Birtaniya na jimamin mummunan harin da aka kai mata shekaru 20 da suka gabata

A treated image shows the aftermath of one of the 7/7 attacks on a bus, above a photo of two policemen.
Birtaniya na jimamin mummunan harin da aka kai mata shekaru 20 da suka gabata
    • Marubuci, Dominic Casciani
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Home and Legal Correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 9

Akwai bayyanannun hotuna masu sarƙaƙiya da sirri - da yanzu aka manta da su - waɗanda a karan kansu sun isa su gamsar da labaran da babu shaka ba a iya tantancewa ba, kuma babu mamaki za su iya daƙile mummunan harin kunar bakin-wake da ya auku shekaru 20 da suka gabata a Landan.

Hotunan mutumin da ya jagoranci hare-haren bama-bamai a ranar bakwai ga watan bakwai wanda a turance ake kira 7/7 - hotonsa na farko ya soma fita ne a sansanin horarwa da ake alakantawa da al-qaeda a wani yanki da ake kira Lake District a 2001 a Birtaniya.

Wasu ƙarin hotuna biyu da aka ɗauka a 2004 sun nuna shi - sunansa, amma babu wanda ya san manufarsa - ya hadu da wasu mahara biyu a wajen Landan, daga bisani tawagar M15 sun rinƙa bibiyar sa har ya koma Leeds.

Grainy black and white image showing Shehzad Tanweer and Mohammed Sidique Khan

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Hoton da ke nuna Mohammed Sidique Khan (hannun dama) wanda ya jagoranci harin 7/7

Babu wanda ya iya tunanin cewa wannan mutumin shi ne Mohammad Sidique Khan har sai bayan shi da mutanensa uku suka kashe mutane 52 ta hanyar amfani da bam da aka ƙera a gida.

Duk da cewa sun yi ta haduwa da ganawa da mutane, babu wanda ya taɓa tunanin akwai damuwa ko bukatar yin bincike.

A tsawon watanni ina ta tambayar manyan mutane - kama daga kan Firaiministoci da tsoffin masu ra'ayin riƙau - domin fahimtar abubuwan da suka koya ko darasin da suka ɗauka daga harin shekaru 20 da suka gabata a ranar 7/7. Sir Tony Blair ne Firaminista a wancan lokacin. Ya ce a yanzu an samu cigaba.

Na gano cewa gwamnatin Burtaniya, a yanzu babu shaka suna da karfin gano ire-iren waɗannan ayyuka na ta'addanci, idan aka yi kokarin kitsa su.

Amma kuma duk da hakan barazana da karfin ikon da ake amfani da su wajen daƙile ta'addanci a yau na sake buɗe kofa ga barazanar abin da aka gani a 2005. Don haka shekaru 20 bayan harin ranar 7 ga watan 7, mu na iya cewa mun tsira, ko da sauran aiki?

'Babu shaka an gaza'

Harin ranar 7 ga watan Juli, wato 7/7 ya matuƙar tayar da hankali da nausar da gwamnatin Burtaniya kan kafa hukumar yaƙi da hare-haren ta'addanci.

Al-Qaeda na shirya komansu kamar na soji - da umartar mambobinta, ciki har da maharan 7 ga watan 7. Amma akwai darussa da dama na ɗauka kan harin 7 ga watan 7.

M15 da ƴansanda sun fahimci akwai bukatar aiki tare domin magance barazanar tsaro domin daƙile Al-Qaeda.

M15 na da kwarewa matuƙa wajen tattara bayanan sirri. Suna iya gano barazanar tsaro cikin lokaci kalilan. Amma a lokacin harin 7 ga watan 7, sai aka samu akasi daga wajen hukumar.

Screen grab taken from video footage taken by emergency services of the scene at Russell Square Tube station in London, after a bomb blast onboard a train

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Hoton bidiyo da aka dauka lokacin aikin gaggawa bayan kai wani hari a hanyar jirgin kasa da ke tashar dandalin Russell a Landan.

Peter Clarke shi ne jami'in ƴansanda da ke jagorantar daƙile ayyukan ta'addanci a lokacin harin 7 ga watan 7.

"Ban yi magana da kowa ba wanda muke aiki tare wajen daƙile hare-haren ta'addanci ko bayannan sirri, wanda ba sa ganin hakan a matsayin gazawa, kamar yadda ya shaidamun."

Gazawar na tattare da sarkakkiya. Lord Jonathan Evans, tsohon shugaban M15 - a lokacin harin 7 ga watan 7, ya bada labarin matsin da suka shiga a wannan lokacin.

"Dole ka kasance mai matsaya a binciken ayyukan ta'addanci. Ba kuma za ka iya bincikar komai ba, abin tambayar shi ne shin ne kana bincike da nazartar barazanar nan kurkusa da daukan matakan da suka dace?"

Yadda M15 suka daƙile harin bam

Harin 2005 ya tilasta wa hukumar da 'yansanda nazari mai zurfi kan yadda za su iya ɗinke matsalolinsu da inda suke fuskantar gazawa wajen binciken mutane.

Wasu daga cikin matsalolin na kuɗi ne - kuma a tsawon shekaru an yi ta narka kuɗi domin toshe wannan giɓi.

Amma abu mafi a'ala ga M15, tare da haɗin-gwiwar 'yansanda, sun soma samun cigaba da bunƙasa wajen tattara bayanai da fahimtar barazanar a kan lokaci.

Wannan ya taimaka wa ƴansanda, wajen fahimtar barazana cikin gaggawa, abin da ya kai ga ana kama mutane a kai su gidan yari.

A London Underground train damaged by bombing rests on the tracks at the Aldgate tube station

Asalin hoton, Metropolitan Police via Getty Images

Bayanan hoto, Bayan harin 7/7 majalisa ta kirkiro sabuwar dokar yaƙi da ta'addanci
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shekara ɗaya bayan harin 7 ga watan 7 sun yi nasara wajen murkushe gagarumin harin ta'addanci. Maharan na ɗauke da wani kullin sinadarin bam da ke kama da lemun sha - kuma sun shirya tada shi a jirgin saman transatlantic.

M15 sun bada mamaki wajen kama mashirya harin. Sun gano mutanen a lokacin da suke kai komo ɗauke da wasu karafa da suka ce na aikin gida ne, ciki harɗa kwalaben lemu da kamarori.

Babu wanda ya iya tantace abin da suke shiryawa - har sai dai bayanan sirri da aka tattara suka bankaɗo mutane a lokacin da suke naɗar bidiyon shahada.

A 2006, majalisa ta zauna zaman nazarin bijiro da dokokin yaƙi da ta'addanci.

Wannan kokari ne na karawa 'yansanda karfi. Abinda suke bukata a yanzu shine nunawa kotu ko gamsar da alkali cewa mutumin da suka gurfanar da tattare da ra'ayin ta'addanci kuma yana kokarin aikata hakan, ta hanyar gabatar da abubuwan da bincikensu ya gano.

Max Hill KC ya jagoranci irin wannan shari'a - kuma hakan ya ba shi damar zama daraktar gabatar da kara tsakain 2008-2023. Yayi kokarin ganin anyi hukunci mai tsanani kan mutane da ake gurfanarwa saboda hakan ya zama darrasi ga masu irin wannan ra'ayi. Sai dai galibin lokota idan batun ya hada da hada bam ana shiga cikin yanayi na sarkakkiya tsakanin 'yansanda da M15.

Hare-haren ƙashin kai a sassan Turai

A 2014, dubban mata da maza masu tsattsauran ra'ayi sun shiga ƙungiyoyin jihadi da suka ƙware a Syria da Iraki, inda suke ganin wadannan ƙungiyoyi su za su samar da ƙasa ta dahir.

Gangamin ya shaida wa mabiyansa, da ba za su iya tafiya ba, su shirya nasu hare-haren a gidajensu ba tare da jiran umarni daga wajen kowanne kwamanda ba.

Wannan wani sabon abu ne da ya razanar sosai - abin da ya kai ga an samu hare-haren ƙashin kai a sassan Turai, ciki har da Burtaniya.

Gwamnati ta yi gaggawa wajen ɗaukan matakan tarwatsa wannan gangami a ciki da wajen ƙasar, ta hanyar soke fasfo dinsu ko ƙwace musu takardun 'yan ƙasa.

Hari na farko a jeren waɗannan hare-hare shi ne wanda ya faru a 2017, lokacin da wani matuƙi ya kutsa cikin mutanen da ke tafiyar kafa a gadar Westminister kafin daga bisani ya daɓa wa ɗansanda wuka a kofar shiga majalisa.

Two images showing ambulance scenes on Westminster Bridge in 2017, and another of flowers left outside the Houses of Parliament to pay tribute to the victims of Westminster terror attack

Asalin hoton, In Pictures via Getty Images and Anadolu Agency via Getty Images

Bayanan hoto, A 2017 wani mahari ya kutsa cikin mutane a gadar Westminister tare da daɓawa ɗansanda wuka a kofar shiga ginin majalisa

Karuwar ire-iren waɗannan hare-hare - sun kasance kalubale matuƙa. An yi kokarin ɗaukan matakai kada abin ya zarce tunani a koma ana kai harin ramuwa.

A 2015, wani matashi mai shekara 25 na ƙungiyar National Action, da a yanzu aka haramta, ya kai harin ƙiyayya kan wani mabiyan Sikh a wani kanti. Shi kaɗai ya kitsa harin. Kuma harin iri ɗaya ne da wanda aka kai wa ƴan majalisa Jo Cox shekara ɗaya kafin wannan lokaci, lokacin batun ficewar Burtaniya daga Turai.

Jo Cox ɗan majalisa ne a Jam'iyyar Labour MP da ke wakiltar Batley da Spen kuma an kashe shi ne bayan harbi da daba masa wuka a mazabarsa

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Jo Cox ƴar majalisa ne a Jam'iyyar Labour MP da ke wakiltar Batley da Spen kuma an kashe shi ne bayan harbi da daɓa masa wuka a mazabarsa

Wannan yanayi ya tilasta wa jami'an tsaro da abokan huldarsu, ciki har da FBI - kafa tawaga ta musamman da ke sanya ido kan rawar da shafukan sada zumunta ke takawa wajen hure kunnuwan matasa.

Suna zuwa a matsayin abokai da kirkirar shafukan da ke sauya wa matasa tunani da zuga matasa su kasance masu tsattsauran ra'ayi.

Tun daga wannan lokaci zuwa yanzu alkaluma sun nuna cewa a 2015, yara matasa 5,000 aka gano da ke cikin wannan barazana da kuma taimaka musu wajen dawowa hanya, ta hanyar jan hakalinsu sannu a hankali da ganar da su.

Abin da ya sa M15 ta gaza dakatar da harin bam din Manchester

Kazamin harin ta'addancin Manchester da aka kai 2017 - wanda mutane 22 suka mutu - ya gano cewa M15 ta gaza wajen fahimtar ana shirya wannan hari domin ta dakatar - kuma hakan ya nuna wasu abubuwan da suka gushe mata.

Ɗan Figen Murray, Martyn Hett na cikin mutane 22 da aka kashe.

Alhini da kaduwar da tayi sun sa ta kalubalanci jami'an tsaro a wani yanayi na shari'a da aka jima baa gani ba shekaru 20 da suka gabata.

Flowers and balloons are placed in central Manchester on May 22, 2018, the one year anniversary of the deadly attack at Manchester Arena

Asalin hoton, Oli Scarff/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, A 2017, mutane 22 suka kashe a harin ƙunar bakin-wake da aka kai Manchester

Tare da Nick Aldworth, tsohon babban jami'in 'yansanda, sun roƙi gwamnati domin kafa "dokar Martyn".

Dokar - da za ta soma aiki nan da shekara biyu - ta bukaci wuraren shirya taro su kasance suna da tsari na tsaro da zai taimaka wajen daƙile matsalar harin ta'addanci a wurarensu.

Sannan wuraren taron da ke saukan mutane sama da 800 na bukatar karin matakai kamar naurorin CCVT ko Jami'an tsaro, sannan duk wuraren da ke karɓan mutane sama da 200 dole su kasance suna da tsari na kare al'umma da tabbatar da cewa ma'aikatansu na da horo na musamman idan bukatar agajin gaggawa ta taso.

A wuraren kamar su O2 Arena a Landan, misali, ma'aikatan na tantance mahalarta taro tun daga saukarsu a filin jirgin sama. Sannan sun sanya injinan tantace da binciken ko mutum na dauke da makamai.

Rikici mara aƙida

Mataimakin kwamishinan Vicky Evans, wanda shi ne shugaban hukumar daƙile ta'addanci a yanzu, ya ce jami'ansu na ganin karuwar matasa da ke nuna tsatsauran ra'yi a shafukan sada zumunta.

A wasu lokutan jami'ai na kokarin tantace me ke faruwa kuma me ya kamata su yi wajen cirewa mutane irin wannan tunani.

Protesters throw flares in Liverpool during a demonstration held in reaction to the fatal stabbings in Southport on July 29

Asalin hoton, Peter Powell/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Bayan harin Southport, zanga-zanga ta ɓarke a sassan Ingila

Batun kisan Axel Rudakubana a Southport - wanda aka ta gargaɗi a kai - ya kasance abinda ake tafka muhawara a kai a shafukan internet.

Bincike na gaba zai so fayyace tarin tambayoyin da mutane ke da shi, kuma hakan na nuna dole a sake nazari kan batun amfani da kalmar "ta'addanci."

Matakin da sakataren harkokin cikin gida Yvette Cooper ya dauka na cire ƙungiyar Falasdinawa ta Palestine Action daga jeren ƙungiyoyin ta'addanci - duk da zargin aikata laifuka - ya sake ingiza muhawarar da ake tafkawa kan barazanar ire-ire waɗannan ƙungiyoyi da ayyukansu.

A 2017, 'yansanda sun ce an aikata laifukan ta'addanci cikin gida sau 15 kuma sun murkushe irin wannan yunkuri har sau 43.

A lokacin harin 2005, an zargi Sir Tony Blair da taka rawa wajen tsaikon murkushe wasu akidu.

Na tambayashi ko yanzu ya iya daidaita lamura - sai dai amsar da ya bayar za ta kasance zakaran gwajin dafi ga duk wanda ya gaje shi.