Yarjejeniyar samar wa ƙasashen Turai makamashi mai rahusa daga Rasha ta zo ƙarshe

Pipeline

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Bututun da aka samar tun zaman Tarayyar Soviet ya bi ta cikin Ukraine ta wani yanki da dakarun Ukraine ke riƙe da ikon shi a yanzu a yankin Kursk
Lokacin karatu: Minti 5

An dakatar da shigar da gas daga Rasha zuwa ƙasashen Tarayyar Turai ta Ukraine bayan yarjejeniyar da aka yi ta shekara biyar ta ƙare, wanda ke nufin yarjejeniyar da ake amfani da ita tsawon gomman shekaru ta zo ƙarshe.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce ƙasarsa ba za ta bar Rasha ta cigaba da ''cin ribar biliyoyi da jininmu ba''. A gefe guda kuma gwamnatin Poland ta ce dakatar da yarjejeniyar wata nasara ce a kan Moscow.

Hukumar Turai ta ce Tarayyar Turai a shirye take kan wannan sauyi kuma akasarin ƙasashen za su iya ci gaba da harkokinsu a hakan. Ƙasar Moldova wadda ba ta cikin tarayyar Turan ta fara fuskantar matsalar ƙarancin makamashi.

Sai dai Rasha za ta iya ci gaba da aika gas zuwa Hungary da Turkiyya da kuma Serbia ta hanyar bututun TurkStream da ke tekun Black Sea.

Kamfanin Rasha mai suna Gazprom ya tabbatar da cewa shigar da gas zuwa Turai ta Ukraine ta tsaya ne da karfe 08:00 agogon Moscow (wato karfe 05:00 agogon GMT) a ranar Laraba.

Tun shekarar 1991 Rasha ke tura gas zuwa Turai ta cikin Ukraine.

Duk da dai tasirin katsewar a yanzu ba shi da yawa, tasirinsa nan gaba a Turai baki ɗayanta na da girma.

Rasha ta rasa wata babbar hanyar cinikayya, sai dai Shugabanta Vladimir Putin ya ce ƙasashen tarayyar Turai ne za su fi shan wahala.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun bayan mamayar da Rasha ta yi a Ukraine a shekarar 2022, Tarayyar Turai ta rage sayen iskar gas daga Rasha, sai dai har yanzu wasu ƙasashen yamma sun dogara kacokan kan samun gas daga Rasha, wanda hakan ke samar wa Rasha kimanin Euro biliyan biyar a duk shekara, kwatankwacin dala biliyan 5.2.

Adadin gas ɗin da aka shigar da shi Tarayyar Turai a shekarar 2023 ya yi ƙasa da kashi 10 bisa 100, a cewar ƙungiyar idan aka kwantanta da kashi 40 a shekarar 2021.

Sai dai ƙasashe da dama da ke cikin Tarayyar Turai, ciki har da Slovakia da Austria, sun cigaba da shigo da adadi mai yawa na gas daga Rasha.

Masu kula da samar da makamashi a Austria sun ce ba su yi hasashen samun wani tangarda ba saboda tuni su ka raba ƙafa wajen samun gas din kuma sun gina rumbunan ajiya.

Sai dai kuma ƙarshen yarjejeniyar ya kawo fargaba sosai a Slovakia wadda ita ce babbar hanyar shigar gas ɗin Rasha zuwa Tarayyar Turai kuma su na samun kuɗaɗen shiga ta hanyar shigar da gas din zuwa Austria da Hungary da kuma Italiya.

Slovakia ta ce za ta biya ƙarin ƙudade saboda samun wasu hanyoyin daban. Tun a farkon watan Disamba, hukumar samar da makamashinta ta sanar da cewa farashin gas din zai tashi a 2025 ga ƴan ƙasar masu siya.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Firaministan Slovakia, Robert Fico a ranar Laraba na cewa kawo ƙarshen yarjejeniyar zai samar da mummunar sakamako ga ƙasashen Tarayyar Turai, ba a kan Rasha ba.

A ranar Juma'a, Fico - wanda ya kai ziyarar bazata zuwa Moscow domin tattaunawa da Putin - ya yi barazanar daina samar da wutar lantarki ga Ukraine.

Hakan ya sanya Zelensky ya zargi Fico da taimaka wa Putin ''tallafa wa yaƙin da kuɗi da kuma raunana Ukraine.''

''Fico na ƙoƙarin sako Slovakia cikin yunƙurin da Rasha ke yi na ƙara jefa ƴan Ukraine cikin wahalahalu,'' a cewar shugaban Ukraine.

Poland ta yi tayin mara wa Kyiv baya idan har Slovakia ta katse samar mata da wutar lantarki, wani abu da ke da muhimmanci sosai ga Ukraine wadda cibiyoyinta da ke samar da wutar lantarki ke fama da hare-haren Rasha.

Firaiministan Poland, Radoslaw Sikorski ya shaida wa shirin Radio 4 na BBC cewa akwai wasu hanyoyin na daban na samun gas daga kasuwannin duniya, kamar daga Croatia da kuma Jamus da Poland.

''Akwai buƙatar a gwada yin amfani da waɗannan hanyoyi saboda kada Rasha ta samu kuɗi daga sayar da man fetur da gas zuwa ƙungiyar Tarayyar Turai,'' a cewar Sikorski.

Poland na shigo da gas daga Amurka da Qatar da kuma North Sea, in ji shi.

''Kamar dai yadda na fahimta, kowace ƙasa tana da hanyoyi na daban,'' in ji Sikorski.

Moldova na iya fuskantar matsaloli sosai bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar. Tana samun akasarin wutar lantarkinta daga wata tashar wutar lantarki da ke amfani da gas ɗin Rasha.

A ranar 28 ga watan Disamba, kamfanin samar da gas na Rasha mai suna Gazprom ya ce zai rage yawan gas ɗin da yake samar Moldova daga ranar 1 ga watan Janairu saboda bashin da ake bin ta.

Firaiministan Maldova, Dorin Recean ya musanta zargin gaza biyan bashin, sannan ya zargi Rasha da yin amfani da "makamashi a matsayin makamin siyasa", a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta.

Ya ce matakin zai bar Transnistra "babu wuta kuma babu hanyar jin ɗumi yayin da ake fama da ƙanƙararren sanyi".

An katse na'urar dumama wuri da ruwan zafi daga Transnistria '' saboda katsewar wucin gadi da aka yi na samar da gas'' da karfe 07:00 agogon gida (05:00 agogon GMT) a ranar Laraba, a cewar kamfanin samar da makamashi mai suna Tirasteploenergo a shafinsu na Telegram.

Sun buƙaci mazauna yankin su sanya kaya masu kauri, iyalai su tattaru a ɗaki guda, su kuma lulluɓa da bargo da kuma rufe tagogi da labule mai kauri, haka nan kuma su yi amfani da na'urar ɗumama wuri mai amfani da laturoni.

Ana ganin yayanin sanyi zai yi ƙasa da maki '0' a ma'aunin salshiyas a daren Laraba.

Amma ana cigaba da samar wa ma'aikatun lafiya da asibitoci wuta, in ji kamfanin.

Ministan kula da makamashi na Moldova, Constantin Borosan ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakan tabbatar da samar da wutar lantarki, amma ya yi kira ga ƴan ƙasar su daina ɓarnar makamashi.

Tun tsakiyar watan Disamba aka sanya dokar-ta-ɓaci a fannin samar da makamashi na kwana 60.

Shugaba Maia Sandu ta zargi gwamnatin Rasha da shafa musu baƙin fenti da nufin kawo hargitsi a ƙasarta kafin babban zaɓen 2025. Gwamnatin Moldova ta kuma ce ta aika da tallafi zuwa Transnistria.

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta gano wasu hanyoyi na daban na samun iskar gas daga Qatar da Amurka, da kuma gas daga Norway tun bayan mamayar Rasha a Ukraine.

A watan Disamba, hukumar Tarayyar Turai ta samar da wasu tsare-tsare domin sauya shigo da gas ta Ukraine baki ɗaya.