Jami'o'in Amurka na fama da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa

Masu goyon bayan Falasdinawa a jamiar Columbia ta Amurka

Asalin hoton, Getty Images

An kama gomman masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a jami’o’in Amurka, yayin da tashin hankalin dalibai ke karuwa a jami’o’in.

Dauki-ba-dadi mafi muni da aka yi shi ne na Jami'ar Texas a Austin, inda ‘yansanda a kan dawaki suka hana masu zanga-zangar kafa sansani, sai kuma wadda aka yi a California.

Wasu na dora alhakin a kan masu tsattsauran ra’ayi daga wajen jami’o’in, wadanda suka yi nasarar kutsawa harabobin makarantun in ji masu korafin.

Wasu daga cikin jami’an gwamnati na kira da a dauki tsattsauran mataki a kan masu zanga-zangar, da cewa masu akidar kyamar Yahudawa ne.

‘Yansanda a kan dawaki cikin damara, sun yi taho-mu-gama da masu zanga-zangar a Jami’ar Texas inda suka kama gommansu.

Wasu daga cikin jami'an gwamnatin Amurka na danganata zanga-zangar da masu tsattsauran ra’ayi da suka ce sun yi kutse ne cikin jami’o’in kasar da ake ta samun wannan ra'ayi na goyon baya ga Falasdinawa dangane da yakin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Gwamnan jihar ta Texas Greg Abbott, wanda ya ce masu zanga-zangar sun fi dacewa da gidan yari, ya bayar da umarni ga rundunar tsaron kasar ta Natoinal Guard da ta kai dauki harabar jami’ar da ke Austin.

Gwamnan ya ce ya kamata a kori daliban da suka shiga zanga-zangar da ya ce ta nuna kyamar Yahudawa ce.

Can a Los Angeles, an yi dauki-ba-dadi da masu zanga-zangar da ‘yansanda, bayan da jami’an suka yi kokarin cire wasu tantuna da masu tayar da kayar bayan suka kafa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yayin ziyarar da ya kai Jamia’r Columbia a New York shugaban majalisar wakilan Amurka Mike Johnson ya ce dole ne a kawo karshen zanga-zangar.

Sai dai ya gamu da eho daga daliban yayin da yake korafi da cewa an bar masu tsattsauran ra’ayi da ‘yan ta-kife su muzguna wa dalibai Yahudawa a zanga-zngar:

Ya ce, '' a yau na zo nan domin na sheda wa dukkanin wadanda ke kumaji da neman shafe kasar Isra’ila daga taswira da kai hari kan dalibanmu Yahudawa da ba su ji ba ba su gani ba, cewa ba daya daga cikinsu, Isra’ila ko wadannan dalibai Yahudawa da ke wannan jami’a da za su kasance su kadai.''

Grace Dai, wadda daliba ce a Jami’ar ta nuna bacin ranta a kan ziyarar shugaban majalisar wakilna Amurkar.

Ta ce, ''ba ma tsammaninsa ko kadan. Ina ganin ya zo nan ne ya tayar da hankali. A gaskiya, ya haddasa bala’i a ko’ina. Ina ganin abin da ya sa muka yi masa eho kenan.

Zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa a jami’o’in Amurkar na ta karuwa tun bayan da aka kama sama da mutum dari daya da ke zanga-zangar a makon da ya gabata a Jami’ar Columbia.

A martani ga masu kira da Shugaba Joe Biden ya dauki tsattsauran mataki a kan masu zanga-zangar kakakin shugaban, ya ce, Mista Biden ya yarda da ‘yancin muhawara, amma dole ne masu zanga-zangar su kasance suna yinta cikin lumana kuma ba tare da nuna kyamar Yahudawa ba.