Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 03/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 3 ga watan Maris 2026.

Taƙaitattu

  • Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
  • Ƴan shi'a sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan Iran a Legas
  • Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari kan ofishin shugaban ƙasar Iran
  • Iran na ci gaba da luguden wuta kan Isra'ila da sansanonin sojin Amurka
  • Yawan sojojin Amurka da aka kashe a yaƙin Iran ya kai 6
  • An kai hari kan ofishin jakadancin Amurka a Saudiyya
  • Hezbollah ta ce ta kai hari kan sansanonin sojin Isra'ila uku
  • Farashin gas na ci gaba da tashi sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya
  • Mutum shida da za su iya maye gurbin Ayatollah Ali Khamenei

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Abdullahi Bello Diginza

  1. Gwamnatina ba za ta lamunci rashawa ba - Ahmed Aliyu

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya "gargaɗi" manyan ma'aikatan gwamnatin jihar game da rashawa, tare da bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba.

    Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na gwamnan jihar Abubakar Bawa ya fitar, ta ce gwamnan ya yi wannan bayani ne sa'ilin taron buɗe-baki da manyan sakatarori da shugabannin ma'aikatu da kuma daraktocin gwamnatin jihar a ranar Litinin.

    Aliyu ya ce "a matsayinku na shugabanni a ma'aikatunku, wajibi ne ku rungumi ɗabi'ar kaffa-kaffa da adalci a kan duk wata hulɗa."

    Sanarwar ta kuma ja hankalin ma'aikata kan zuwa aiki latti da kuma ƙin zuwa aikin baki ɗaya.

    Ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakan inganta walwalar ma'aikata, saboda haka ya kamata su ma, su saka mata ta hanyar mayar da hankali wajen aiki.

  2. Yadda yaƙin Iran zai shafi farashin man fetur a Najeriya da duniya

    Yaƙi na ci gaba da rincaɓewa tsakanin Iran da Amurka da kuma Isra'ila tun bayan kisan jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei.

    Yayin da Isra'ila da Amurka ke ci gaba da kai wa Iran hari a biranenta, Iran ta matsa ƙaimi wajen kai hare-hare kan duk wata kadarar Amurka da wasu cibiyoyin makamashi a yankin Gabas ta tsakiya.

    Wani abu da ake ganin wannan yaƙi zai shafa shi ne fannin makamashi.

    Farashin gangar man fetur ya tashi da ƙarin kashi 4% yayin da rikicin ke ci gaba da ƙazancewa a Gabas ta Tsakiya.

    A ranar Talata an riƙa sayar da gangan man fetur ɗaya kan dala 80, wanda shi ne farashi mafi tsada daga farkon wannan shekara.

    Iran ta datse mashigar Hormuz - wanda wata ƙaramar mashiga ce da ake bi wajen safarar man fetur, wadda ta haɗa yankin Gulf da tekun Indiya.

  3. Yadda ake takun-saƙa tsakanin El-Rufai da ICPC

    Dambarwa ta kaure tsakanin hukumar ICPC mai yaƙi da almundaha a Najeriya da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

    Sa-in-sar ta ɓarke ne bayan da a ranar Litinin hukumar ta shigar da shi ƙara gaban babbar kotun tarayya da Abuja.

    Tun a ranar 19 ga watan Fabrairun da ya gabata ne hukumar ta tabbatar da cewa El-Rufai na hannunta, bayan da ta kama shi, jim kaɗan bayan hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sallame shi daga gayyatar da ta yi masa.

    Tun da farko hukumar ta gayyace shi domin amsa wasu tambayoyin da ta ce tana son samun amsarsu daga gare shi.

    Bayan tsare shi hukumar ta kuma kai samame gidansa da ke Abuja, domin gudanar da bincike a ciki, kamar yadda Muyiwa Adekeye, kakakin yaɗa labaran El-Rufai ya bayyana a shafinsa na X.

    Cikin wata hira da El-Rufai ya yi da gidan talbijin na Arise gabanin kama shi ya yi iƙirarin satar jin wayar babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu.

  4. Tafiye-tafiye ta jirgin sama na funkantar cikas a ƙasashen Gabas ta Tsakiya

    Tafiye-tafiye ta jirgin sama sun funkanci cikas a yawancin ƙasashen Gabas ta Tsakiya, sakamakon rikicin da ake yi a yankin.

    A wani ɓangaren, jiragen Emirates daga Daular Larabawa sun fara tashi.

    Wasu jiragen sun tashi daga kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da Italiya da Switzerland, amma an soke tashin jirage da dama.

    Amurka da Isra'ila dai na ci gaba da kai munanan hare-hare a Iran

    Zai yi wuya a san ainahin abin da ke faruwa a Iran, sakamakon rashin sadarwar intanet.

    Amma mutanen da suka samu dama sun bayyana halin da ake ciki wanda ya fi kamari a birnin Isfahan da cibiyar makamin nukiliyar Iran ke ciki.

  5. An buɗe iyakar Gaza karon farko bayan hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran

    Isra’ila ta ce ta buɗe babbar hanyar da ke shiga Gaza, wadda take da muhimmanci wajen shigar da kayan agaji a karon farko tun bayan da ta kai hare-haren jiragen sama kan Iran.

    Majiyoyi daga Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin agaji sun yi gargaɗi cewa rufe hanyoyin shiga ne ya sa kayan abincion da mai ke ƙarewa a Gaza.

    Wannan ya sa mutane sun fara siyan kaya cikin hanzari, abin da ya sa farashin kaya ya tashi a kasuwannin cikin gida.

    Hukumar tsaron Isra’ila, Cogat, wadda ke kula da hanyoyin shiga, ta bayyana cewa an rufe iyakar Kerem Shalom ne saboda “barazanar harin makami” da ke da haɗari ga ma’aikatan Isra’ila da na Falasɗinu.

    Majiyoyi a Gaza sun shaida wa BBC cewa an tura motocin agaji zuwa Kerem Shalom da safe amma har yanzu ba su dawo da kaya ba.

    A wani ɓangare kuma, har yanzu mashigar Rafah da ke zuwa ƙasar Misira wadda ake amfani da ita wajen fitar da marasa lafiya a rufe take.

  6. Spain ta hana Amurka amfani da filin jirginta domin kai wa Iran hari

    Wasu jiragen sojin Amurka sun bar sansanonin Rota da Morón da ke kudancin ƙasar Spain bayan gwamnatin Spain ta ƙi bai wa Washington izinin amfani da wuraren domin kai hari kan Iran.

    Ministan harkokin wajen Spain, José Manuel Albares, ya ce ƙasarsa ba za ta amince a yi amfani da ƙasarta ba ga “duk wani abu da bai yi daidai da ƙundin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya ba".

    Matakin ya sa Spain ta saɓa wa ra’ayin wasu ƙawayenta na Turai.

    Sai dai babban sakataren ƙungiyar tsaron ƙasashen yammacin duniya ta NATO, Mark Rutte, ya shaida wa BBC cewa Turai “na goyon bayan harin Amurka a Iran.”

    Duk da haka, firaministan Spain, Pedro Sánchez, ya soki matakin da Amurka da Isra’ila suka ɗauka kan Iran.

  7. Dangote ya ƙara farashin man fetur

    Matatar man Dangote ta ƙara farashin man fetur daga naira 774 zuwa naira 874 kan kowacce lita, lamarin da ya haifar da damuwa game da yiwuwar tashin farashin fetur a faɗin Najeriya.

    Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wani babban jami’in matatar ya tabbatar da sabon farashin a ranar Litinin, inda ya ce an ɗauki matakin ne saboda rashin tabbas da hauhawar farashin man a kasuwannin duniya sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.

    Binciken petroleumprice.ng ya nuna cewa an riga an fara amfani da sabon farashin, wanda zai iya shafar dillalan sayarwa da kuma masu amfani da fetur a ƙasar baki ɗaya.

    Ƙarin farashin ya biyo bayan dakatarwar da matatar ta yi kan lodin fetur daga karfe 12 na dare a ranar 2 ga Maris, 2026, sakamakon farashin mai a duniya da ya wuce dala 80 a kan kowacce ganga cikin dare ɗaya.

    Masu sayar da fetur a kasuwannin unguwanni sun bayyana fargaba cewa wannan ƙaruwa na iya kawo ƙarancin mai a wasu wurare, musamman a lokutan da ake da yawan buƙata, inda wasu ke ganin cewa hakan na iya ƙara matsaloli ga masu amfani da motoci da kamfanonin sufuri a Najeriya.

    Haka zalika, masana tattalin arziki sun yi gargadi cewa ƙarin farashin zai iya janyo hauhawar wasu kayan more rayuwa, wanda zai ƙara tsananta halin tattalin arziki ga talakawa da 'yan kasuwa a ƙasar.

  8. Ƴan shi'a sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan Iran a Legas

    Ƴan Shi'a a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Jihar Legas, da ke kudu maso yammacin Najeriya, domin yin allawadai da kisan jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran.

    Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa masu zanga-zangar sun ratsa wasu sassan yankin Maryland, ɗauke da alluna da tutoci, suna allawadai da abin da suka kira mamaye Iran da kuma kisan gilla kan jagoranta wanda ya daɗe yana mulki.

    An kashe Ayatollah Ali Khamenei ne a safiyar Asabar 28 ga Fabrairu a hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai tare da wasu manyan jami’an gwamnatin Iran.

    Zanga-zangar ta Legas na zuwa ne bayan irin zanga-zangar da mabiya Shi’ar suka gudanar a jihohin Kano da Yobe da Gombe da Bauchi a ranar Lahadi.

  9. Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai hari kan ofishin shugaban ƙasar Iran

    Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa sojojinta sun kai hari kan ofishin shugabancin ƙasar Iran.

    A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Telegram, rundunar ta ce an jefa “makamai da dama” a kan Ofishin Shugaban da majalisar tsaron ƙasar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa an kai harin ne kan wata cibiyar horon soji da “ƙarin muhimman gine-ginen shugabancin ƙasar.”

    Rundunar ta ce tsohon jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei wata sa'in yana amfani da ofishin shugaban ƙasar.

    An kashe jagoran addinin ne a hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kai kan Iran a ƙarshen makon da ya gabata.

  10. Hezbollah ta ce ta kai hari kan sansanonin sojin Isra'ila uku

    Ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran ta bayyana cewa ta kai hari kan sansanonin sojin Isra'ila uku a matsayin martani ga barnar da harin Isra’ila ta yi wanda ya shafi garuruwa da ƙauyuka da dama a Lebanon.”

    A cikin saƙonni guda uku da ta wallafa a shafin Telegram, Hezbollah ta ce ta harbi sansanin Nafah dake kan tsaunukan Golan da “manyan roka,” sannan ta kuma kai hari kan sansanonin jiragen sama na Meron da Ramat David, a arewacin Isra’ila da jirage marasa matuƙa.

    Isra’ila ba ta yi wani bayani ba game da harin da Hezbollah ta ce ta kai mata.

  11. Farashin gas na ci gaba da tashi sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya

    Farashin gas a kasuwannin Turai na ci gaba da hauhawa sakamakon rikicin da ke ƙara kamari a Gabas ta Tsakiya.

    Ma’aunin farashin gas na Turai ya tashi da kashi 33 cikin ɗari, yayin da na Birtaniya ya ƙaru da kashi 30 cikin ɗari.

    Duka ɓangarorin biyu na cinikayya a matakan da ba a taɓa gani ba tun watan Janairun shekarar 2023.

    A ranar Litinin farashin gas ya tashi da kusan kashi 50 cikin ɗari bayan kamfanin QatarEnergy, wanda ke cikin manyan masu fitar da gas a duniya, ya dakatar da samarwa sakamakon abin da ya kira hare-haren soji kan wasu wurarensa.

    A cewar kamfanin Trading Economics, Birtaniya na cikin mawuyacin hali musamman saboda ƙarancin wuraren adana gas da take da su, da kuma dogaro mai yawa kan shigo da shi daga waje.

    Rahoton ya nuna cewa adadin gas da ke ajiye a cikin ƙasar bai wuce kashi 30 cikin ɗari ba zuwa ƙarshen watan Fabrairu.

  12. Isra'ila ta kai hari kan hukumar yaɗa labaran Iran

    Shugaban kafar yaɗa labarai ta Iran IRIB, Peyman Jebeli, ya ce an kai hari kan wasu sassan harabar ofisoshin hukumar da ke birnin Tehran, lamarin da ya janyo ɓarna a wasu sassan gine-gine yayin da rundunar sojin Isra’ila ta kuma tabbatar da cewa ta kai hari kan IRIB ɗin.

    A wani saƙo da rundunar ta wallafa a shafinta na harshen Farisa a dandalin X, ta ce ta kai hari kan abin da ta kira “kafar yaɗa ƙarya da danniya” ta rundunar kare juyin juya halin Iran.

    Kafofin yaɗa labarai na Iran sun ruwaito a jiya cewa wasu gine-ginen gidan talabijin na gwamnati sun fuskanci hari.

    Wannan ba shi ne karon farko ba da aka kai hari kan kafar yaɗa labaran Iran domin an taɓa kai mata hari a lokacin yaƙin kwanaki goma sha biyu tsakanin Iran da Isra’ila a watan Yunin shekarar da ta gabata.

  13. Trump ya soki firaiministan Birtaniya kan 'rashin taimaka' wa Amurka

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki firaiministan Birtaniya, Keir Starmer, kan abin da ya kira rashin taimaka wa Amurka a hare-haren da ta kai kan Iran.

    A wata hira ta wayar tarho da jaridar The Sun, Trump ya ce Starmer “bai taimaka ba. Ban taɓa tunanin zan ga hakan ba. Ban taba tunanin zan ga hakan daga Birtaniya ba.”

    Ya kara da cewa wannan abin takaici ne ganin dangantakar ƙasashen biyu.

    A ranar Litinin, Starmer ya shaida wa majalisar dokokin Birtaniya cewa gwamnatinsa “ba ta goyon bayan sauya mulki ta hanyar hare-hare ba."

    Da farko dai Birtaniya ba ta amince Amurka ta yi amfani da sansanoninta wajen kai hari kan Iran ba, amma daga baya ta buɗe sansanonin nata domin abin da ta kira hare-haren kariya kan wasu wurare a Iran.

    Trump ya kuma ce Faransa ta nuna goyon baya sosai, yana mai cewa, “Faransa ta yi abin kirki.

    Sauran ma sun yi abin kirki. Amma Birtaniya ta bambanta da sauran.”

  14. Muna da isassun makaman yaƙi 'har abada' - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na da isassun makaman yaƙi da za a iya amfani da su “har abada”, yana mai jaddada cewa Amurka a shirye take ta yi nasara a duk wani rikici.

    Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta na Truth Social, inda ya yi magana kan abin da ya kira tarin makaman da Amurka ke da su.

    Ya rubuta cewa, ana iya gudanar da yaƙe-yaƙe na dogon lokaci ta amfani da irin waɗannan makamai kaɗai.

    Ya kuma ƙara da cewa, “Amurka na da tarin makamai marasa iyaka, kuma a shirye take ta yi nasara babba,”.

    Trump ya kuma zargi tsohon shugaban ƙasar, Joe Biden, da bai wa Ukraine makaman Amurka masu matuƙar ƙarfi da yawa.

    A ƙarshen wa’adin mulkinsa na shekara huɗu, Biden ya amince Ukraine ta yi amfani da makamai masu linzami na dogon zango irin su ATACMS, waɗanda ke iya kai hari har nisan mil 190, kimanin kilomita 300.

  15. Harin Iran ya lalata sansanin sojin saman Amurka a Bahrain

    Rahotanni na cewa wani hari da Iran ta kai ya lalata babban sansanin sojin saman Amurka da ke ƙasar Bahrain.

    Hotuna da bidiyo da kamfanin dillancin labarai na Fars News Agency, wanda ke da alaƙa da dakarun juin juya halin Iran IRGC ya wallafa, sun nuna abin da ya yi kama da jerin makamai masu linzami na faɗowa kan wasu wurare daga nesa tare da fashewa.

    Rahoton ya yi iƙirarin cewa harin jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami na IRGC ya lalata wani ginin da ma’aikatar Amurka a yankin Sheikh Isa na Bahrain, tare da haddasa fashewar tankunan mai.

    Har zuwa yanzu, Amurka ba ta fitar da wata sanarwa kan waɗannan rahotanni ba.

    A baya dai an ga hayaƙi na tashi daga wani sansanin sojan ruwa da Amurka ke gudanarwa a Bahrain.

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ba ‘yan ƙasarta umarnin su fice daga Bahrain nan take, tare da wasu ƙasashe kusan goma sha biyu a yankin Gabas ta Tsakiya, saboda matsalar tsaro da ke ƙara kamari.

  16. An kai hari kan ofishin jakadancin Amurka a Saudiyya

    Ma’aikatar Tsaron Saudiyya ta tabbatar da cewa an kai hari kan ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Riyadh da jiragen sama marasa matuƙa guda biyu, lamarin da ya haddasa wata ƙaramar gobara da kuma lalacewar kayayyaki kaɗan a ginin.

    A cikin sanarwar da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X, ta ce bisa ƙiyasin farko, harin bai yi sanadiyyar asarar rai ba, amma ya janyo ɓarnar da ba ta wuce iyaka ba a cikin ginin.

    A nasa bangaren, ofishin jakadancin Amurka a Saudiyya ya fitar da umarnin kowa ya zauna a inda yake ga ma’aikatansa da ke biranen Jeddah da Dhahran tare da Riyadh.

    Haka kuma ya bayyana cewa zai takaita duk wata tafiya da ba ta zama dole ba zuwa sansanonin soji a yankin.

  17. Iran na ci gaba da luguden wuta kan Isra'ila da sansanonin sojin Amurka

    Iran na ci gaba da yin luguden wuta kan Israila da sansanonin sojin Amurka a ƙasashen gabas ta tsakiya.

    Saudiyya ta ce wasu jirage marasa matuƙa biyu na Iran din sun kai hari kan Ofishin Jakadancin Amurka da ke babban birnin ƙasar, Riyadh.

    Ma’aikatar tsaron ƙasar ta ce ta samu nasarar kakkaɓo wasu jirage marasa matuƙa guda takwas da ke kan hanyarsu ta zuwa babban birnin, da kuma birnin Al-Kharj da ke kusa.

    Ofishin Jakadancin Amurka ya bai wa ‘yan ƙasarsa da ke zaune a masarautar shawarar su nemi mafaka a inda suke.

    Ƙasashen Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Isra’ila su ma sun bayar da rahoton cewa makamai masu linzami na ta yawo a sararin samaniyarsu.

    Yanzu haka Amurka ta bukaci yan kasarta da ke zaune a kasashe goma sha biyu na yankin su fice cikin gaggawa.

  18. Yawan sojojin Amurka da aka kashe a yaƙin Iran ya kai 6

    Rundunar sojin Amurka ta tsakiya, wato Centcom ta ce adadin sojojin Amurka da suka mutu a yaƙin Iran ya kai shida.

    A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa sojojinta sun gano gawarwakin wasu sojoji biyu da a baya ba a san inda suke ba, daga wani gini da aka kai wa hari a farkon luguden wutar da Iran ta soma kai wa a yankin.

    Sanarwar ta kara da cewa yaƙi na ci gaba da gudana, duk da asarar da aka samu.

    Rundunar ba ta yi ƙarin bayani kan inda harin ya fi ƙamari ba ko kuma ko akwai ƙarin sojojin da suka jikkata.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke kara tsananta a yankin ƙasashen gabas ta tsakiya inda ake ci gaba da musayar wuta tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran

  19. Mutum shida da za su iya maye gurbin Ayatollah Ali Khamenei

    Kamar yadda kundin tsarin mulkin Iran ya tanada, Majalisar Masana ta ƙasar – wadda ta ƙunshi manyan malaman addini 88 – ce za ta zaɓi mutumin da zai zamo sabon jagoran addinin ƙasar.

    Ana zaɓen wakilan majalisar malaman Iran ne a duk shekara takwas, kuma dole ne sai Majalisar Magabata ta ƙasar ta tantance su.

    Masu goyon bayan Ali Khamenei ne suka lashe dukkanin kujerun majalisar a zaben shekara ta 2024, inda daga baya aka samu giɓi a kujeru huɗu bayan mutuwar wakilansu – cikin har da Ebrahim Raisi, waɗanda za a cike gurbinsu a zaɓen cike gurbi da za a yi a watan Mayun 2026.

    Sashe na 111 na kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi cewa a samar da wata majalisa ta mutum uku ta wucin-gadi, wadda za ta gudanar da al'amuran ƙasar kafin zaɓen sabon jagoran addini.

    Kwamitin riƙon-ƙarywar zai ƙunshi shugaban ƙasa Massoud Pezeshkian, da babban alƙalin alƙalan ƙasar Gholamhossein Mohseni Ejei da kuma malami masanin shari'a guda ɗaya daga Majalisar Magabata ta ƙasar.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.