Ƴar Najeriyar da aka shigar Birtaniya ta ɓarauniyar hanya - wadda aka kasa gano iyayenta

- Marubuci, Sanchia Berg and Tara Mewawalla
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 6
Ɗabi'un da ba a saba gani ba da wasu ma'aurata suka riƙa nunawa kan ƙaramin yaron da suke ɗauke da shi lokacin da suka sauka a filin jirgin sama na Manchester da ke Birtaniya ne ya janyo hankalin jami'an tsaro.
Ɗaya daga cikin jami'an tsaron kan iyaka na Birtaniya ya shaida wa sauran cewa "akwai wani abu" game da waɗancan mutanen.
Daga nan sai jami'an tsaro suka keɓe su domin yi musu tambayoyi. Namijin mai suna Raphael Ossai ya yi iƙirarin cewa shi ne mahaifin ƙaramar yarinyar.
Ya miƙa wa jami'an tsaro wata takardar shaidar haihuwa, wadda ya ce ta yarinyar ce, takardar ta nuna cewa matar da suke tare da ita, Oluwakemi Olasanoye ita ce mahaifiyar yarinyar.
Amma sai jami'an tsaron suka gano wata takardar haihuwar ta daban a aljihun akwatin mutanen. A takardar akwai sunan wata matar daban - matar Raphael da ke zaune a Birtaniya - a matsayin mahaifiyar yarinyar.
Wannan ne mafarin yunƙurin bankaɗo wani sirri wanda har yanzu ba a kai ƙarshensa ba - har yanzu ba a tantance asalin mahaifan yarinyar ba.
Abin da aka gano shi ne yarinyar ba ta da alaƙa da dukkanin mutanen da aka gan ta tare da su. Yarinyar, wadda za mu kira ta da suna Lucy, alamu sun nuna cewa an haife ta ne a wani ƙauye da ke Najeriya a watan Satumban 2022.
Ma'auratan biyu da suka tafi da ita zuwa Birtaniya, wato Ossai da Olasanoye sun amsa laifin karya dokar shige da fice kuma tuni aka yanke musu hukuncin ɗauri na wata 18 sannan kuma za a mayar da su gida.
Yanzu haka Lucy ta kwashe kimanin shekara biyu a hannun hukumomi a birnin Manchester. Ofishin jakadancin Najeriya ya ƙi mayar da hankali kan lamarin duk da buƙatar hakan daga kotu.
A cikin wata tara da suka gabata, Babbar Kotun Manchester na ta ƙoƙarin gano asalin Lucy, yayin da kuma take ci gaba da tunanin mene ne zai kasance makomarta.
Ƙaramar yarinyar da ta ɓace
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An shaida wa kotu cewa mutane biyu, Ossai da Olasanoye sun shigar da Lucy Birtaniya - daga birnin Legas na Najeriya, inda suka bi ta Addis Ababa - ba bisa ƙa'ida ba.
Olasanya ya kasance yana da takardar izinin yin aiki a Birtaniya kuma ya amince zai shigar da Ossai da Lucy zuwa ƙasar.
Lokacin da kotu ta yanke wa ma'auratan hukunci, an ɗauka cewa Lucy ƴa ce ga Ossai, wadda ya haifa da matarsa haifaffiyar Najeriya, mazauniyar Birtaniya.
Ossai ya haɗu da matarsa ne a Kenya, sannan aka ɗaura musu aure da ita a Najeriya a shekarar 2017 - to amma bai taɓa zama a Birtaniya ba. Bai samu takardar izinin zuwa Birtaniya ba saboda gaza cika ƙa'idojin da suka jiɓanci kuɗi.
A lokacin yanke hukunci alƙalin ya ce "maƙasudin aikata wannan laifi" shi ne domin su kai yarinyar Birtaniya ta yadda shi da matarsa mai takardar zama a Birtaniya za su samu damar rayuwa tare a matsayin "iyali."
To sai dai a lokacin da kotun ke zama, wani gwajin halittar gado da aka yi ya nuna cewa Lucy ba ta da alaƙa da dukkanin mutanen biyu.
Takardun da aka gabatar wa kotu sun nuna cewa wata yarinya ɗaliba ce ta haife ta a wani ƙauye da ke Najeriya, wadda ba za ta iya ɗaukar nauyin kula da yarinyar ba kuma ba a san mahaifinta ba.
Takardun sun nuna cewa mahaifiyar ce ta miƙa yarinyar ga gidan marayu bisa raɗin kanta.
Ossai da matarsa mai takardar zama a Birtaniya sun kasance sun daɗe suna neman ƙaramar yarinya da za su riƙe a matsayin ƴa, wannan ya sanya suka karɓe ta tun tana ƙanƙanuwa.
Ma'auratan sun samu izinin riƙe yarinyar amma ba a matsayin ƴa ba kuma ba za su iya fitar da ita daga ƙasar ba.
Ossai, wanda mai shirya waƙoƙi ne, ya ajiye ƙaramar yarinyar a gidansa da ke Legas inda ya kula da ita na tsawon wata tara.
Ya shaida wa kotu cewa ya kula da yarinyar da kyau - ya samar mata da abinci mai kyau, yakan kunna mata waƙoƙi kuma ya kare ta daga duk wata cutarwa.
Sai dai wata jami'a a hukumar kula da yara da lamurran iyali (CAFCASS) a Birtaniya ta shaida wa kotu cewa tana da yaƙinin cewa Lucy ba ta samu kulawar da ta dace ba, ba a ciyar da ita yadda ya kamata ba kuma ba a ba ta kariyar da ta dace ba.
Ta fara haɗuwa da yarinyar ne lokacin da take da shekara ɗaya da ƴan watanni a watan Oktoban 2023.
Wata ma'aikaciyar kula da lamurran yara ta shaida wa kotu cewa "Yadda na gan ta da farko abin takaici ne."
Lokacin da take bayar da shaida, ta ce da alama "ba ta ma fahimci cewa ita ɗan'adam ba ce".
"Ba ta san halin da take ciki ba, ba ta cikin hayyacinta... tana jin kanta kamar ba ta tare da kowa amma zagaye da mutane," in ji jami'ar.
A wani lokaci da aka je duba ta, ma'aikaciyar ta bayyana cewa Lucy ta "firgita" lokacin da mai kula da ita ya tashi zai fita daga ɗakin.
Ta kuma riƙa yin "kuka mai tsanani" wanda ke "da wahalar rarrashi."
Lokacin da aka tambaye ta ko Lucy ta shiga wannan halin ne sanadiyyar tafiya a jirgin sama ko kuma saboda an miƙa ta gidan rainon yara, jami'ar gidan rainon ta ce zai yi wahala a ce wannan kawai ne zai jefa ta cikin hjalin.
Alƙali ya ce yarinyar ba ta nuna alamar wata shaƙuwa da mutanen ba.
'Muna kallon ta a matsayin ƴa'
Duk da cewa an yanke musu hukuncin ɗauri da kuma na fitar da su daga Birtaniya, Ossai da matarsa sun buƙaci kotu ta ba su damar kula da Lucy.
Ossai ya ce yana kallon Lucy tamkar ɗiyar cikinsa. Lauyoyinsa kuma sun ce tunda dai hukumomin Najeriya sun amince da shi a matsayin uban riƙo ga Lucy, kotun Birtaniya ba ta da ƴancin da za ta hana masa kula da ita.
Ossai ya ce Lucy ta kasance cikin farin ciki a tsawon lokacin da take tare da shi, kuma yana ganin cewa miƙa ta hannun fararen fata a gidan rainon yara shi ne ya tayar mata da hankali.
Haka nan lauyoyinta sun nuna damuwa kan cewa idan turawa fararen fata suka karɓe ta domin rainon ta a matsayin ƴa, za ta yi asarar al'adunta da asalinta.
Ossai da matarsa ƴar Birtaniya sun fashe da kuka a lokacin da suke magana kan ƙaunar da suke wa yarinyar.
Abin da ya fi dacewa ga Lucy
Alƙalin babban kotun da ke sauraron ƙarar, Sir Jonathan Cohen ya yi watsi da buƙatar Ossai da matarsa na cewa a duba yiwuwar mallaka musu yarinyar.
Ya ce ƙarairayin da suka yi da kuma yadda suka ɗauki yarinyar daga Najeriya zuwa Birtaniya ya "cutar da tunaninta."
Yanzu haka Lucy ta shiga hannun mutane da dama da ke kula da ita a gidajen rainon yara uku da aka kai ta tun bayan shigar da ita Birtaniya.
A watan Afrilu alƙalin ya buƙaci a nemi waɗanda za su iya karɓarta a matsayin ƴar riƙo a Birtaniya sannan kuma a sauya mata suna.
Ya ce Lucy "na buƙatar samun dama mafi dacewa a nan gaba", kuma hakan zai iya faruwa ne "kawai idan aka miƙa ta hannun wani iyalin na daban da zai kula da ita."
Alƙalin ya ce idan ta girma za a sanar da ita "asalinta" da kuma abin da ya faru da ita lokacin tana yarinya.
Ofishin jakadancin Najeriya bai mayar da martani kan ƙoƙarin da BBC ta yi na ji daga gare shi ba kan lamarin.










