Kotu ta taka wa Trump birki kan lafta wa ƙasashe haraji

Wata kotun tarayya a Amurka, ta dakatar da matakin Shugaban kasar Donald Trump na jibga haraji ga kasashen duniya, a daya daga cikin wani babban kalubale na shari'a ga manufofin tattalin arzikin shugaban.
Kotun ta amince da bangaren lauyoyin da ke wakiltar masu kananan harkokin kasuwanci a Amurka, wadanda suka ce Mista Trump ya wuce gona da iri ta hanyar sanya haraji a kan kayan da ake shigarwa Amurka.
A lokacin da Shugaba Trump ke sanar da matakin jibga harajin a kan hajojin da ake shigar da su Amurkar, kusan daga dukkanin kasashen duniya a watan Afrilu- harajin da ya kai har kashi 50 cikin dari, Trump ya kira ranar – ranar 'yanci.
Kundin tsarin mulkin Amurka dai ya bayar da ikon sanya irin wannan haraji ne ga majalisar dokokin kasar, kawai.
To amma Mista Trump ya kafe cewa gibin da ake da shi a kasuwancin Amurka, ya kai ga abin da za a ayyana a matsayin matakin gaggawa na kasa – wanda hakan ya ba shi damar ci gaba da aiwatar da manufar tasa mai takaddama.
To yanzu dai bayan kusan wata biyu da ayyanawar kotun Amurka kan harkokin kasuwanci na kasa da kasa, ta taka wa gwamnatin Trump din birki kan aiwatar da wannan manufa ta harajin ramuwar- gayya, inda ta yanke hukuncin cewa MistaTrump ba shi da ikon sanya harajin.
Daman dai Shugaban ya dakatar da fara aiki da harajin har zuwa watan Yuli, domin bayar da dama a tattauna da kasashen da abin ya shafa.
Wannan hukunci dai a yanzu a iya cewa ya daburta shirin gwamnatin Trump din na wannan haraji, da a iya cewa ya raunana damarsa ta samun yadda yake so wajen cimma matsaya ko yarjejeniya da kasashen da ya jibga wa harajin.
Sai dai hukuncin bai shafi harajin kashi 10 cikin dari na shugaban ba.
Haka kuma nan take da ayyana hukuncin fadar gwamnatin Amurkar ta daukaka kara.
Wannan shari'a daya ce kawai daga cikin tarin shari'un da ke zaman jira a fadin kasar ta Amurka, dangane da manufofin Shugaba Trump din.











