Haaland ya ci Dortmund tsohuwar kungiyarsa a Etihad

Manchester City ta doke Borussia Dortmund da ci 2-1 a wasa na biyu a cikin rukuni a Champions League ranar Laraba a Etihad.

Dortmund ce ta fara cin kwallo ta hannun dan wasan tawagar Ingila, Jude Bellingham jin kadan da suka koma zagaye na biyu, bayan hutu ba ci.

Saura minti 10 su tashi daga wasan John Stone ya farke, wanda ya koma buga wa City tamaula a ranar bayan jinya da ya sha.

Minti hudu tsakani Erling Haaland ya kara na biyu da ya bai wa City damar hada maki ukun da take bukata ta kuma ci wasa biyu kenan a jere a bana.

Kenan Haaland ya zura kwallo na 26 a wasa 21 a Champions League da ya buga.

Mai shekara 22 da kwana 55 ya zama matashi a tarihin Gasar Zakarun Turai da ya ci tsohuwar kungiyarsa, bayan da ita ma can a baya ya ci mata kwallaye a gasar.

Mai wannan tarihin a baya shi ne Alvaro Morata da ya ci Real Madrid mai shekara 22 da kwana 194 a lokacin.

Wannan shi ne karo na biyar da suka kara a Champions League, inda kungiyar Ingila ta ci uku ta Jamus ta yi nasara a daya da canjaras daya.

A wasan farko a cikin rukuni a Champions League da suka buga a makon jiya Borussia Dortmund ta doke Copenhagen 3-0, ita kuwa City ta je Sifaniya ta casa Sevilla 4-0. .

Jerin wasannin da suka buga

2022/23

Champions League Laraba 14 ga watan Satumba 2022

  • Man City 2-1 B Dortmund

2020/2021

Champions League Laraba 14 ga watan Afirilun 2021

  • B Dortmund 1 - 2 Man City

Champions League Talata 6 ga watan Afirilun 2021

  • Man City 2 - 1 B Dortmund

2012/2013

Champions League Talata 4 ga watan Disambar 2012

  • B Dortmund 1 - 0 Man City

Champions League Laraba 3 ga watan Oktoban 2012

  • Man City 1 - 1 B Dortmund

Borussia Dortmund ta tabbatar da daukar Erling Haaland ranar 29 ga watan Disambar 2019.

Ta kuma dauki dan wasan kwana uku kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai a lokacin kan yarjejeniyar kaka hudu kan €20 million.

Haaland ya fara yi wa Dortmund tamaula a karawar da ta ziyarci FC Augsburg ranar 18 ga Janairun 2020, wanda ya shiga fafatawar daga baya, amma ya ci kwallo uku cikin minti 23 a wasan da Dortmund ta yi nasara da ci 5–3.

Sai dai ranar 10 ga watan Mayun 2022, Borussia Dortmund ta sanar cewar Haaland zai koma buga Premier League tare da Manchester City.

Kwana hudu tsakani dan kwallon ya yi ban kwana da magoya bayan kungiyar Jamus a Westfalenstadion daf da wasan karshe na Dortmund da Hertha BSC.

A wasan na karshe da Hertha, Dortmund ta yi nasara da ci 2-1, kuma Haaland ne ya fara cin kwallo a gumurzun.

Dan wasan mai shekara 21 ya zura kwallo 86 a raga a wasa 89 da ya buga wa Borussia Dortmund.

Manchester City ta kammala sayen Erling Haaland daga Borussia Dortmund kan £51.2m.

Dan wasan ya koma Manchester City a bana da taka leda, kan kwangilar shekara biyar da za ta kare a karshen kakar 2027.

A watan Mayu ne dan kasar ta Norway ya kulla yarjejeniya da City.

A baya dai kungiyoyin da ke buga gasar La Liga Real Madrid da Barcelona sun nemi daukar Haaland kafin ya yanke shawarar yin aiki da Guardiola.

Haaland ya zura kwallaye 92 a gasar lig a wasa 121 jimilla da ya buga wa Molde, Red Bull Salzburg da kuma Dortmund.

Nasarorin da ya samu:

Red Bull Salzburg

Austrian Bundesliga: 2018–19, 2019–20

Austrian Cup: 2018–19

Borussia Dortmund

DFB-Pokal: 2020–21

Norway U17

Syrenka Cup: 2016

Bayan Haaland da akwai wasu 'yan wasan Manchester da suka koma taka leda a Ethad da suka buga tamaula a Borusssia Dortmund.

'Yan wasan sun hada da Sergio Gomez da kuma Manuel Akanji.

Manchester City ta tabbatar da daukar dan wasan tawagar Sifaniya, Sergio Gomez daga Anderlecht a bana.

Mai shekara 21 ya koma Etihad da taka leda kan kwantiragin kaka hudu kan 13m euros (wato £11m) har da tsarabe-tsarabe.

Gomez ya fara daga makarabtar koyon tamaula ta Barcelona, kafin daga baya ya je Belgium kungiyar da tsohon kyaftin din City, Vincent Kompany ya horar wato Anderlecht.

Kungiyoyin da Gomez ya buga:

2017–2018 Barcelona B

2018–2019 Borussia Dortmund II

2018–2021 Borussia Dortmund

2019–2021 Huesca (wasannin aro)

2021–2022 Anderlecht

2022– Manchester City

Manchester City ta sanar da daukar dan kwallon tawagar Switzerland, mai tsaron baya, Manuel Akanji kan yarjejeniyar kaka biyar.

Mai shekara 27 ya koma Borussia Dortmund a Janairun 2018, wadda ya yi wa wasa 158.

Akanji ya yi wa Switzerland wasa 41 ya kuma taka rawar gani da tawagar ta samu gurbin shiga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.