Abin da INEC ta ce kan rikicin cikin gida na jam'iyyun siyasar Najeriya

Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar zaben Najeriya, INEC ta yi tsokaci game da matakan shari'a da bangarorin cikin gida na jam'iyyun siyasar kasar ke dauka a tsakaninsu, da kuma rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyun.

Shugaban Hukumar zaben Professor Joash Amupitan wanda ya bayyana damuwar ya ce yanayin ba alheri ba ne ga jam'iyyun, kuma hakan na yin barazana ga saita tsarin dimokuradiyya a Najeriya.

Farfesa Amupitan ya koka da cewa, maimakon jam'iyyun su zama wani tsanin kawo sauyi a kasa, amma sun koma suna hamayyar shugabanci da ringingimu, al'amarin da ya koma kamar wani wasan kwaikwayo.

Hukumar Inec ta yi kira ga jam'iyyun su gaggauta daidaita rikicin cikin gida da ya dabaibaye su kafin babban zaɓe.

"Zabuka na jam'iyyu su ne ginshiƙin gudanar da babban zaɓe, don haka muke kira ga jam'iyyun su yi ƙoƙarin daidaita duk wata matsala ko rashin fahimta da ke tsakaninsu a jam'iyance kafin a kai ga zuwa kotu," kamar yadda Hajiya Zainab Aminu Abubakar, jami'a a sashen yada labarai da wayar da kan jama'a a hukumar Inec ta shaida wa BBC.

Ta ƙara da cewa kotu ce ya kamata a ce ya zama wuri na ƙarshe da za a je domin daidaita duk wata matsala tsakanin jam'iyyu.

Inec ta ce harakar kotu na jefa ta cikin wani ƙalubale musamman idan an samu saɓanin hukunci daga wata kotu zuwa wata.

"Wannan yana wahalar da hukumar zaɓe wajen gudanar da ayyukanta na tunkarar babban zaɓe," in ji Hajiya Zainab Aminu.

Fargabar Inec

Hukumar Inec ta nuna damuwa musamman yadda rikicin cikin gida na jam'iyyu zai iya tasiri ga ingancin zaɓen fitar da ƴantakara.

Hukumar zaɓe ta ce laifi daga ƙarshe yana dawo wa kanta ne sakamakon riginginmun jam'iyyu musamman idan har an jingine da kotu.

"Laifin da ba na hukumar zaɓe ba, sai ya dawo kanta a musamman lokacin da jam'iyyu suka gabatar da hukunce-hukunce na kotu mabambanta a ƙurarren lokaci."

"Ko kuma idan an yi hukuncin da bai yi wa wani ɓangare na jam'iyya daɗi ba, daga ƙarshe sai laifin ya daow kan hukumar zaɓe," in ji Zainab Aminu.

Hukumar Inec ta ce idan jam'iyyun za su yi ƙoƙarin sasanta rikicinsu na cikin gida a jam'iyyance zai taimaka mata wajen shirin gudanar da zaɓe.

Jam'iyyu da dama a Najeriya na fuskantar rikicin cikin gida inda wasu jam'iyyun ma sun rabe gida biyu

Yawan zuwa kotu kuma na ɗauke hankalin jam'iyyun musamman a daidai lokacin da ya kamata su a haɗu domin tallata jam'iyya.

A ranar 23 ga watan Afrilu zuwa 30 ga Mayun 2026 ne hukumar zaɓen Najeriya ta ba jam'iyyu domin fitar da ƴantakara.