Ronaldo zai yi takarar shugabancin hukumar ƙwallon ƙafa ta Brazil

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Sean Kearns
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
- Lokacin karatu: Minti 1
Tsohon tauraron ɗanwasan Brazil Ronaldo ya sanar cewa zai yi takarar zama shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar domin "dawo da martabar" tawagar ƙwallon ƙafarsu.
Tsohon ɗan ƙwallon mai shekara 48 ya buga wa Brazil wasa 98, kuma zai nemi maye gurbin Ednaldo Rodrigues ne a matsayin shugaban Confederation of Brazilian Football (CBF).
Brazil wadda ta ɗauki Kofin Duniya har sau biyar kuma mafi yawa a tarihi, ta ɗauki na ƙarshe ne a 2002 kuma ba ta sake wuce matakin kwata fayinal ba tun daga lokacin.
"Tsawon lokaci, fannin wasannin Brazil ne ke ɗauke wa 'yan ƙasar kewa daga matsalolin da suke fuskanta a kullum," kamar yadda Ronaldo ya faɗa wa Globo Esporte.
"Wannan ne abin da ke ƙarfafa musu gwiwa, amma yanzu muna ganin yadda mutane ke wofintar da tawagar ƙwallon ƙafar.
"Daga abubuwa da yawa da suka ba ni ƙwarin gwiwa wajen neman zama shugaban CBF har da son dawo da kima da martabar tawagar da take da shi tsawon shekaru."
Waa'din Rodrigues zai kai har ƙarshen 2026 amma wajibi ne a yi sabon zaɓe cikin wata 12 kafin lokacin.
Ronaldo wanda tsohon ɗanwasan Real Madrid ne, ya shafe shekara 17 yana buga wa ƙasarsa wasa, inda ya lashe Copa America da kuma tagulla a gasar Olympic.
Sai dai sau ɗaya kacal Brazil ta ci Copa America tun bayan ritayar Ronaldo a 2011.
A matsayin wani ɓangare na tsayawa takarar, Ronaldo ya ce zai sayar da hannun jarinsa a ƙungiyar Real Valladolid mai buga gasare La Liga ta Sifaniya.











