Kakannin Vinicius Junior ƴan Kamaru ne - Bincike

Dan wasan Brazil da Real Madrid, Vinicius Junior ya yi suna wajen ƙoƙarin yaƙi da wariyar launin fata a harkar wasanni

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dan wasan Brazil da Real Madrid, Vinicius Junior ya yi suna wajen ƙoƙarin yaƙi da wariyar launin fata a harkar wasanni
Lokacin karatu: Minti 1

Wani bincike da aka yi na ƙwayoyin halitta, ya tabbatar cewar ɗan wasan Brazil, Vinicius Jr. tushensa daga Kamaru yake.

Hukumar ƙwallon kafar Brazil ce ta yi binciken tare da haɗin gwiwar masu gano ƴan asalin tsatson Afirka (African Ancestry) ranar Talata a Fonte Nova.

An bayyana sakamakon binciken ne gabanin wasan da aka buga na wasan neman shiga gasar cin kofin duniya, inda aka tashi 1-1 tsakanin Brazil da Uruguay.

Binciken ya gano cewar tsatson dan wasan na Real Madrid daga kabilar Tikar yake a Kamaru.

An bayar da takardar shaida ga Vinicius Jr. ta cewar daga Kamaru yake, tare da wani faifan bidiyo da ke nuna gadon kakanninsa na Tikar, wata fitacciyar kabila a Kamaru.

Wannan yunƙurin wani ɓangare ne na sanin haƙiƙanin tushe daga CBF, wanda ke girmama tarihi da na al'ummar baƙaƙen fata ƴan asalin Brazil, tare da mayar da hankali na musamman kan ƙwallon ƙafa.

Da yake magana game da tushensa, Vinicius ya ce, “Gano cewa tsatsonsa yana daga Kamaru lokaci ne na musamman a gare ni da iyalina.''

Dangane da binciken, mahaifin Vinícius ya nuna farin cikinsa, yana cewa, 'Yana da mahimmanci a gare mu mu san inda muka fito. Yawancin mutanen Brazil ba su da masaniya game da zuriyarsu ko gadonsu. Na yi farin ciki da cewa muna da tushe a Kamaru.'

Domin girmama kakanninsa, Vinicius Jr. ya sanya riga ta musamman mai ɗauke da tutocin Brazil da Kamaru a wasan da suka buga da Uruguay, inda aka tashi kunnen doki 1-1, inda dan wasan Real Madrid ya buga dukkan mintuna 90.