Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Haaland ya ci wa Man City kwallo uku rigis a Premier
Manchester City ta doke Crystal Palace da ci 4-2 a wasan mako na hudu a gasar Premier League da suka fafata ranar Asabar a Etihad.
Palace ta fara cin kwallo bayan da John Stones ya fara cin gida, sai Joachim Andersen ya kara na biyu tun kan hutu.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Bernardo Silva ya zare daya, sai Erling Haaland ya farke na biyu.
Daga nan Haaland ya kara na uku da kuma na hudu a wasan - ya zama na farko da ya ci kwallo shida a wasa hudu a Premier, bayan bajintar Sergio Aguero..
Haka kum dan wasan ya zama na hudu da ya zura kwallo shida ko fiye da haka a wasa hudu da fara Premier League tun bayan Diego Costa mai bakwai a 2014.
Ranar 7 ga watan Agusta Haaland ya fara cin West Ham United kwallo biyu a wasan makon farko da City ta yi nasara a kan West Ham 2-0.
Haka kuma ranar 21 ga watan Agusta City ta tashi 3-3 da Newcastle, inda Haaland ya ci daya daga ciki.
City ta ci gaba da dora tarihin cin wasa 47 da canjars biyu a karawa 55 da ta yi ranar Asabar da karfe uku na yammaci da rashin nasara biyu kacal.
Wasa biyun da ta yi rashin nasara shi ne wanda Palace ta doke ta.
Ranar 31 ga watan Agusta City za ta karbi bakuncin Nottingham Forest a wasan mako na biyar a gasar Premier League.