'Muna fama da ƙarancin jami'an tsaro da kayan aiki a jihar Katsina'

Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin jihar Katsina a Najeriya, ta koka game da ire-iren kalubalen da ake fuskanta a fafutukar yaki da matsalar tsaro a wasu sassan jihar, kamar karancin jami'an tsaro da kayan aiki, ga kuma wahalar shiga, da rashin sakin jikin jama'a wajen samar da bayanan sirri.

Sai dai duk da haka gwamnatin jihar ta Katsina, ta ce tana bin dukkan matakan da suka kamata, domin shawo kan matsalar.

A yanzu gwamnatin ta kara yawan kananan hukumomin da ta dauki jami'an tsaro na sa-kai daga kananan hukumomi takwas zuwa goma sha takwas, domin su taimakawa jami'an tsaro a yakin da suke yi da barayin dajin da ke satar mutane domin neman kudin fansa.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Dakta Nasiru Mu'azu, ya shaida wa BBC cewa gwamnati na bakin kokari wajen ganin an samu zaman lafiya a jihar, sai dai ana fuskantar cikas ta fannoni da dama.

''Jami'an tsaro kama daga 'yansanda da sojoji da sauransu ba su wadata ba a jihar Katsina, kuma mai girma gwamna ya yi wannan bayani saboda akwai karamar hukumar da baki dayan jami'an tsaron da ake da su baki daya 32 ne, da bindigogi 5 kacal masu aiki. Kuma wannan karamar hukuma tana samun matsalar tsaro sosai, ka ga irin wadannan matsaloli na daga cikin abin da ke kara ta'azzara matsalar tsaron nan,'' in ji Dakta Mu'azu.

Ya kara da cewa wata matsalar da suke kara fuskanta ita ce wasu kauyukan ana shan wuya kafin a shiga, saboda suna nesa da gari akan dauki awa biyu zuwa uku kafin jami'an tsaron su isa wuraren.

Dakta Mu'azu ya ce wata karin matsalar ita ce rashin samun bayanan sirri da mutane ke bayarwa, saboda mutanen su yadda cewa an zo domin kare su wani batu ne da ke damun gwamnati.

Sai tsoron da suke ji na kai wa jami'an tsaro bayanan sirri kan 'yan bindigar saboda idan sun yi hakan jami'an tsaro sun kama barawon ba za a jima ba wani zai yi belin shi, to fa da zarar ya fito zai fara farautar wanda ya kai bayani a kan shi.

''Duk da wadannan matsalolin gwamnatin jihar Katsina ba zaune take ba, domin idan ba a manta ba ta dauki 'yan sa-kai a kananan hukumomi takwas, kuma an ba su horo da kayan aiki da alawus domin su taimaka wa jami'an tsaro, na 'yan sanda da Civil Defence da sojoji.

Kananan hukumomin sun hada da Jibiya da Batsari da Safana da Danmusa da Kankara da Dandume da Faskari da Sabuwa. A yanzu kuma mun fadada wannan aikin na 'yan sa-kai zuwa kananan hukumomi 18 na jiharmu, kuma tabbas kwalliya na biyan kudin sabulu.''

BBC ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yansandan Najeriya a jihar ta Katsina, game da batun karancin 'yansanda da kayan aiki a karamar hukuma da gwamnatin jihar ta bayyana, sai dai hakarmu ba ta cimma ruwa ba, saboda rashin amsa kiraye-kirayenmu na waya.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro ta 'yan fashin daji, da ke sace wa mutane dabbobi da lalata amfanin gona da sace mutane don neman kudin fansa, kuma a kodayaushe hukumomin tsaro a Najeriya na nanata kokarin da suke yi na magance matsalar.