Trump ya dakatar da bai wa ɗaliban ƙasashen ƙetare bizar shiga Amurka

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Gwamnatin shugaba Donald Trump ta ba wa ofisoshin jakadancinta da ke ƙasashen duniya umarnin dakatar da bai wa dalibai takardar neman izinin shiga ƙasar wato biza a yayin da take shirin faɗaɗa binciken kafafan sada zumuntar mutanen da take bai wa bizar.
Cikin wani saƙo da ya aikewa ofisoshin jakadancinta da ke ƙasashen duniya, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya ce za a ci gaba da ɗaukar wannan mataki har sai an fitar da wani sabon tsarin.
Matakin faɗaɗa binciken kafafan sada zumuntar dalibai da kuma mutanen da ke neman takardar izinin shiga Amurka zai yi matukar tasiri a harkokin ofisoshin jakadanci da diflomasiya.
Gwamnatin Trump ta ɗauki wannan mataki ne bayan zargin wasu manyan jami'o'in ƙasar da kasancewa masu tsattsauran ra'ayi.
Ya ce wasu daga cikin jami'o'i na bayar da ƙofa ga masu nuna ƙyama ga Yahudawa tare da nuna wariya a yayin bayar da gurbin karatu.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Tammy Bruce ta ce "a duk inda kake za mu rinka sanya maka idanu, idan kana son ka fara neman takardar izinin shiga Amurka to ka bi hanyoyin da suka dace".
Duk wasu dalibai daga wasu ƙasashen da ke neman gurbin karatu a Amurka su kan nemi biza ne a ofisoshin jakadancin Amurka da ke ƙasashensu kafin su shiga Amurkar don yin karatu.
Yawancin jam'o'in ƙasar sun dogara ne akan daliban da ke zuwa karatu daga wasu ƙasashe domin samun kuɗaɗen gudanar da makarantun saboda kuɗin makaranta mai tsokar da dalibai ke biya.
Gwamnatin Trump ta dakatar da bayar da kuɗaɗen tallafin da take bai wa jami'o'i, sannan ta mayar da dalibai da dama ƙasashensu musamman waɗanda aka soke bizarsu bayan gano wani kuskure a cikin bizar.
Amma kotu ta dakatar da mayar da wasu dalibai da dama bayan gudanar da bincike.
Fadar gwamnatin Amurka ta zargi wasu jami'o'in ƙasar da kyale masu goyon-bayan Falasdinawa da kasancewar dalibai a ƙasar.
Tuni jami'o'in suka soki gwamnatin Trump da take hakkin dalibai.











