Adadin mutanen da suka rasu sakamakon fashewar tankar mai a Jigawa ya kai 181

Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnan jihar Jigawa a arewacin Najeriya ya bayyana cewa adadin mutanen da suka rasu sakamakon faɗuwar wata tanka ɗauke da man fetur ya kai mutum 181.

Umar Namadi ya bayyana haka ne lokacin da ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a ranar Talata, yana mai cewa mutum 80 ne ke asibiti zuwa yanzu.

"Dalilin da ya sa adadin ke sauyawa shi ne har yanzu akwai waɗanda suka ji raunin amma kuma suna gida ba su je asibiti ba," a cewarsa bayan ganawa da Tinubu.

Tun da farko, kakakin rundunar 'yansanda a Jigawa, DSP Lawal Shiisu Adam ya ce mutum 100 ne suka jikkata a ranar Laraba 16 ga watan Oktoba sakamakon gobara da ta tashi a daidai lokacin da mutanen yankin suka je kwasar fetur ɗin da ke zuba daga motar.

Gwamna Umar Namadi ya faɗa wa BBC cewa ana ba su kulawa ne a manyan asibitoci biyar da suka haɗa da asibitin Malam Aminu Kano, da na Jahun, da Nguru, da Haɗejia, da kuma na Gumel.

"Tankar man ta taso ne daga Kano za ta tafi Nguru a jihar Yobe lokacin da ta kwace wa direban," in ji Kakakin 'yansandan.

Babbar jami'ar hukumar kiyaye haɗurra a Jigawa, Aishatu Sa'adu, ta ce hatsarin ya faru ranar Talata da daddare a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura.

Ta shaida wa BBC cewa ibtila'in ya faru ne bayan da direban tankar ya kauce wa wata babbar mota ɗauke da tumatur.

Hakan ya sa direban tankar ya faɗa gefen titin har kan motar ya rabu da gangar jikinta, lamarin da ya sa fetur ɗin da yake dako ya malale titi da kwatoci a gefen hanyar.

Shi kuma kakakin rundunar 'yansanda a Jigawa, DSP Lawan Adam, ya ce bayan tankar ta faɗi sai mutane suka yi dafifi a wurin domin kwasar man da ya zuba a ƙasa bayan sun ci ƙarfin jami'an tsaron da ke korarsu a ƙokarin kauce wa tashin gobara.

Shaidu sun shaida wa BBC cewa tankar ta yi kusan awa biyu tana ci da wuta kafin jami'an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.

A yanzu haka jami'an tsaro sun tsare direban tankar kuma babu abin da ya same shi.

Hotunan da aka turo wa BBC sun nuna yadda aka lulluɓe gawarwakin mutanen da ganyayyaki, yayin da wasu hotunan suke ɗauke da gawarwakin da suka rasa wasu sassa na jikinsu.

Gwamnan jihar Umar Namadi da wakilai daga masarautar Dutse ne suka jagoranci jana'izar mutanen, tare da binne su a wani babban ƙabari ɗaya.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin taimakawa wadanda lamarin ya rutsa da su.

Ko a farkon watan Satumban bana, irin wannan ibtila'i ya halaka mutum 59 a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya bayan da wata tankar mai ta yi karo da wata babbar mota ɗauke da fasinjoji da kuma shanu.

Ana yawan samun faruwar hatsarin tankokin mai a Najeriya, musamman saboda rashin kyawun tituna da kuma tuƙin ganganci.