daga gefe, ta hanyar ƙoƙarin ɗasawa da duk wanda ya maye gurbin Khamenei a matsayin jagoran addinin ƙasar, sannan ita ma Rasha za ta nemo wasu hanyoyin cigaba da ɗasawa da ƙasar.