Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pogba na fuskantar 'kwace da barazana' daga wata kungiyar masu laifi
Paul Pogba ya ce yana fuskantar kwace da barazana daga wata kungiyar masu aikata laifi.
Dan kwallon Juventus ya fitar da wannan sanarwar ta hannun lauyansa ranar Lahadi, ya kara da cewar ya kai rahoto ga jami'an tsaro.
Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ambaci wata kafa da ke cewar 'yan sandan Faransa sun fara bincike kan lamarin.
Tun a baya dan uwan Pogba, Mathias ya fitar da wani faifan bidiyo a kafar sada zumunta da yin alkawarin zai wallafa 'wasu bayanai masu girma kan tsohon dan kwallon Manchester United.
Mathias Pogba ya ce bayanan suna da girma, sai dai bai yi wani karin bayanai ba.
''Ana samun karin barazana da kokarin yi wa Pogba kwace daga wata kungiyar masu aikata laifi' kamar yadda ya sanar.
''An sanar da jami'an tsaro a Italiya da na Faransa tun a watan jiya, amma ba wani karin bayani kan lamarin, bayan da ake yin bincike.''
Pogba, wanda ya lashe kofin duniya da tawagar Faransa a 2018, ya koma Juventus a kakar nan, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Manchester United.
A faifan bidiyon, Mathias Pogab ya ce ''Ya kamata duniya da 'yan uwa da magoya baya da tawagar Faransa da kungiyar Juventus da kamfanonin da suke hulda da shi su san wasu batutuwan''.
Ya kara da cewar bayanan sun kuma shafi wakilin Pogba, Rafaela Pimenta.