Mene ne asalin gaba tsakanin Iran da Isra'ila kuma ta yaya yaƙin Gaza ya tsananta ta?

Asalin hoton, Manu Brabo / Getty
- Marubuci, Guillermo D. Olmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Zaman fargaba na ci gaba da ƙaruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Iran ta kaddamar da harin jirage marasa matuka da kuma makamai masu linzami kan Isra'ila a daren Asabar, a cewar kafofin yaɗa labaran ƙasar.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kira taron majalisar yaƙin ƙasar kuma ya ce an tura na'urorin tsaron ƙasar domin su daƙile harin.
Iran ta yi alkawarin kai harin ramuwar gayya ne bayan kashe mata kwamandojin soji biyu a ranar 1 ga watan Afrilu a wani hari kan ofishin jakadancinta a birnin Damascus na Syria, wanda ta ɗora wa Isra'ila alhakin kaiwa.
Wannan dai shi ne sabon takun saƙa tsakanin ƙasashen, waɗanda suka ɗauki tsawon lokaci ba su jituwa.
Isra'ila da Iran sun shiga rikicin hamayya mai muni na tsawon shekaru. Hakan ya zamo ɗaya daga cikin abubuwa da ke janyo rashin zaman lafiya na siyasa a Gabas Ta Tsakiya.
Tehran tana ganin Isra'ila a matsayin karamar "shaiɗaniya" ƙawar Amurka a Gabas Ta Tsakiya, wadda ita kuma suke kira "babbar shaiɗaniya".
Isra'ila ta zargi Iran da tallafa wa ƙungiyoyin ƴan ta'adda da kuma kaddamar da hare-hare kan muradanta.
Gabar da ke tsakaninsu ta janyo mutuwar ɗimbin mutane, wanda yawanci abubuwan da gwamnatocin ke yi ne suka janyo su, sai dai sun sha musanta hakan.
Yaƙin da ake yi a Gaza ya ƙara janyo taɓarɓarewar al'amuran.

Asalin hoton, Getty Images
Ta yaya gaba tsakanin Isra'ila da Iran ta fara?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dangantaka tsakanin Isra'ila da Iran na cikin yanayi mai kyau har sai a shekarar 1979, lokacin da dakarun juyin-juya halin Musulunci suka kwace mulki a Tehran.
Duk da cewa ta nuna adawa da batun raba Falasɗinu, wanda ya janyo kirkiro da ƙasar Isra'ila a 1948, Iran ta kasance ƙasar Musulmi ta biyu da ta amince da su, bayan Masar.
A wancan lokaci, ƴan gidan sarautar Pahlavi ne ke mulkar Iran, waɗanda suka kasance ɗaya daga cikin ƙawayen Amurka a Gabas ta Tsakiya. A kan wannan dalili, wanda ya kirkiro da Isra'ila da kuma shugaban gwamnatinta na farko, David Ben-Gurion, suka ƙulla abota da Iran a matsayin wata hanya ta magance batun kin amincewa da sabuwar ƙasar Yahudawa daga makwabtanta Larabawa.
Sai dai a 1979, juyin-juya halin Ayatollah Khomeini ya janyo hamɓarar da mulkin Shah da kuma assasa Jamhuriyar Musulunci wadda ta gabatar da kanta a matsayin mai kare hakkin waɗanda aka tsangwama.
Ɗaya daga cikin abin da ake gane sabuwar gwamnatin shi ne kin amincewa da katsalandan ko tursasawar Amurka da ƙawarta Isra'ila.

Asalin hoton, Getty Images
Sabuwar gwamnatin ta Ayattolah ta katse dangantaka da Isra'ila, ta kuma daina amincewa da sahihancin fasfo ɗin ƴan ƙasarta da kuma kwace iko da ofishin jakadancin Isra'ila a Tehran da miƙa shi ga Falasɗinawa, wadda a lokacin ke jagorantar gwagwarmayar kafa ƙasar Falasɗinu da adawa da gwamnatin Isra'ila.
Alí Vaez, jagoran wani shiri a Iran na ƙungiyar ICG, wadda ƙungiya ce mai zaman kanta da ke neman warware rikici a duniya, ya shaida wa BBC cewa nuna kiyayya kan Isra'ila na ɗaya daga cikin abubuwan da gwamnatin Iran a wancan lokaci ta zo da shi, saboda yawancin jagororinta sun taya Falasɗinwa yaƙin sari-ka-noke a wurare kamar Lebanon, kuma suna jin tausayinsu.
Sai dai, Vaez ya yi imanin cewa, "sabuwar Iran na son gabatar da kanta a matsayin kasar Musulunci mai karfi wadda kuma ta bijiro da batun kafa ƙasar Falasɗinawa da ƙasashen Musulmi suka watsar.
Ta wannan hanyar, Khamenei ya fara nuna cewa batun kirkiro da ƙasar Falasɗinawa tasa ce kuma an koma mara wa masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Tehran baya.

Asalin hoton, Getty Images
Vaez ya bayyana cewa ba a fara nuna kiyayya kan Iran a Isra'ila ba, sai a shekarun 1990, saboda a baya ana ganin shugaban Iraƙi Saddam Husseini a matsayin babbar barazana a yankin.
Gwamnatin Isra'ila na ɗaya daga cikin masu shiga tsakani da suka taimaka wa wani shiri mai suna 'Iran-Contra', wadda ta dalilinsa ne Amurka ta karkatar da makamai zuwa Isra'ila domin ta yi amfani da su a yaƙin da ta yi da makwabciyarta Iraƙi tsakanin 1980 da 1988.
Sai dai a tsawon lokaci, Isra'ila ta fara ganin Iran a matsayin ɗaya daga cikin masu barazana ga kasancewarta, inda gabar da ke tsakaninsu ta tashi daga cacar-baki zuwa gwabzawa.
Yaƙin 'sunƙuru' tsakanin Isra'ila da Iran
Vaez ya bayyana cewa, bayan da Iran ta fara ganin an zamar da ita saniyar ware musamman a irin ƙasashe kamar Saudiyya, wadda ke da karfi a yankin Gabas Ta Tsakiya, daga nan ta fara bijiro da tsare-tsare da zimmar dakatar da makiyanta daga kai mata hare-hare.
Isra'ila ba ta zauna haka kawai ba, inda ita da Iran suka yi ta kai wa juna hare-hare.
An kwatanta faɗa tsakanin Iran da Isra'ila a matsayin yaƙin sunkuru saboda duka ƙasashen sun kai wa juna hare-hare, inda a yawan lokuta ba tare da gwamnati ta bayyana hannunta a hukumance ba.
A 1992, ƙungiyar Jihadi Islamic Jihad, kusa da Iran, ta far wa ofishin jakadancin Isra'ila a Buenos Aires, abin da ya janyo mutuwar mutum 29. Jim kaɗan kafin haka, aka yi wa shugaban Hezbollah Abbas al-Musawi kisan gilla.
Wani abu da ke damun Isra'ila, shi ne ganin hanyar da za ta bi wajen dakile shirin nukiliyar Iran da kuma hana ƙasar samun muggan makamai.

Asalin hoton, Getty Images
Tehran ta kuma ɗora laifin kai harin kan jami'an leƙen asirin Isra'ila.
Isra'ila tare da ƙawayenta na yamma, ta zargi Iran da kai mata hare-haren jirage marasa matuki da kuma na roka a baya, da kuma wasu hare-hare ta intanet.
Yaƙin basasar Siriya wadda ta faro a 2011, na ɗaya daga cikin abin ya janyo takun tsaka.
Majiyoyin leƙen asiri na ƙasashen yamma sun ce Iran ta tura makamai, kuɗi da kuma kwararru domin mara wa dakarun shugaba Bashar al Assad kan ƴan tawaye da ke ƙoƙarin hamɓarar da gwamnatinsa.
Hakan ya sanya hankula suka tashi a Isra'ila, wadda ta yi imanin cewa makwabtanta Siriya na cikin hanyoyin da Iran ke bi wajen aika makamai da kayan yaƙi ga Hezbollab a Lebanon.
Yaƙin 'sunkurun' ya kai bakin teku a 2021. A wancan shekarar, Isra'ila ta zargi Iran da kai wa jiragenta hare-hare a tekun Oman.
Iran, a nata ɓangaren, ta zargi Isra'ila da far wa jiragenta a tekun Bahar Mahaliya.

Asalin hoton, Hamed Malekpour / Getty
Harin Hamas kan Isra'ila
Bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da mayaka Falasɗinawa suka kai wa Isra'ila da kuma kaddamar da gagarumin farmakin soji da Isra'ila ta yi a Gaza a matsayin martani, masu sharhi da kuma gwamnatoci a faɗin duniya sun nuna damuwar cewa rikicin zai janyo gagarumar matsala a yankin Gabas Ta Tsakiya, da kuma arangamar yaƙi tsakanin Iran da kuma Isra'ila.
Faɗa tsakanin dakarun Isra'ila da kuma mayaƙa waɗanda ake zargi da alaƙa da Hezbollah a kan iyaka da Lebanon ya ƙaru a watannin baya-bayan nan, kamar yadda ake samun irin haka tsakanin sojojin da kuma Falasɗinawa masu zanga-zanga a Gaɓar Yamma da aka yi wa ƙawanya.
Har zuwa wannan Asabar, dukkan Iran da Isra'ila sun guji janyo yaɗuwar faɗa zuwa babbar yaƙi. Sai dai hakan ya sauya bayan da Tehran ta kaddamar da hare-hare da jirage marasa matuki da kuma makamai masu linzami.

Asalin hoton, Menahem Kahana / Getty
A cewar Vaez, “batun shi ne babu wanda yake son shiga cikin wani yaƙi yanzu. Isra'ila na cikin wata shida da fara yaƙi da Hamas a Gaza, wanda ya janyo mummunan tasiri kan martabarta a idon duniya da kuma saka ta zama saniyar ware wadda ba a taɓa ganin irinsa ba.
Masu sharhi sun yi gargaɗin cewa, ba kamar Hamas ba, Iran a matsayin ƙasa, na da karfin iko na gaske.

Asalin hoton, Ammar Ghali / Getty
Harin da Isra'ila ta kai kan karamin ofishin jakadancin Iran a Damascus, ya janyo mutuwar mutum 13, ciki har da manyan kwamandojin juyin-juya hali na Iran kamar Birgediya-Janar Mohammed Reza Zahedi, da mataimakinsa Birgediya-Janar Mohammed Hadi Haji-Rahimi, ya ƙona wa Tehran rai matuka.
Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta yi alkawarin hukunta waɗanda suka kai harin, kuma jakadanta a Siriya, Hossein Akbari, ya sanar da cewa martanin ba zai yi kyau ba.
Harin jirage marasa matuka da na makamai masu linzami na ranar Asabar, ba shi ne na karshe ba cikin wannan takun saƙa ta tsawon shekaru.











