Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka ta bayyana sunayen sojojinta da suka mutu a yaƙin Iran
- Marubuci, Olivia Ireland
- Lokacin karatu: Minti 3
Rundunar sojin Amurka ta bayyana sunayen sojojinta na farko-farko da suka mutu sanadiyyar yaƙin da ake yi tsakanin Iran da Amurka da kuma Isra'ila.
Sojojin Amurka shida suka mutu a lokacin da "jirgi maras matuƙi" ya zulle wa garkuwar hari ta sama, ya faɗa kan sansanin sojin Amurkar na Port Shuaiba da ke Kuwait, a ranar Lahadi.
Da farko rundunar sojin ta ce mutum uku ne suka mutu sanadiyyar harin, amma a ranar Litinin hukumomi sun tabbatar cewa yawan wadanda suka mutu ya nunka bayan wani da ya samu rauni ya mutu, sannan kuma an gano gawar ƙarin mutum biyu a cikin ɓaraguzai.
Waɗannan sojojin shida, su ne kadai waɗanda Amurka ta tabbatar da mutuwarsu tun bayan yaƙin da Amurkar, tare da haɗin gwiwar Isra'ila suka kai wa Iran.
A ranar Talata ne rundunar sojin ta bayyana sunan huɗu daga cikin sojojin na Amurka, wato:
- Kyaftin Cody Khork mai shekara 35
- Saje Noah Tietjens, mai shekara 42
- Saje Nicole Amor, mai shekara 39
- Saje Declan Coady, mai shekara 20
Khork, mazaunin jihar Florida, a baya an taɓa tura shi aiki zuwa Saudiyya da sansannin Guantanamo Bay da kuma ƙasar Poland.
Ita kuwa Amor, ƴan jihar Minnesota ce, wadda a baya aka tura zuwa ƙasashen Kuwait da kuma Iraq.
Tietjens mazaunin jihar Nebraska, sau biyu ana tura shi ƙasar Kuwait.
Rundunar sojin Amurka ta ce an yi wa Coady ƙarin girma bayan mutuwar tasa. Cody wanda ya fito daga jihar Iowa, ya shiga aikin sojin Amurka ne shekaru uku da suka gabata.
A wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, sakataren harkokin tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce wani "ƙaƙƙarfan makami" ya faɗa kan "sansanin tsara ayyuka mai matuƙar tsaro".
Wasu jami'an tsaron Amurka uku, waɗanda ke da masaniya kan harin na Iran sun shaida wa kafar yaɗa labarai ta CBS cewa sojojin sun kasance suna aiki ne a wani tanti lokacin da aka kai harin.
Sun yi shakku ko tabbas an tsaurara tsaro a sansanin, inda suka ce ana amfani da tirela a matsayin wurin aiki, inda aka yi amfani da wani ƙarfe wajen samar wa tirelar kariya.
Amurka na da daɗaɗɗiyar alaƙar tsaro da Kuwait, kuma akwai sojojin Amurka sama da 13,000 da ke jibge a ƙasar.
Iran ta mayar da martani ga hare-haren da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar a kanta ta hanyar harba makamai masu linzami kan ƙasashen yankin Gulf masu alaƙa da Amurka.
Ƙasashen Bahrain da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Saudiyya da Oman da Qatar duk sun fuskanci hare-hare.
A Kuwait, Amurka ta tabbatar da kaɓo jiragenta uku, wani abu da aka bayyana a matsayin kuskure.
Wani bidiyo da aka yaɗa ya nuna yadda ɗaya daga cikin jirgin ke wulwulowa ƙasa. Dukkanin matuƙa jiragen sun tsira da rayukansu.
Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta yi ikirarin cewa Iran ce ta kaɓo jiragen, sai dai ba ta bayar da wata shaida ba.