Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace irin alaka ce tsakanin Amurka da Isra'ila?
isr’ila da Amurka sun hada kai wajen kaddamar da hare-hare kan Iran, kuma a yanzu haka yaki ya kaure tsakanin kasashen uku.
Yayin da ita kuma Iran a nata bangaren ta ke kai hare-haren ramuwa kan kasashen yankin Gulf, wadanda ke da sansanonin sojin Amurka.
Amurka dai a yanzu za a iya cewa ita ce kan gaba a cikin kasashen duniya masu karfin fada a ji, musamman a bangaren karfin soji da siyasa, wanda hakan ya sa take iya juya akalar diflomasiyyar kasashe.
Sai dai yadda Isra'ila ta zama 'yar lelen kasar ta Amurka, sai ya sa wasu ke tunanin ta fara zama tamkar ita ce ma uwargijiya, saboda ana ganin tamkar tana juya Amurka ne yadda take so tamkar waina a tanda.
Yadda Amurka ta dage wajen kai hare-hare babu ƙaƙƙautawa a wannan yaƙin a Iran ya taimaka wajen ƙara fahimtar yanayin ƙarfin alaƙar da ke tsakanin Isra'ila da Amurka.
Tun da aka fara yaƙin, an fi jin amon Amurka sama da Iran ɗin, wadda asali yaƙinta ne, inda yanzu ake kallon yaƙin a matsayin wanda Amurka da Isra'ila ke gwabzawa da Iran.
'Alaka ce mai girma'
Farfesa Tukur Abdulƙadir malami a jami'ar jihar Kaduna, KASU kuma mai nazarin kimiyyar siyasa da diflomasiyya ya ce suna da alaka mai girma da ta dade kuma ta rika habaka na tsawon lokaci.
Sai dai masanin ya ce duk da cewa kasashen biyu na da alaka mai kyau, Amurka ta ba taka rawar gani ba wajen tabbatar da ginawa da wanzuwar kasar Isra'ila, sai daga bisani ne ta dauka ta daura.
''Akwai dalilai da yawa da suka sa suke da alaka mai kyau. Kafin kafa kasar Isra'ila, kusan Amurka ba ta taka wata rawa ba wajen gina kasar, musamman a bangaren wajen goyon baya ko wanzuwarta,'' in ji shi.
Ya ce Amurka ta fara alaka mai karfi ne da Isra'ila a lokacin kololuwar yakin cacar-baki.
''Tun bayan yakin Larabawa da Isra'la a 1948, sai aka fara ganin goyon bayan Amurka ga Isra'ila. Daga 1973 ne za a iya cewa taimako da goyon bayan Amurka a Isra'ila ya fito fili karara. A yanzu babu kasar da ke amfana da Amurka kamar Israila a duniya,'' in ji Farfesa Tukur.
Yaya alaƙar take?
A game da ribar da Amurka za ta samu daga alakar kasashen biyu, Farfesa Tukur ya ce akwai daure kai matuka kan asalin ribar da Washington za ta samu daga taimaka wa kasar Isra'ila.
Sai dai ya ce akwai kungiyoyin duniya manya na Yahudawa masu karfin fada a ji a Amurka da suke da tasiri matuka a tattalin arzikin kasar, kuma suke da karfi a kafofin watsa labarai.
''Akwai kungiyoyi da dama, akwai manya irin su EPAC, wadanda kungiyoyi ne na Yahudawa, kuma suna da kudi sosai da karfi, sannan suna amfani da kafofin sadarwa na ciki da wajen Amurka da kuma harkokin kasuwancinsu domin marawa da goyon bayan Isra'ila,'' in ji shi.
Tukur Abdulqadir ya ce ko tsohon Shugaban Amurka Barrack Obama, a cewar masanin ba sa dasawa sosai da Benjamin Netanyahu, shi ma yana matukar girmama muradun Isra'ila.
''Obama ya bayyana cewa alaƙar da ke tsakanin Amurka da Isra'ila alaƙa ce wadda ba za ta yanku ba. Sannan shi ma tsohon shugaban ƙasar, Joe Biden ya ce tsaron Isra'ila tsaron Amurka ne."
Farfesa Tukur ya ce Biden ya yi alwashin kare muradu da tsaron Isra'ila, "domin ya bayyana cewa tsaron Isra'ila na cikin ginshiƙan muradun harkokin ƙasashen wajen Amurka, sannan ya ce duk abin da zai taɓa tsaron Isra'ila, zai taɓa tsaron Amurka," kamar yadda masanin ya bayyana.
Sai dai a lokuta da dama, an yi amannar ana ƙulla alaƙa ne tsakanin ƙasashe biyu ta hanyar shiga yarjejeniyar da kowane ɓangare zai amfana.
Domin jin irin ribar da Amurka za ta samu, Farfesa Tukur ya ce akwai wahalar fahimta.
Farfesa Tukur ya ce akwai masu ganin Amurka na shiga cikin harkokin Isra'ila ta yi dumu-dumu a ciki, ko da kuwa babu wani alfanu da ƙasar za ta samu.
”Sai dai kuma wani lokaci hakan na nuna irin karfin soji da Amurka take da shi a duniya, yadda ta baza kayan yakinta a kusan ko ina, kuma za ta iya kai hari kan kowace kasa cikin kankanin lokaci”.
''Abin tambayar a yanzu shi ne shin wace irin alaƙar ce a tsakanin Larabawa da Amurka, sannan wace iri ce a tsakanin Amurka da Isra'ila. Za a iya cewa Larabawa sun zama tamkar bayi ne ga Amurka, amma Isra'ila ta zama tamkar uwargiiya ga Amurka."
Ya ce akwai Amurkawa da suke bayyana rashin jin daɗinsu kan yanayin yadda Donald Trump yake tafiyar da mulki.
''Da dama na cewa sun zaɓe shi ne kan cewa zai barranta da abubuwan da Jam'iyyar Democrats ke yi, da ƙiyayyarsa da yaƙi da yadda yake fitita muradun Amurka."
Kafin zaɓen, ƴan ƙasar sun kasance suna yabon yadda yake yawan ambaton Amurka da cicciɗa muradunta.