Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran sun halasta?
- Marubuci, Luis Barrucho
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, WSL Global Journalism
- Lokacin karatu: Minti 7
Hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran, da kuma martanin da Iran ta mayar sum yi sanadin mutuwar fararen hula.
Majalisar Dinkin Duniya, ta bakin shugabanta António Guterres ta yi Allah-wadai da hare-haren, tare da kiran a tsagaita wuta da kuma mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.
Dukkanin ɓangarorin biyu na iƙirarin cewa a kan daidai suke, amma kuma ba za a iya tabbatar da hakan ba sai an bincika dokokin da kasashen duniya suka amince da su bayan yaƙin duniya na biyu.
Jin kaɗan bayan da Amurka da Isra'ila suka harba bama-bamai a Iran a ranar 28 ga watan Fabaraiu, shugaba Donald Trump ya zargi Tehran da yunkurin ƙera makaman nukiliya, wanda hakan barazana ce ga ƙawayenta.
Sai dai sakataren Amurka Marco Rubio ya ce ya zama wajibi Amurka ta ragargaji Iran saboda tana da masaniyar cewa Isra'ila za ta kai hari ƙasar.
Sai dai, shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya shaida wa BBC cewa yunƙurin Iran na mallakar makamin nukuliya ya isa ya sa su ƙaddamar mata da harin.
Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hari Isra'ila da wasu sansanonin sojin Amurka da ke ƙasashen gabas ta tsakiya a matsayin kare kai.
Sama da mutum 780, ciki har da yara mata 165 da ma'aikatan da Iran ta ce harin na Isra'ila a kan wata makaranta ya hallaka, kamar yadda ƙungiyar agaji ta Iran ta Red Crescent ta bayyana. Sama da mutum 50 ne aka kashe a wani harin da Isra'ila ta kai a Lebanon a ranar Litinin.
A gefe guda kuma, gomman mutane ne ciki har da sojojin Amurka shida suka mutu a Isra'ila da wasu ƙasashen Gulf.
Shin hare-haren na kan doka?
Masana shari'a da BBC ta tuntuɓa sun bayyana cewa, a dokance babu wasu dalilai da za a iya cewa sun cancanci Amurka da Isra'ila su ƙaddamar da hari kan Iran, duk da yake sun ce ita ma Iran ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa bayan martanin da ta mayar.
A ƙarkashin dokoki MDD, an haramta wa ƙasashe amfani da ƙarfin soji kan wata ƙasa sai dai bisa wasu sharuɗɗa kawai.
Dokokin guda biyu sun haɗa da:
- Sashe na 2(4): Haramcin yin barazana ko amfani da ƙarfin soji kan wata ƙasa.
- Sashe na 51: Ya ba da damar a yi amfani da ƙarfin soji idan harin na 'yan ta'adda ne.
Babbar tambayar ita ce ko matakin na Iran barazana ce.
Susan Breau, ƙwararriya a kan dokokin ƙasa da ƙasa a Cibiyar Nazarin Dokokin da ke Birtaniya, ta ce kafin ɗaukar matakin kare kai, akwai ɓukatar "gamsassun hujjojin kai hari", kuma ba ta gamsu da na Iran ba.
Gogaggen lauya mai kare haƙƙin ɗan'adam Sir Geoffrey Nice shi ya yarda da hakan. Daga shekarar 1998 zuwa 2006, ya jagoranci gurfanar da tsohon shugaban Yugoslav Slobodan Milošević, a kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa.
"Ba a gabatar da wata hujja ba," in ji shi. "Alamu sun gama bayyana cewa yaƙin ya saɓa da doka."
A Amurka kuwa, da dama daga cikin 'yan jam'iyar Democrats sun ce harin da aka kai Iran ya saɓa da doka, inda suka ce majalisar ƙasar ce kawai ke da hurumin ayyana yaƙi.
Duk da yake babban kwamadan tsaron ƙasar, wato shugaban ƙasa zai iya amfani da sojojin ba tare da ya sanar a hukumance ba.
Mece ce barazanar da ake fargaba?
Shugaba Trump ya ce Amurka ta yi yunƙurin tattaunawa da Iran bayan harin da ta kai wuraren haɗa makaman nukiliyarta guda uku a watan Yunin 2025, amma Tehran "ta ɓarar da damar ta na dakatar da shirin."
Ya bayyana cewa Iran na yunƙurin sake ci gaba da aikin samar da nukiliyar ta da kuma ƙera wasu makamai masu linzami da za su iya zama barazana ga ƙawayen Amurka.
"Mun samu rahotannin cewa...Iran na shirn kai hari da makamai masu linzami kafin Amurka da Isra'ila su yanke shawarar kai nasu harin," a cewar Ezra Cohen, ɗaya daga cikin tawagar tsaro da tattara bayanan sirri na gwamnatin Trump a wa'adin mulkinsa na farko a hirarsa da BBC.
Shi ma Rafael Grossi, daraktan Hukumar Sa Ido Kan Makamashin Nukiliya (IAEA), ya ce Iran ta daɗe tana burin mallakar makamin nukiliya amma babu wata hujja da ke nuna cewa suna kera makamin.
Wani rahoto da Hukumar Tattara Bayanan Sirri na Tsaro ta Amurka (DIA) ya ce tana da yaƙinin cewa Iran na da aiki ja a gabanta kafin ta iya ƙera makamai masu linzami masu cin dogon zango.
Masana sun bayyana cewa zargin da Trump ya yi a baya na cewa san lalata shirin Iran na nukiliya a yakin kwanaki 12 da aka gwabza tsakanin Iran da Isra'ila a shekarar da ta gabata bai yi wani tasirin kawar da barazanar ba.
Batun da ke da sarƙaƙiya a game da dokokin ƙasa da ƙasa shi ne matakin da za a iya cewa ya zama barazana.
A al'adance, barazana tana nufin "rasa dama ta karshe da mutum ke da ita ta dakatar da harin da zai iya faɗawa cikin ƙasa," in ji Marc Weller, wani malamin dokoki a jami'ar Cambridge.
An daɗe ana tafka muhawara kan wane lokaci ne wata ƙasa za ta iya amfani da ƙarfinta wajen kare kai, inda Breau ta ce: wasu na ganin cewa idan har akwai hujjojin da ke nuna an kai harin; wasu kuma na ganin za a iya ɗaukar matakin kare kai da zarar an samu sahihan bayanai cewa za a iya kai hari a kowane lokaci.
"Amma idan bai kai shekaru 10 ba," in ji ta.
Akwai kuma wasu sharuɗɗa biyu da suke sa a kare kai a dokance, inda Breau ta ce: idan hakan ya zama wajibi kuma babu wata mafita.
Weller da Breau suna ganin harin da Isra’ila ta kai kan Masar a shekarar 1967 a yaƙin kwanaki shida da suka fafata a matsayin wanda aka fi buga misali da shi game da yadda ƙasashe za su iya kare kansu a yanzu.
Breau ta ce, da dama sun yi amannar cewa dakarun Masar a lokacin da suke bakin iyaka sun kasance cikin shirin ko ta kwana domin daƙile hare-haren.
Sai da ta ce duk da haka ana ganin harin na Isra'ila na da sarƙaƙiya.
Shin martanin da Iran ta mayar yana kan doka?
Masu sharhi da dama sun yi amanna cewa martanin da Iran ta mayar ya saɓa da dokokin ƙasa da ƙasa.
Weller ya ce Iran ta karya dokokin ƙasa da ƙasa ta hanyar zafafa hare-harenta a kasashen yankin Gulf.
Sir Nice ya jaddada cewa duk da yake Iran na da damar kare kanta, bai kamata martanin ya wuce gona da iri ba.
"Yadda Iran ta yi amfani da makamai masu linzami da ba lallai su tsaya inda aka yi hari ba, wanda za a iya kallon hakan a matsayin abin da ya saɓa da doka.
Sai dai Breau ta gamsu cewa harin da Iran ta kai Otal din Fairmont da ke Dubai, yunƙuri ne na farmakar fararen hula ba wuraren sansanonin soji ba.
Mummunar hanya
Masana sun yi gargaɗin cewa rashin amfani da haramcin amfani da ƙarfi zai iya rage tasirin dokar nan da wasu lokuta.
Breau ta yi gargadin cewa wasu ƙasashen za su iya amfani da irin wannan damar su yi amfani da ƙarfi, irin su China.
"Abu ne mai matuƙar haɗari a dokokin ƙasa da ƙasa idan aka ci gaba da amfani da ƙarfi wajen kare kai ba kamar yadda aka tsara ba" in ji ta.
Idan ƙasashe masu ƙarfi suka ci gaba da take dokokin ƙasa da ƙasa ba tare da wani hukunci ba, mutane da dama na ganin hakan zai sa a samu koma baya a duk lokacin da yaƙi ya zo ƙarshe.