Yadda ƴan Rasha ke da fata mai kyau tare da yin ɗari-ɗari da Donald Trump

- Marubuci, Steve Rosenberg
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Russia editor, Moscow
- Lokacin karatu: Minti 5
Shawara gare ku - ka da ka sayi kwalaben giya 132 muddin ba ka da tabbacin za ka yi murna.
A watan Nuwamban 2016, wani ɗan siyasar ƙasar Rasha mai suna Vladimir Zhirinovsky na cike da murna kan nasarar Donald Trump a zaɓen shugaban ƙasa, saboda yana da tabbacin nasararsa za ta karfafa dangantaka tsakanin Amurka da Rasha.
Ya sayi kwalaben giya 132 domin yin murna a majalisar dokokin Rasha da kuma ofishin jam'iyyarsa a kuma gaban manema labarai.
Ba shi ne kaɗai ke murna ba.
Kwana ɗaya bayan nasarar Trump ta shiga fadar White House, wata shugabar gidan talabijin ɗin ƙasar Rasha, Margarita Simonyan, ta wallafa a shafinta na sada zumunta niyyar da take da ita ta fita tuki a faɗin Moscow riƙe da tutar Rasha cikin motarta.
Kuma ba zan taɓa manta lokacin da wani jami'in ƙasar Rasha ya faɗamin cewa ya sha taba da giya domin murnar lashe zaɓen Trump ba.
A Moscow, ana cikin zumuɗin cewa Trump zai soke takunkuman da aka kakaba wa Rasha, har ma da amincewa da yankin Crimea a matsayin wani ɓangare nata.
"Matsalar Trump ita ce bai taɓa yin magana kan batun ƴancin ɗan'adam ba a Rasha," in ji Konstantin Remchukov, mamallakin jaridar Nezavisimaya Gazeta.
Ba a ɗauki lokaci ba kafin abubuwa su taɓarɓare.
"Trump ya kakaba takunkumai masu tsauri kuma manya ga Rasha a lokacin," in ji Remchukov.
"A karshen mulkinsa, mutane da dama sun yi Alla-wadai da salon mulkinsa."
Abin da ya sa shekara takwas bayan nan - jami'an Rasha na taka tsan-tsan da takarar Trump a wannan lokaci.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaba Vladimir Putin ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga ƴar takarar jam'iyyar Democrat, duk da cewa wasu na kallon hakan kamar ba'a fadar Kremlin ke yi.
Putin ya yi iƙirarin cewa yana son salon "murmushin" Kamala Harris.
Amma ba sai ka zama cikkaken ɗan siyasa ba za ka gane abin da yake nufi, inda yake nufin son Trump ba wai Harris ba.
Alal misali, Trump ya soki irin taimakon soji da Amurka ke bai wa Ukraine, bai kuma ɗora laifi kan Putin ba a kan mamayar Ukraine, kuma lokacin muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa, bai ce yana son Ukraine ta samu nasara kan yaƙin ba.
A daya gefen, Harris ta ce Amurka na da zimmar taimakon Ukraine kuma ta kwatanta Putin a matsayin "mai kisa ɗan kama karya".
Makonni kalilan da suka wuce, wani mai karanta labarai a wani gidan talabijin a Rasha, ya soki kwarewar Kamala Harris a ɓangaren siyasa. Ya ce abin da ya fi mata shi ne ta riƙa gabatar da shirin girke-girke a gidan talabijin.
Akwai wani sakamako da zai yi daidai da ra'ayin Kremlin - fafatawa mai zafi a zaɓen da kuma sakamakon da take so. Sakamakon bayan zaɓe a Amurka zai janyo ruɗani da takun tsaka, zai kuma sanya ƙasar ba za ta mayar da hankali kan harkokin ƙasashen waje ba, ciki har da yaƙin Ukraine.
Dangantaka tsakanin Amurka da Rasha ta yi tsami lokacin mulkin Barack Obama, abin ya yi kamari karkashin mulkin Donald Trump, kuma kamar yadda jakadan Rasha a Washington Anatoly Antonov ya faɗa a baya-bayan nan, abubuwa naƙara rincaɓewa yanzu lokacin Joe Biden.
Washington ta ɗora laifin haka kan Moscow.
Kremlin ta kaddamar da mamaya kan Ukraine ne bayan halartar wani taro a Geneva inda Putin da Biden suka haɗu kimanin watanni takwas bayan nan.
Ba sanya takunkumi kan Rasha kaɗai Amurka ta yi ba, ta kuma taimaka ainun wajen bai wa Kyiv taimakon soji a yaƙin da aka kwashe sama da shekara biyu ana gwabzawa.
Cikin abubuwan da Amurka ta aika wa Ukraine har da tankokin yaƙi na Abrams da kuma rokokin HIMARS.
Da wuya a amince yanzu cewa akwai wani lokaci a baya-bayan nan, wanda Amurka da Rasha suka yi alkawarin aiki tare domin karfafa tsaro a duniya.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarun 1991 matan shugabannin ƙasashen Amurka da kuma Rasha wadda ke a matsayin Tarayyar Soviet a wancan lokaci, Raisa Gorbacheva and Barbara Bush, suka kaddamar da wani mutum-mutumi a Moscow - na wata agwagwa da ƴaƴanta takwas.
An gabatarwa da Moscow wannan ne a matsayin wata alama ta kulla abota tsakanin Tarayyar Soviet da kuma yaran Amurka.
Har zuwa yau ƴan Rasha na ci gaba da girma batun.
Ƴan ƙasar na tururuwar zuwa wajen shakatawa na Novodevichy domin ɗaukar hoto da tsuntsaye, duk da cewa masu ziyara kalilan ne suka san tarihin abin da ya sa aka kaddamar da abin don "karfafa hulɗar diflomasiyya".
Kamar dangantakar Rasha da Amurka, su ma agwagwin na da alaƙa da haka. Akwai wani lokaci da aka sace wasu daga ciki sai da aka sayi wasu domin maye gurbinsu.
Na yi tafiya don gano yaya ƴan Rasha ke kallon Amurka da kuma zaɓen ƙasar.
"Ina son Amurka ta ɓace," in ji wani mai suna angler Igor wanda ke kamun kifi a wani tafki da ke kusa. Amurka ta janyo yaƙe-yaƙe da dama a duniya. Ita abokiyar gabarmu ce lokacin Tarayyar Soviet kuma har yanzu muna gaba. Babu ruwanmu ko ma waye shugaban ƙasar."

Asalin hoton, Getty Images
Amurka abokiyar gabar Rasha ce har a bada - haka kafofin yaɗa labaran ƙasar ke nuna wa. Shin Igor yana fushi ne saboda yana samun labarai daga talabijin ɗin ƙasar Rasha? Ko kuma saboda bai kama kifaye da yawa bane.
Mutane da dama da na tattaunawa da su a nan, ba sa ganin Amurka a matsayin a matsayin abokiyar gaba.
"Ina son zaman lafiya da kuma abota," in ji Svetlana. "Sai dai abokina a Amurka yana fargabar kira na a waya yanzu. Watakila babu damar yin hakan a can. Ko kuma, matsalar a nan Rasha take. Ban sani ba."
"Ya kamata ƙasashenmu su zama ƙawaye," in ji Nikita, "Ba tare da yin yaƙi ba da kuma gogayya da juna wajen nuna wanda ya fi maƙamai masu linzami. Na fi son Trump. Lokacin da yake mulki babu yaƙe-yaƙe.
Duk da irin bambancin da ke tsakanin Rasha da Amurka, akwai wani abu ɗaya da suka yi kama da juna - maza ne ke mulkar ƙasashen a kowane lokaci.
Shin Rasha za ta iya ganin sauyawar haka?
"Ina ganin zai yi kyau idan mace ta zama shugaban ƙasa," in ji Marina.
"Zan yi farin ciki waje zaɓar mace shugaban ƙasa a nan Rasha. Ban ce hakan ne ya fi ko kuma bai dace ba. Sai dai zai zama da bambanci."











