An naɗa ɗan ƙasar Rwanda Most Revd Laurent Mbanda, a matsayin sabon shugaban cocin Ingila na duniya a yayin taron mabiya ɗarikar Angalika na duniya wato Gafcon a birnin Abuja, Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan wani sashe na mabiya dariƙar Angalika da suka ce ba su amince da shugabancin Babbar Bishop ɗin cocin Ingila ba suka gudanar da nasu taron.
A yanzu za riƙa kiransa da Primus Inter Pares.
Kafin naɗin nasa a wannan muƙamin, Mbanda shi ne babban limamin cocin Angalika da ke Rwanda, kuma an yi zaɓen ne cikin sirri a daren ranar Laraba, inda aka sanar da naɗin nasa a Alhamis.
Cocin Angalika ya zama coci na uku mafi tarin mabiya addinin kirista a fadin duniya. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da bai wuce mako uku ba da rantsar da Dame Sarah Mullally a matsayin sabuwar Bishop ta cocin Canterbury.
Cocin Ingila bai ce komai ba game da sanarwar.
Wannan zaɓen na daga cikin manyan abubuwan da suka faru a taron Gafcon karo na 26 a Abuja babban birnin Najeriya, inda ɗaruruwan malaman addinin kirista ke halarta daga sassan duniya ciki har da nahiyar Arewacin Amurka, Australia da Afrika
Masu zaɓen sun bayyana cewa ba wai suna adawa da zaman mace a matsayin shugabar cocin Ingila ba ne, sai dai suna ganin shugabancin cocin na Ingila yana ƙoƙarin kawo wani sabon tsari da ya saɓa da koyarwar da aka bi a ɗarikar Angalika, kuma ba su cikin littafin Injila.
Sakataren yaɗa labaran taron na Gafcon karo na 26, Justin Murff, ya faɗa wa manema labarai a ranar Laraba cewa, Gafcon ba wai wani sashe ba ne da ya ɓalle daga haɗin kan mabiya Angalika, sai dai cocin Ingilan ne ya ɓalle daga tsarin ɗariƙar, inda ya ƙara da cewa ƙofar tuba a buɗe take idan sun shirya sake haɗewa da uwar ƙungiyar.