Manyan jami’an Amurka na ƙoƙarin hana bazuwar rikici a Gabas ta Tsakiya

Asalin hoton, Reuter
Gwamnatin Amurka ta ƙara ƙaimi wajen inganta huɗɗar diflomasiyyar ta a Gabas ta Tsakiya.
Jami’an gwamnatin sun ce suna ƙaƙari ne don hana yaduwar yaƙin da Isra’ila ke yi da Hamas.
Yanzu haka tsohon shugaban hukumar tsaro ta CIA, kuma tsohon jakadan Amurka a Jordan yana wata ziyara a Isra’ila, inda zai tattauna da jami’an gwamnati.
An gayyato shi ne don faɗaɗa hanyar tattara bayanan sirri da kuma ƙoƙarin kaucewa kisar fararen hula a yaƙin.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, zai gana da hukumomi a Turkiyya, daga cikin ziyarar da yake a Gabas ta Tsakiya don cimma manufar Amurkar.
Sa’oi kaɗan kafin saukar Mr Blinken Turkiyya, an yi arangama tsakanin ƴan sanda da masu zanga-zanga a wani sansanin sojin Amurka da ke kudancin ƙasar.
Ƴan sanda sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye da ruwa wajen tarwatsa masu zanga-zanagr da suka nemi kutsawa cikin sansanin.
Mr Blinken ya kuma yi wata ziyarar ba-zata a Iraqi, duk dai a cikin yunƙurin Amurka na neman goyon bayan Gabas ta Tsakiya.
Da yake jawabi ga magoya baya, sakataren harkokin wajen Amurkan ya ce ya yi tattaunawa mai dadi da Firaiminita Mohammed Al Sudani, game da ƙoƙarin hana rikicin Gaza yaɗuwa zuwa sauran ƙasashen yankin.
Ya ce ‘‘Mun yi tattaunawa mai kyau. A taƙaice muna aiki tuƙuru ne don tabbatar da ganin yaƙin Gaza bai yaɗu zuwa sauran ƙasashe ba, ko dai a wannan yankin ko kuma a wasu sassan duniya. Wannan yana da muhimmanci, kuma aikin diflomasiyya ne da Amurka ta sa a gaba, kuma take yaɗawa a wannan ziyara.’’
Yakuma ce sun tattauna a kan ƙoƙarin hana hare-haren da ƙungiyar ƴan bindiga mai samun goyon bayan Iran, a kan dakarun Amurka da ke Iran da sauran wurare.
Kwana huɗu kenan da sakataren harkokin wajen Amurkar ke ziyara a ƙasashen Gabas ta Tsakiya da nufin shawo kan rikicin da ke barazanar karaɗe yankin.











